Ra'ayoyin Masu Saurare kan ficewar Meta daga Najeriya
May 05, 2025•10 min
Episode description
Kamfanin Meta da ya mallaki Facebook, Instagram da Whatsapp ya yi barazanar ficewa daga Najeriya bayan da aka lafta masa biyan tarar dala miliyan 290 saboda karya ƙa’ida. To sai dai gwamnatin Najeriya ta ce ko da kamfanin ya janeye daga ƙasar, to dole ne sai ya biya wannan tarar. Za mu so jin ra’ayoyinku a game da wannan takun-saka tsakanin Najeriya da kuma wannan shahrarran kamfani na sadarwa.
Ku latsa alamar sauti domin sauraren mabanbantan ra'ayoyin jama'a.
For the best experience, listen in Metacast app for iOS or Android
Open in Metacast