Rasha ta karɓi baƙuncin taron bikin cika shekaru 80 da kawo ƙarshen yaƙin duniya na biyu
May 10, 2025•20 min
Episode description
Shirin Mu Zagaya Duniya na wanan makon tareda Nura Ado Suleimane, ya yi duba ne kan nasarar kashe ‘yan ta’adda fiye da dubu 13 da jami’an tsaron Najeriya suka yi.
Shirin kuma ya sake waiwayar wani rahoton ƙwararru da ya ce dubun dubatar mutane ne ke rasa rayukansu a dalilin cutuka masu alaka da abincin da suke ci.
Haka zalika ya taɓo batun yadda a Sudan ta Kudu kazamin rikicin da ke faruwa a yankunan da ke kusa da kogin Nilu, ya hana jami’an agaji tallafa wa yara ƙanana kimanin dubu 60 da ke fama da cutar yunwa.
Akwai kuma labarin yadda Rasha ta karbi bakuncin taron ƙasashe a bikin cika shekaru 80 da samun nasarar murƙushe sojojin Nazi na Jamus abin da ya kawo ƙarshen yaƙin duniya na biyu.
Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.
For the best experience, listen in Metacast app for iOS or Android
Open in Metacast