Cibiyar nazarin da bincike kan ƙasar noma ta jam'iar Bayero a jihar Kano dake Najeriya ce ta shirya taron da ya hada ƙasashe da masana da suka yi duba a kai. Taron karo na biyar ya baiwa masana damar nazari don lalubo hanyoyin magance matsaloli da suka hadabi wannan sashe da ya hada da noma da kiwo a Sahel da wasu ƙasashen.
May 24, 2025•20 min
A wannan makon, shirin zai yi duba ne kan halin da madatsun ruwa da ke jihohin Jigawa da Kano ke ciki, da irin amfanuwa ko akasi da masu cin moriyar su da suka haɗa da manoma da masunta da sauran al’ummmar yankunan ke yi da su.
May 18, 2025•20 min
Shirin namu na yau zai mayar da hankali ne akan yadda mahukunta a jihar Damagaram ko Zinder ta Jamhuriyar Nijar suka yi hobbasa wajen samar da yanayi mai ƙyau na noman shinkafa ga manoman da suka bada himma a bara, suka kuma ga amfaninta.
May 10, 2025•20 min
Shirin Muhalllinka Rayuwarka’ ya yada zango ne a jihar Maraɗi ta Jamhuriyar Nijar, inda ɗimbin manoman albasa suka shiga halin ‘ni ƴasu’ sakamakon yadda ƙaddara ta sa suka yi kiciɓis da mugun irin albasa, lamarin da ya sa suka tafka asara.
May 06, 2025•20 min
A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan hadin gwiwa da Gwamnatin jihar Jigawa ta yi da wani babban kamfanin samar da dabino na kasar Saudiyya da kuma wani kamfanin ƙwararru da bunkasa harkokin noma na Najeriya. Babbar manufar wannan haɗin gwiwar ita ce bunƙasa noman dabino a jihar, ta hanyar bullo da dabarun noma na zamani, da musayar fasahohi, da kuma samar da jarin noma.
Apr 26, 2025•20 min
A yau shirin zai yi nazari ne akan yadda karyewar farashin kayan abinci zai yi tasiri akan noman bana, sakamakon zargin da ake cewa gwamnatin ƙasar ta shigar da kayan abinci daga waje, wadanda ke gogayya da waɗanda manoman cikin gida suka noma. A shirin da ya gabata, mun kawo kukan da manoma ke yi akan wanna al’amari, inda suke cewa gwamnati ba ta yi wani abu a game da kayayyakin aikin gona da suke saya da tsada. A yau shirin zai duba irin tasirin da hakan zai yi da noman bana.
Mar 29, 2025•20 min
Manoma a Najeriya na cigaba da kokawa dangane da matakin da gwamnatin Najeriya ta ɗauka na karya farashin kayan gona a daidai lokacin da ƙasar ke ƙokarin samar da wadatar abinci.
Mar 26, 2025•20 min
Shirin ya yi duba kan yadda matsalar ta ƙaracin ruwa ke haifar da tasgaro a fannin noma don samar da wadatar abinci, inda mu ka ji daga manoma musamman na rani a Najeriya kan irin kalubale da su ke fuskanta na rashin samun wadataccen ruwa a gonakinsu, a daidai lokacin da ƙasar ta yi watsi da batun gyara galibin madatsun ruwa da ake da su ballantana ma a kai ga batun gina sabbi.
Mar 17, 2025•20 min
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wanan makon tareda Micheal Kuduson wanda kashi na uku ne ya dora akan kashi na biyu wanda ya gabata a makon jiya. Idan ba a manta ba, a makon da ya gabata shirin ya mayar da hankali ne kacokam akan yadda masu aiki a cikin teku ke rayuwa har ma da yadda za a yi amfani da teku, tafki, rafi ko kogi domin gudanar da harkokin noma da kuma kyautatawar muhalli.
Mar 09, 2025•20 min
Shirin, ‘Muhallinka Rayuwarka’ na wannan makon ci gaba ne daga shirin da kuka ji a makon jiya. Idan a wannan kashi na uku wanda shi ne na ƙarshe, ya mayar da hankali ne kan tasirin ruwan Tekuna da Tafkuna da kuma Koguna ga kyautatuwar muhalli ko gurbatarsa, da kuma hanyoyin magance ƙalubalen da muhalli ka iya fuskanta. Masana kimiyyar muhalli sun haƙiƙance cewa tabbas waɗannan nau'ika na ruwa guda uku suna da ɗumbin tasiri akan muhalli. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da ...
Mar 08, 2025•20 min
A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan bambancin da ke tsakanin teku da tafki da kuma kogi, tare kuma da yin duba game da irin gudunmowar da suke bayarwa ga muhall. Babu shakka masana kimiyyar halittu sun kasa ita wannan duniyar da muke ciki zuwa ɓangarori guda hudu: na farko, wanda ke dauke da duk ragowar ukun shi ne tsandauri, wanda ya hada da duwatsu da tudu da kwari da kasa da kwazazzabai, wadanda ake takawa ake tafiya a ciki da sauran abubuwa da ake yi yau da kullum.
Feb 22, 2025•20 min
A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan tasirin gurɓataccen sauti ga lafiyar halittu da muhalli wato Sound pollution a turance daga nan RFI.
Feb 08, 2025•19 min
Shirin ‘Muhalllinka Rayuwarka’ ya na dubi ne kan batutuwan da ke da nasaba da muhalli, sauyin yanayi, da kuma noma da kiwo, kuma duk mako ya ke zuwa muku a wannan tasha, kuma a daidai wannan lokaci, tare da abokinku, Michael Kuduson. A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne a kan noman kango ko kuma noman filin bayan gida wato Backyard Farming or Green House Farming a turance.
Feb 01, 2025•20 min
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wannan mako ya yi duba ne kan fitar da amfanin gona da aka noma a damunar bara da Kungiyar Gwamnonin Najeriya ta ce a ke yi sakamakon karyewar darajar kuɗin ƙasar, lamarin da su ka ce ya sanya su suma su ka tsunduma cikin masu ribibin sayen amfanin gonar, su na adanawa a rumbunansu domin maganin gobe. A farkon makon watan Janairun wannan shekarar, a yayin ziyarar gaisuwar sabuwar shekara da kungiyar gwamnonin Najeriya ta ka kai wa Shugaban ƙasar, Bola Ahmed Tinubu,...
Jan 25, 2025•20 min
Shirin Muhallinka Rayuwarka na wanan mako tareda Michael Kuduson ya mayar da hankali ne kan tasirin rashin tsara birane da gine-gine a kan muhalli, da kuma dangantaka tsakanin rashin tsara gari da gurbatar Muhalli.
Jan 18, 2025•20 min
Shirin 'Muhallinka Rayuwarka' na wannan makon tare da Michael Kuduson ya tattauna ne akan muhimmancin kula da ƙasar noma ta yadda za ta amfanar da al’umma ta fuskar bunƙasar ayyukan noma.
Dec 19, 2024•20 min
A cikin shirin wannan makon, zamu ji cewa a karon farko, gwamantin tarayya Najeriya ta kaddamar da shirin noman rani da na damina a jihar Cross River a ƙoƙarin da ta ke yi na haɓɓaka noma don samar da isasshen abinci, kuma ministan noma da samar da abinci Abubakar Kyari ne ya kaddamar da shirin noman rani na farko a madadin gwamnatin tarayya a wannan jiha da ke kudu maso kudancin ƙasar.
Dec 07, 2024•20 min
Najeriya na cikin kasashen da suka yi fice a noman rani dana damina, inda manoman ke noma shinkafa, tun bayan da tsohuwar gwamnatin ƙasar ta hana shigo da wasu nau’ikan kayan abinci, ciki har da shinkafa a wani ƙoƙari na bunƙasa noman shinkafar a cikin gida. Shirin ya yada zango ne a Nassarawa dake tarayyar Najeriya, jihar da ta bayyana shirin shiga harkar noman shinkafa ita da kanta, inda ta ware kadada sama da dubu 10 don noma shinkafar.
Nov 30, 2024•19 min
Shirin Muhallinka rayuwarka tare da Michael Kuduson kamar kowanne mako a wannan karon ya yi duba ne kan tsarin noma mai ɗorewa da ke nufin magance matsalar ƙarancin abinci da kuma yadda za a baiwa muhalli kariya.
Nov 23, 2024•20 min
Shirin ‘Muhallinka Rayuwarka’ na wannan makon ya yi tattaki zuwa Kano, inda hadin gwiwar Bankin Duniya da Gwamnatin jihar, ya jagoranci taron masu ruwa da tsaki kan kiwon dabbobi, domin inganta fannin ta kyautatawa ko zamanantar da tsarin kiwon dabbobin, samar da abincinsu, da kula da Lafiyarsu, gami da sarrafa madara da naman da suke samarwa.
Nov 16, 2024•20 min
A yau shirin zai leka Jamhuriyar Nijar don duba matsalar zaizayewar kasar noma da kiwo da ta jawo yaduwar sakaran gari ko tumbin jaki, wata kalar ciyawa dake mamaye filayen noma da kiwo, kuma dabbobi sam ba sa cin ta, haka ba ta da wani amfani da aka sani ga al’umma.
Nov 02, 2024•20 min
Shirin ‘Muhallinka Rayuwarka’ da ke nazari kan abin da ya shafi muhallli, canjin yanayi, noma da kiwo, ya yi tattaki zuwa Kamaru, inda ya duba shirin tallafa wa manoma wajen noman dawa mai jure fari da kasa mara kyau. Hukumar kula da samar da albarkatun gona a arewacin Kamaru IRAD ce ke jagorantar aiwatar da shirin na sake fasalin bunkasa noman dawa 'yar rani, wato moskowari.
Oct 26, 2024•20 min
Shirin ‘Muhallinka Rayuwarka’ na wannan makon zai mayar da hankali ne a kan matsalar karancin nama da aka shiga a sassa da dama na Najeriya, inda za mu je jihar Adamawa a arewa maso gabashin kasar don jin yadda ake ciki da kuma inda matsalar ta ke.
Oct 19, 2024•20 min
A yau Shirin zai mayar da hankali ne kan wani babban Taron karawa juna ilimi kan harkokin samar da abinci da bunkasa noma a Jihar Kano dake arewacin Najeriya Karkashin kulawar bankin Musulunci da Gidaunaiyar Bill and Melinda da Gidaunaiyar sarki Salman Wanda kungiyar harkokin noma ta SASAKAWA Africa ke jagoranta.
Oct 12, 2024•20 min