Tasirin ziyarar ministan wajen Najeriya a Nijar ga rikicin ƙasashen biyu - podcast episode cover

Tasirin ziyarar ministan wajen Najeriya a Nijar ga rikicin ƙasashen biyu

Apr 19, 202519 min
--:--
--:--
Listen in podcast apps:
Metacast
Spotify
Youtube
RSS

Episode description

Shirin Mu Zagaya Duniya tare da Nura Ado Suleiman, kamar kowannen mako kan yi bitar muhimman labaran da suka faru cikin makon da muke ban kwana da shi, kuma kamar kodayaushe a wannan karon wasu daga cikin labaran da ke ƙunshe a shirin sun ƙunshi ziyarar da Ministan Harkokin Wajen Najeriya ya kai Jamhuriyar Nijar, wadda a karon farko kenan tun bayan kifar da gwamnatin shugaba Muhammad Bazoum da sojoji suka yi.

A Najeriya shirin ya leƙa Filato aka samu hasarar ɗimbin rayuka, sakamakon hare-haren da aka kai a wasu yankunan jihar, a Najeriyar za a ji yadda wata shu’umar cuta ta janyowa manoman Tumatir hasarar ɗimbin amfanin gonar, sai kuma yadda ‘yan damfara suka yi awon gaba da sama da naira tiriliyan 1 a Najeriyar.

A Sudan kuwa ƙungiyar bayar da  agaji ta Redcross ce ta aƙalla mutane dubu 8000 suka bace a yakin kasar.

Sai kuma Kenya inda aka cafke wasu mutane da ke shirin fasa kaurin dubban tururuwa zuwa ƙasashen ƙetare.

Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

For the best experience, listen in Metacast app for iOS or Android
Open in Metacast
Tasirin ziyarar ministan wajen Najeriya a Nijar ga rikicin ƙasashen biyu | Mu Zagaya Duniya podcast - Listen or read transcript on Metacast