Wasu daga cikin labarun mako a cikin shirin Mu Zagaya Duniya
Jan 25, 2025•20 min
Episode description
Cikin makon da ya ƙare, Zaratan sojin Najeriya dake fatattakar ‘yan ta’adda a yankin arewa maso yammacin ƙasar, suka samu nasarar kashe kwamandojin riƙaƙken ɗan fashin dajin nan Bello Turji wanda ya zame wa jama’a Batoyi. Jami’in kula da watsa labaran rundunar ta ‘Operation Fansan Yamma’ Lafatanar Kanar Abubakar Abdullahi yayi mana ƙarin bayani kan nasarorin da suka samu.
For the best experience, listen in Metacast app for iOS or Android
Open in Metacast