Shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wanan makon tare da Nura Ado Suleimane, ya mayar da hankali kan wasu manyan labarai da suka fi ɗaukar hankali a makon da muka yi bankwana da shi ciki harda bukin cika shekaru 18 da gidan radiyon RFI ta yi.
May 24, 2025•20 min
Shirin Mu zagaya Duniya na wanan mako tare da Nura Ado Suleimane, ya maida hankali kan wasu munanan hare hare da kungiyoyi masu dauke da makamai su kai a Burkina Faso da wasu sassan Najeriya. Ku latsa alamar sauti domin jin cikakken bayani.....
May 17, 2025•20 min
Shirin Mu Zagaya Duniya na wanan makon tareda Nura Ado Suleimane, ya yi duba ne kan nasarar kashe ‘yan ta’adda fiye da dubu 13 da jami’an tsaron Najeriya suka yi. Shirin kuma ya sake waiwayar wani rahoton ƙwararru da ya ce dubun dubatar mutane ne ke rasa rayukansu a dalilin cutuka masu alaka da abincin da suke ci. Haka zalika ya taɓo batun yadda a Sudan ta Kudu kazamin rikicin da ke faruwa a yankunan da ke kusa da kogin Nilu, ya hana jami’an agaji tallafa wa yara ƙanana kimanin dubu 60 da ke fam...
May 10, 2025•20 min
Shirin Mu Zagaya Duniya na wanan makon tareda Nura Ado Suleimane, ya yi duba ne kan mai’aikata a sassan Duniya suka gudanar da bikin rana ta musamman da aka ware musu a daidai lokacin da wani adadi da dama daga cikinsu ke fuskantar ƙalubale iri-iri. Ku latsa alamar sauti domin jin cikakken shirin......
May 03, 2025•20 min
Shirin Mu Zagaya Duniya tare da Nura Ado Suleiman, kamar kowannen mako kan yi bitar muhimman labaran da suka faru cikin makon da muke ban kwana da shi, kuma kamar kodayaushe a wannan karon wasu daga cikin labaran da ke ƙunshe a shirin sun ƙunshi ziyarar da Ministan Harkokin Wajen Najeriya ya kai Jamhuriyar Nijar, wadda a karon farko kenan tun bayan kifar da gwamnatin shugaba Muhammad Bazoum da sojoji suka yi. A Najeriya shirin ya leƙa Filato aka samu hasarar ɗimbin rayuka, sakamakon hare-haren d...
Apr 19, 2025•19 min
Shirin Mu Zagaya Duniya na wanan makon tareda Nura Ado Suleimane ya duba yadda matakin shugaban Amurka Donald Trump na dakatar da harajin da ya shafe kayayyakin dukkanin kasashe ya farfado da tagomashin kasuwannin duniya, duk da cewar Gogan ya ce sassauncin na kwanaki 90 bai shafi ƙasar China ba. Ku latsa alamar sauti domin sauraron cikakken shirin.....
Apr 12, 2025•20 min
ƙasashe da dama ciki har da na Ƙungiyar EU, suka sha alwashin mayar da martanin ƙaƙaba wa kayayyakin Amurka haraji, kamar yadda shugaba Trump ya ƙaddamar da sabon tsarin karɓar harajin da ya ce ya shafi duniya baki ɗaya.
Apr 05, 2025•20 min
Sabuwar gwamnatin riƙon ƙwarya ta fara aiki a Jamhuriyar Nijar, bayan da aka kaddamar da fara aikin ƙudurorin da taron ƙasar na watan Fabarairu ya bayar da shawarar aiwatarwa. A Najeriya hukumar Kwastam ta janaye haraji a kan dukkanin kayayyakin asibiti da magungunan da ake shigar da su ƙasar daga ƙasashen ƙetare. Mummunar girgizar kasa ta rutsa da gwamman mutane a ƙasashen Myanmar da Thailand.
Mar 29, 2025•20 min
Masu sauraro Assalamu Alaikum, barkanmu da sake haɗuwa cikin shirin Mu Zagaya Duniya, wanda ke waiwayar wasu daga cikin muhimman lamurran da suka wakana a makon da muka yi wa bankwana da shi. A farkon makon da muka yi bankwana, Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya kafa dokar ta ɓaci a jihar Rivers, ya kuma dakatar da gwamna da mataimakiyarsa da kuma dukkan ‘yan majalisun dokokin jihar na tsawon watanni shida. Tinubu ya ce ya ɗauki matakin ne biyo bayan rikicin siyasar da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa...
Mar 22, 2025•20 min
Shirin Mu Zagaya Duniya’na wanan makon tareda Micheal Kuduson ya kuma duba batun watsi da wasu kungiyoyin farar hula a Jamhuriyar Nijar suka yi da rahoton taron ƙasa da ta shawarci shugaban mulkin sojin ƙasar ya ci gaba da zama kan karagar mulki har nan da shekaru biyar. Latsa alamar sauti domin jin cikakken shirin....
Mar 15, 2025•20 min
Mu Zagaya Duniya,bitar wasu daga cikin muhimman lamurran da suka wakana a makon da muka yi wa bankwana,cikin labarun da shirin ya waiwaya aƙwai tattaunawar da aka yi tsaƙanin manyan hafsoshin tsaron Najeriya da Nijar da Burkina Faso da kuma Mali,sai danbarwar da aka shafe makon da ya ƙare ana gani tsakanin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya da ɗaya daga cikin Sanatoci zauren majalisar Mata, bayan da ta zarge shi da ƙoƙarin cin zarafinta ta hanyar nemanta da lalata.
Mar 08, 2025•19 min
Daga cikin labarun da shirin Mu Zagaya Duniya na wannan makon ya ƙunsa akwai gargaɗin da Majalisar Ƙoli kan Shari’ar Musulunci ta Najeriya ta yi wa Malamai kan cewa su yi taka tsan-tsan yayin gabatar da wa’azi, musamman a cikin watan Azumin Ramadana mai alfarma. Sojojin Somaliya sun halaka mayaƙan Al Shebaab a ƙalla 70.Muna kuma ɗauke da bitar rahoton da ya gano yadda wata muguwar ƙwaya mai ta kashe dubban mutane (Tare da ci gaba da aika wasu dubban zuwa asibiti) a wasu ƙasashen yammacin Afirka....
Mar 01, 2025•20 min
Kamar yadda aka saba a kowane mako, a wannan karon ma shirin 'Mu Zagaya Duniya' ya waiwayi wasu daga cikin manyan labaru a kan lamurran da suka wakana a cikin satin da muka yi wa bankwana. Daga cikin labarun da shirin ya ƙunsa kuma akwai, afuwar 'yan Nijeriya da tsohon shugaban ƙasar Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya nema a kan soke zaɓen ranar 12 ga watan Yuni na shekarar 1993. Shirin ya kuma yi bitar labarin nasarar halaka mayaƙan Boko Haram kusan 300 da sojojin Chadi suka samu....
Feb 22, 2025•20 min
Daga cikin labarun da shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan makon ya yi bitarsu akwai matakin da kamfanonin sadarwa suka ɗauka a Nijeriya wajen ƙara farashin kuɗin kiran Waya da na Data, la'akari da yadda tsadar rayuwa ke shafar ayyukansu. Shirin ya kuma leƙa ƙasar Habasha inda gwamnatin ƙasar ke karɓar baƙuncin taron shugabannin ƙasashen nahiyar Afirka domin tattaunawa a kan muhimman batutuwa, ciki har da neman biyan diyya daga Turawan mulkin mallaka saboda bautar da miliyoyin 'yan Afirka da suka...
Feb 15, 2025•20 min
A cikin shirin 'Mu zagaya Duniya', wanda ya saba bitar wasu daga cikin muhimman lamurran da suka auku a makon da muka yi wa bankwana, za ku ji cewa: ‘Yan tawayen M23 tare da haɗin giwar mayaƙan AFC sun yi shelar kafa gwmnati a birnin Goma, ‘yan kwanaki bayan ƙwace shi da suka yi daga hannun sojojin Jamhuriyar Dimokarɗiyar Congo. A Jamhuriyar Nijar kuma, gwamnatin sojin ƙasar ce ta dakatar da baki ɗayan ayyukan hukumar bayar da agajin gaggawa ta 'Red Cross'.
Feb 08, 2025•20 min
Daga cikin labarun da shirin ya sake waiwaya a wannan makon, akwai cikar wa’adin ficewar kasshen Mali da Burkina Faso da kuma Nijar daga cikin ƙungiyar kasashen yammacin Afirka CCOWAS, da kuma abinda ya biyo baya.
Feb 01, 2025•20 min
Cikin makon da ya ƙare, Zaratan sojin Najeriya dake fatattakar ‘yan ta’adda a yankin arewa maso yammacin ƙasar, suka samu nasarar kashe kwamandojin riƙaƙken ɗan fashin dajin nan Bello Turji wanda ya zame wa jama’a Batoyi. Jami’in kula da watsa labaran rundunar ta ‘Operation Fansan Yamma’ Lafatanar Kanar Abubakar Abdullahi yayi mana ƙarin bayani kan nasarorin da suka samu.
Jan 25, 2025•20 min
Wasu daga cikin muhimman labaran da za ku ji a wannan shiri sun ƙunshi nasarar cimma yarjejeniya tsakanin Isra’ila da Hamas sai kuma wutar dajin Los Angeles wadda ta cinye faɗin yankin da ya zarta girman birnin Washington DC fadar gwamnatin Amurka akwai yadda
Jan 18, 2025•20 min
Daga cikin abubuwan da shirin Mu Zagaya Duniya na wanan makon ya yi waiwaye akai akwai yadda gobarar daji ce ke cigaba da tafka barna a birnin Los Angeles inda ta raba mutane kusan dubu 200 da muhalansu bayan kone fadin kasa da gine-gine masu yawan gaske.
Jan 11, 2025•19 min
Daga cikin labarun da shirin wannan makon ya waiwaya akwai yadda ɗaruruwan mutane mazauna ƙauyuka aƙalla 50 suka tsere daga muhallansu saboda barazanar da ƙasurgumin ɗan ta’adda Bello Turji yayi na kai musu farmaki, a ranar 1 ga watan Janairun da ya gabata. Sai kuma waiwayar rawar da tsohon shugaban Amurka marigayi Jimmiy Carter ya taka wajen samar da zaman lafiya a Yankin Gabas ta Tsakiya.
Jan 04, 2025•20 min
Shirin Mu Zagaya Duniya ta wannan makon tare da Nura Ado Sulaiman ya yi bitan wasu daga cikin labaran da suka fi daukar hankali a makon da muka yi bankwana da shi, masamman nanata zargin Najeriya da shugaban mulkin sojin Nijar ya yi na hada kai da wasu ƙasashen wajen yi musu zagon ƙasa ta fuskar tsaro sun haifar muhawara a tsakanin ‘yan ƙasashen, yayin da su kuma makuntan Najeriyar suka yi watsi da zarge-zargen da suka bayyana a matsayin marasa makama. A Mozambique kuwa fursunonin akalla dubu 60...
Dec 28, 2024•20 min
Shirin 'Mu Zagaya Duniya' na wannan makon tare da Nura Ado Suleimaza ya mayar da hankali ne kan mayan labarai da suka fi ɗaukar hanhali a makon da muka yi bankwana da shi, masamman halin da ake ciki a Najeriya bayan da shugaban ƙasar ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2025.
Dec 21, 2024•20 min
Shirin Mu Zagaya Duniya na wannan mako tare da Nura Ado Sulaiman kamar ko yaushe ya yi duba kan muhimman labaran da suka faru a makon da ya gabata, ciki kuwa har da batun yaddama’aikatar tsaron Najeriya ta bakin hafsan hafsoshin sojin ƙasar Janar Christopher Musa ta sanar da cewa cikin watanni 6 na ƙarshen wannan shekara adadin ƴan ta’adda dubu 129 da 417 tare da iyalansu ne suka ajje makamai bayan miƙa wuya ga mahukuntan ƙasar, lamarin da ke matsayin gagarumar nasara a ƙoƙarin da Najeriya ke yi...
Dec 14, 2024•20 min