Bambamce-bambance tsakanin teku, kogi da tafki da gudummawar su ga muhalli
Feb 22, 2025•20 min
Episode description
A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan bambancin da ke tsakanin teku da tafki da kuma kogi, tare kuma da yin duba game da irin gudunmowar da suke bayarwa ga muhall.
Babu shakka masana kimiyyar halittu sun kasa ita wannan duniyar da muke ciki zuwa ɓangarori guda hudu: na farko, wanda ke dauke da duk ragowar ukun shi ne tsandauri, wanda ya hada da duwatsu da tudu da kwari da kasa da kwazazzabai, wadanda ake takawa ake tafiya a ciki da sauran abubuwa da ake yi yau da kullum.
For the best experience, listen in Metacast app for iOS or Android
Open in Metacast