Ra'ayoyi masu saurare kan alakar Morocco da ƙasashen AES
Apr 30, 2025•10 min
Episode description
Bisa ga dukan alamu Maroko na ƙara samun kusanci da ƙasashen Burkina Faso, Mali da kuma Jamhuriyar Nijar a daidai lokacin da alaƙa ke ƙara yin tsami tsakanin waɗannan kaasashen da Aljeriya.
Ministocin Harkokin Wajen ƙasashen uku sun ziyarci Maroko tare da ƙulla yarjejeniyar da ke ba su damar yin amfani da tashoshin ruwa ƙasar, alhali ba ɗaya daga cikinsu da ke da iyaka da Marokon.
Ko yaya ku ke kallon wannan alaƙa tsakanin Maroko da AES, yayin da suka juya wa makociyarsu Aljeriya baya?
Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a.
For the best experience, listen in Metacast app for iOS or Android
Open in Metacast