A wannan talata, al’ummar Kamaru na bikin cika shekaru 53 da haɗewar yankunan da ke amfani da Faransanci da masu amfani da harshen Ingilishi, waɗanda kafin nan suna zaune da juna ne a ƙarƙashin tsarin tarayya. To sai dai a daidai yayin da ake wannan biki, yanzu haka akwai masu gwagwarmaya da makamai don samar wa yankunan da ke turancin Ingilishi ƴanci. Shin ko me za ku ce a game da wannan haɗewa? Ko waɗanne matakai ku ke ganin cewa sun dace a ɗauka domin dawo da yarda a tsakanin bangarorin biyu?...
May 20, 2025•11 min
Matsalar barace-barace a kan titunan manyan birane a Yammavin Afirka sai daɗa yin ƙamari take, to sai dai bisa ga dukan alamu mahukunta a ƙasar Ghana sun ƙuduri aniyar kawo ƙarshen wannan ɗabi’a. Domin a cikin makon jiya, jami’an tsaro sun cafke mabarata sama da dubu biyu a birnin Accra kawai, kuma yawancinsu ƴan asalin ƙasashen Najeriya, Nijar, Burkina Faso da Mali ne. Shin ko akwai dalilan da za su sa jama’a su mayar da bara a matsayin sana’a? Ko waɗanne matakai ya kamata a ɗauka domin kawo ƙa...
May 19, 2025•10 min
A duk ranar Juma'a, RFI Hausa na bai wa jama'a damar tofa albarkacin bakinsu kan abubuwan da ke ci musu tuwo a kwarya kama daga siyasa, tattalin arziki, zamantakewa, harkokin yau da kullum da dai saurarensu. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin tare da Shamsiyya Haruna...
May 16, 2025•10 min
Makonni kaɗan gabanin bukukuwan Sallar Layyah, mahukuntan jamhuriyar Nijar sun bayar da umurnin hana fitar da dabbobi zuwa ƙetare. Ga alama dai an ɗauki matakin ne don hana tashin farashin dabbobi a wannan lokaci, yayin da wasu ke cewa matakin zai iya cutar da tattalin arzikin ƙasar. Abin tambayar shine, menene amfani ko kuma illar wannan mataki ga ƙasar? Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.
May 15, 2025•10 min
Hare-haren ƴanbindiga na ci gaba da ɗaukar sabon salo a Najeriya, inda a baya-bayan nan suka tsananta kai farmaki hatta akan sansanonin soji, kusan a iya cewa haka take a sauran yankin sahel musamman Burkina Faso, lamarin da kanyi sanadin mutuwar jami’an tsaro masu tarin yawa. Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a kan wannan maudu'in.......
May 14, 2025•10 min
Shin ko kun san muhimmancin kula da lafiyar ƙwaƙwalwa kuwa? Wannan tambaya ce mai matuƙar muhimmanci, lura da cewa yanzu haka akwai ɗimɓin mutane da ke fama da wannan matsala a sassan duniya. Yayin da wasu ke kira wannan lalura a matsayin hauka, masana kuwa na cewa hatta shiga yanayi na damuwa ko da ƙuncin rayuwa na iya haddasa wannan matsalar. Shin ko wace irin kulawa ku ke bai wa lafiyar ƙwaƙwalwa? Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a....
May 13, 2025•10 min
A duk ranar Juma'a, RFI Hausa na bai wa jama'a damar tofa albarkacin bakinsu kan abubuwan da ke ci musu tuwo a kwarya kama daga siyasa, tattalin arziki, zamantakewa, harkokin yau da kullum da dai saurarensu. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin tare da Shamsiyya Haruna...
May 09, 2025•10 min
Kamfanin Meta da ya mallaki Facebook, Instagram da Whatsapp ya yi barazanar ficewa daga Najeriya bayan da aka lafta masa biyan tarar dala miliyan 290 saboda karya ƙa’ida. To sai dai gwamnatin Najeriya ta ce ko da kamfanin ya janeye daga ƙasar, to dole ne sai ya biya wannan tarar. Za mu so jin ra’ayoyinku a game da wannan takun-saka tsakanin Najeriya da kuma wannan shahrarran kamfani na sadarwa. Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a....
May 05, 2025•10 min
Shirin ra'ayoyin masu saurare na wannan rana ta Juma'a bisa al'ada ya kan baiwa masu saurare damar fadin albarkacin bakinsu kan batutuwan da ke ci musu tuwo a kwarya. Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Shamsiyya Haruna
May 02, 2025•10 min
Kamar dai kowace shekara, yau 1 ga watan Mayu, ita ce Ranar Ma’aikata ta Duniya, bikin da a bana ana iya cewa ana gudanar da shi ne a cikin wani yanayi na tsadar rayuwa a mafi yawan ƙasashen duniya. Abin tambayar shine, shin ko a cikin wanne yanayi ake gudanar da bukukuwan na bana, musamman a kasashen Afirka? Waɗanne irin manyan buƙatu ma'akata suke son cimma wa? Shiga alamar sauti, diomin sauraron ciakken shirin.
May 01, 2025•9 min
Bisa ga dukan alamu Maroko na ƙara samun kusanci da ƙasashen Burkina Faso, Mali da kuma Jamhuriyar Nijar a daidai lokacin da alaƙa ke ƙara yin tsami tsakanin waɗannan kaasashen da Aljeriya. Ministocin Harkokin Wajen ƙasashen uku sun ziyarci Maroko tare da ƙulla yarjejeniyar da ke ba su damar yin amfani da tashoshin ruwa ƙasar, alhali ba ɗaya daga cikinsu da ke da iyaka da Marokon. Ko yaya ku ke kallon wannan alaƙa tsakanin Maroko da AES, yayin da suka juya wa makociyarsu Aljeriya baya? Ku latsa ...
Apr 30, 2025•10 min
Shirin ra'ayoyin ku masu saurare na wannan rana ya mayar da hankali ne kan yadda wasu fitattun mutane mambobin kungiyar farar hula a Najeriya suka nuna takaicinsu kan yadda gwamnatin mai ci ke neman mayar da kasar tsarin jam'iyya daya. Ku danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Oumarou Sani
Apr 29, 2025•10 min
A duk ranar Juma'a, RFI Hausa na bai wa jama'a damar tofa albarkacin bakinsu kan abubuwan da ke ci musu tuwo a kwarya kama daga siyasa, tattalin arziki, zamantakewa, harkokin yau da kullum da dai saurarensu. Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a.
Apr 25, 2025•10 min
Yayin da a yau aka ƙaddamar da makon rigakafi a duniya, Hukumomi a Najeriya da kuma Unicef, sun yi gargaɗin cewa yanzu haka nau’ukan cutar shan’inna har guda 17 da suka yaɗu a cikin jihohi 8 na ƙasar. Wannan dai babban ƙalubale ne ga sha’anin kiwon lafiya, bayan da aka shelanta kawo ƙarshen cutar tun 2020. Shin ko meye dalilan sake ɓullar wannan cuta a Najeriya? Waɗanne matakai ya kamata a ɗauka domin shawo kanta? Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin masu saurare....
Apr 24, 2025•10 min
Shirin ra'ayoyin masu saurare na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda wani kamfanin hada-hadar kudi ta Internet a Najeriya mai suna CBEX ya tsere da kudaden jama'a. Danna alamar sauarre domin jin cikakken shirin tare da Nasiru Sani
Apr 17, 2025•9 min
Shirin ra'ayoyin masu saurare na wannan mako ya mayar da hankali ne kan gargaɗin gwamnatin Najeriya na yiwuwar samun ambaliyar ruwa a jihohi 30 a daminar bana. Danna alamar saurare domin jin cikakken shirin tare da Abida Shu'aibu.
Apr 16, 2025•10 min
Shirin ra'ayoyin masu saurare na wannan rana ya mayar da hankali ne kan yadda kungiyoyin ta'addanci ke kawowa ilimin yara mata tsaiko a Najeriya. Danna alamar sauarre don jin cikakken shirin tare da Nasiru Sani.
Apr 15, 2025•11 min
Yau ta ke ranar jin ra'ayoyin ku masu saurare kan batutuwan da ke ci muku tuwo a ƙwarya, kama daga fannin siyasa, ilimi, lafiya, tattalin arziƙi da dai sauransu. Latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyi...
Mar 14, 2025•10 min
Hukumar Yaƙi da Rashawa a Najeriya EFCC, ta ce a cikin shekarar ta 2024 da ta gabata, ta yi nasarar ƙwato kusan Naira tiriliyan ɗaya daga hannun barayi da masu handame dukiyar al’umma. EFCC ta ce ko a gaban kotu ma, ta samu nasarori sama da sau dubu huɗu akan masu cin rashawa da kuma ƴan damfara cikin shekarar da ta gabata. Abin tambayar shine, ko aikin hukumar na gamsar da 'yan Najeriya? Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakakken shirin.
Mar 11, 2025•10 min
Ƙungiyar direbobin motoci a Najeriya, ta buƙaci mahukunta su ɗauki matakan kawo ƙarshen kisan da ƴan awaren Biafra ke yi wa direbobin manyan motoci a duk lokacin da suke ratsa yankin kudu maso gabashin ƙasar. Ƙungiyar ta ce an kashe mambobinta sama da 50, kuma 20 daga cikinsu an kashe su ne a shekarar 2024, sannan aka kwashe kayayyaki da kuma ƙona motocinsu. Shiga alamar sauti, domin sauraron cikakken shirin.
Mar 04, 2025•10 min
A yau Juma'a kamar yadda aka saba, masu sauraro ko kuma bibiyarmu a shafukan sada zumunta, kan aiko da saƙonnin ra'ayoyi kan batutuwa da dama, kama daga wanda ke ci musu tuwo a ƙwarya a fannoni daban-daban na rayuwa, da kuma fannin tattalin arziki, da tsaro, da lafiya, da siyasa da sauransu.
Feb 28, 2025•10 min
Aƙalla 40% na mazauna yankin arewa maso yammacin Najeriya ne ka tu’ammuli da miyagun ƙwayoyi, kuma kusan 28 cikin ɗari suna zaune ne a jihar Kaduna kamar dai yadda rahoton hukumomin da yaƙi da wannan matsala ya nuna. Hakazalika, mutum 1 cikin 7 a yankin arewa maso yammacin ƙasar suna tu’ammali da miyagun ƙwayoyin a cewar rahoton. Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin...
Feb 27, 2025•10 min
A yau Juma'a kamar yadda aka saba, masu sauraro ko kuma bibiyarmu a shafukan sada zumunta, kan aiko da saƙonnin ra'ayoyi kan batutuwa da dama, kama daga wanda ke ci musu tuwo a ƙwarya a fannoni daban-daban na rayuwa, da kuma fannin tattalin arziki, da tsaro, da lafiya, da siyasa da sauransu. Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin...
Feb 21, 2025•10 min
Hukumar Ƙayyade Farashin Wutatar Lantarki a Najeriya, sanar da sabon tsarin biyan tara a kan waɗanda ke satar makamashin lantarki a ƙasar. Tarar ta kama daga Naira dubu 100 zuwa dubu 300 daidai da irin salon da mutum ya yi wajen sada gidansa da wannan makamashi.
Feb 20, 2025•10 min