Kasuwanci - podcast cover

Kasuwanci

RFI Hausawww.rfi.fr

Shirin yakan duba yadda kasuwanci da tattalin arizikin kasashen duniya ke ciki. Kana yakan ji sabbin dubaru da hanyoyin ci gaban tattalin arzikin na kasashen duniya. Tare da jin ta bakin 'Yan kasuwa da Masana’antu dangane da halin da suke ciki.

Episodes

Yadda matan Arewacin Najeriya ke ƙara yin tasiri a kasuwancin jihar Lagos

Shirin 'Kasuwa Akai Miki Dole' na wannan makon tare da Ahmad Abba ya mayar da hankali ne kan babban taron da ƙungiyar Matan Arewa ƴan kasuwa mazauna Lagos da ke kudancin Najeriya su ka yi a birnin Lagos, wanda ya mayar da hankali kan karfafawa mata gwiwa kan harkokin kasuwanci da bunkasa tattalin arzikinsu.

May 28, 202514 min

Yadda gobara ta haddasa mumuna asara ga 'ƴan kasuwar Taminus ta Jihar Filato

Shirin Kasuwa akai Miki Dole na wanan makon tareda Ahmed Abba , ya mayar da hankali kan asarar sama da Naira biliyan ɗaya da ƴan kasuwar Taminus na birnin Jos suka tafka sakamakon konewar wani bangare na babbar kasuwar ta jihar Filato dake Najeriya. Ku latsa alamar sauti domin sauraron karin bayani.......

May 07, 202510 min

Yadda manoman zoɓo a Najeriya suka  fuskanci kalubale a harkar

Shirin kasuwa akai miki dole na wannan makon ya mayar da hankali ne kan halin da ake ciki game da noman zoɓo a jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya, da kuma yadda ake fita da shi zuwa ƙasashen ƙetare. Duk da cewa ana noman zoɓo a Jihohi irin su Zamfara da Katsina da Kano da Kebbi da Borno da Yobe, bayanai na cewa kusan kaso 70 cikin 100 na zobon da ake fita da shi ƙasashen waje a jihar Jigawa ake nomawa, sai dai a shekaru biyu da suka gabata manoman na zoɓo sun ɗan fuskanci kalubale a harkar. Ku...

Apr 30, 202513 min

Ghana ta bai wa 'yan ƙasashen waje wa'adin ficewa daga kasuwancin zinare

Yau shirin ya yada zango ne ƙasar Ghana, inda ya mayar da hankali kan matakin gwamnatin ƙasar na bai wa ƴan ƙasashen waje wa'adin ficewa daga kasuwancin zinare. Ƙasar Ghana ta bai wa ƴan ƙasashen waje da su fice daga harkokinta na kasuwancin zinare a ƙarshen wannan wata na Afirilu a wani mataki na bunƙasa kananan masu hakar zinare na cikin gida da kuma samun ƙudin shiga. Ƙasar ta yammacin Afirka dake kan gaba a samar da zinare a nahiyar na ƙokarin tsaftace harkokin harƙar zinare ta hanyar daidai...

Apr 23, 202510 min

Tasirin sabbin harajin Amurka ga ƙasashen Afirka masamman Najeriya

Shirin 'Kasuwa A kai Miki Dole' na wannan makon ya mayar da hankali kan tasirin matakin shugaban Amurka Donald Trump kan shirin sa na sanya gagarumin ƙarin haraji ga kusan ɗaukacin ƙasashen duniya, wanda ya jawo durƙushewar kasuwannin hannayen jari ta duniya da lalata alaƙa tsakanin ƙasar da ƙawayenta, duk da cewa ya yi amai ya lashe wajen dakatar da harajin da watanni uku masu zuwa. Shirin ya duba tasirinsa ga ƙasashen Afirka masamman Najeriya.

Apr 16, 202510 min

Barazanar da mamayar ƴan China ke yi ga kasuwanci a sassan Najeriya

Shirin Kasuwa A Kai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan makon ya yi dubi ne kan halin da fannin kasuwanci ke ciki a Najeriya sakamakon barazana ko ƙoƙarin mamaya da ƴan ƙasar China ke yi, wanda aka tabbatar da irin illar da ayyukansu ke haifarwa ga ƴan kasuwa da kuma tattalin arziƙin ƙasar. Ba sabon abu bane yadda ake samun ƴan ƙasar China da ke aikata abubuwan rashin ɗa'a kama daga ɓangaren haƙar ma'adai ba bisa ƙa'ida ba, yin kutse ga ƴan kasuwa, zamba cikin aminci a intanet da sauransu. Sai...

Apr 02, 202510 min

Ƙananan kamfanoni na taka rawa wajen bunkasa tattalin arzikin yankin Sahel

Shirin Kasuwa akai miki dole na wanan makon tareda Ahmed Abba ya yada zango ne jihar Maradi dake jamhuriyar Nijar, inda ya mayar da hankali kan rawar da kannan kamfanoni ke takawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasar dake yankin Sahel. Ku latsa alamar sauti domin jin cikakken shirin......

Mar 26, 202510 min

Gwamnatin jihar Neja a Najeriya ta janye haraji kan ƙananan ƴan kasuwa da masu talla

Shirin KASUWA AKAI MIKI DOLE na wanan makon ya maida hankali ne kan matakin da gwamnatin jihar Neja ta ɗauka na janye haraji kan ƙananan ƴan kasuwa da masu talla a faɗin jihar, a wani mataki na bunƙasa ƙananan ƴan kasuwa tare da samar wa da al'umma sauƙi a jihar. Ku latsa alamar sauti domin jin cikakken shirin......

Mar 12, 20259 min

Dalilan da suka sanya farfaɗowar darajar Naira a kasuwar musaya

Shirin ‘Kasuwa a kai miki Dole’ tare da Nura Ado Suleiman ya tattauna kan farfaɗowar darajar Naira a kasuwar hada-hadar canjin kuɗaɗen ƙasashen ƙetare, musamman ma a kan Dalar Amurka, nasarar da wasu ke ganin ta biyo bayan manufofin da babban bankin Najeriya CBN ke aiwatarwa. Bayanai dai sun nuna cewa darajar Naira na ta ƙaruwa ne kusan a kowace rana tun daga watan Janairun wannan shekara da mu ke ciki ta 2025. Nasarar da wasu Magidanta suka ce sun shaida samun ta, la’akari da sauƙin da aka fara...

Mar 05, 202510 min

Yadda ake samun sauƙin farashin kayayyakin masarufi a sassan Najeriya

A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan yadda ake kara samun saukar farashin kayan masarufi a sassan Najeriya. Bayanai da muka tattaro na nuni da cewa yawancin kayayyakin da farashin su ya sauka na amfanin gona ne da kuma na kamfanonin kasashen waje, amma na kamfanonin cikin gida har yanzu suna nan a yadda suke. A makon jiya Hukumar ƙididdiga ta Najeriya NBS, ta ce an samu sauƙin matsalar hauhawar farashin kayayyakin masarufi a ƙasar da a ƙalla kashi 10.3. Cikin sanarwar da ta fitar a T...

Feb 26, 202510 min

Hasashen masana kan makomar tattalin arziƙin Najeriya a shekarar 2025

Shirin kasuwa a kai miki dole na wannan makon ya yi duba ne akan hasashen masana game da makomar tattalin arzikin Najeriya a shekarar nan ta 2025. Masana dai sun daɗe da bayyana wasu hanyoyi da ake amfani da su wajen hasashen makomar tattalin arziƙin ko wacce kasa, yanki ko nahiya a faɗin duniya. Latsa alamar sauti domin sauraren cikakken shirin....

Feb 05, 202510 min

Yadda kasuwancin Internet ke bunkasa tattalin arzikin kasashe masu tasowa

A wannan mako shirin ya tattauna ne kan rawar da kasuwancin Intanet ke takawa wajen bunkasar tattalin arzikin kasashe irinsu Najeriya. Kasuwanci ta internet da ake kira da e-commerce a turance, na taka muhimmiyar rawa wajen sauya yadda ake gudanar da harkokin siye da siyarwa a duniya tare da habakar tattalin arziki. A Najeriya, masana sun yi ittifakin cewa kasuwanci internet wato e-commerce na kawo sauyi ga tattalin arzikin kasar, tare da samar da ci gaba ta fuskoki da dama, da kuma samar da ayy...

Jan 22, 202510 min

Gobarar kasuwar kayan gwanjo mafi girma a duniya ya tagayyara ƴan kasuwa a Ghana

Shirin 'Kasuwa a kai Miki Dole' na wannan makon ya mayar da hankali kan asarar da ƴan kasuwar Kantamanto na ƙasar Ghana suka tafka sakamakon gobarar da ta lakume kasuwar ƙurmus.Hukumomi a Ghana sun ce mummunar gobara da ta tashi a kasuwar kayan gwanjo mafi girma a duniya ranar 2 ga watan Janairun wannan shekara ta 2025 ta lakume sama da shaguna dubu 7 tare da tagayyara ƴan kasuwa sama da dubu 30, inda akalla mutun guda ya mutu wasu 14 suka jikkata.

Jan 14, 202510 min

Yadda aka samu hauhawan farashin kayan abinci a kudancin Najeriya

Shirin kasuwa akai miki dole zai mayar da hankali ne kan yadda farashin kayan abinci ya ke hauhawa a Najeriya, daidai lokacin da ake shirye shiryen bukukuwan Kirsimeti, musamman a kudancin ƙasar, inda a halin yanzu farashin buhun albasa yakai sama da ₦320,000 yayin da buhun shinkafa ƴar gida yakai ₦120,000. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba..........

Dec 18, 202410 min

Bankin duniya ya ayyana Najeriya a matsayin ƙasa ta uku wajen cin bashi a duniy

Wani rahoton Bankin Duniya ya nuna cewa Najeriya ce ƙasa ta uku a yawan basususun kasashen ketare, bayan da ta ƙarbi sama da dalar Amurka biliyan 16.5 kwankwacin naira Triliyan 27 da biliyan 700. Da wannan matsayi Najeriya ta na biye ne da ƙasashen Bangladesh mai matsayi na ɗaya da Pakistan ta biyu a yawan basussuka a duniya. Sabon rance Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da majalisar dattawan najeriyar ta sahalewa shugaba Tinubu karbo sabon rancen naira Tiriliyan 1 da biliyan 700, duk da ikir...

Nov 27, 202410 min

Faɗuwar darajar Naira na shafar kasuwancin dabbobi a iyakar Najeriya da Nijar

'Shirin Kasuwa A kai Miki Dole' na wannan makon tare da Ahmed Abba ya duba yadda harkokin kasuwanci ke tafiya a kasuwar dabbobi ta ƙasa da ƙasa da ke Maigatari ta Jihar Jigawa, wato kan iyakar Najeriya da Nijar, da kuma jin irin ƙalubalen da kasuwar ke fuskanta. Kasuwar ta Maigatari wadda ke iyakar Najeriya da Nijar na daya daga cikin manyan kasuwannin dabbobi a yankin arewacin Najeriya, domin ana sayar da nau'ikan dabbobi da suka hadar da shanu, raƙuma, dawaki, tumaki, awaki da jakkai sama da m...

Nov 07, 202410 min

Yadda ƴan kasuwa tsakanin Najeriya da Kamaru ke fuskantar kalubalen rashin hanya

Shirin Kasuwa Akai Miki Dole na wannan makon ya maida hankali ne kan hada-hadar kasuwaci tsakanin Najeriya da makwabciyarta Kamaru, da irin kalubalen da ƴan kasuwar Kamaru da diribobi daga ƙasashen biyu ke fadi tashi a kan iyakokin ƙasashen biyu. Ƴan kasuwar ƙasashen biyu na amfana da juna, a wasu manyan hanyoyin 10 da a hukumance aka san da su da suka hada na mota da kuma ruwa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba.........

Oct 09, 202410 min

Najeriya: Yadda ambaliyar ruwa ta kassara tattalin arzikin al'ummar Maiduduri

Shirin 'Kasuwa A kai Miki Dole' na wannan makon tare da Ahmed Abba ya leka ne jihar Barno da ke arewa maso gabashin Najeriya, inda ya mayar da hankali kan tasarin tattalin arziki da ambaliyar baya-bayan nan ya haifarwa jihar da ma al'ummarta. Makonni biyu kenan tun bayan mummunar ambaliyar ruwa da ta afkawa wasu anguwannin birinin maiduguri na jihar Borno da kewaye, a ranar 10 ga wannan watan Satumba, iftila'in da ya haifar da asarar rayuwa da dukiyoyi mai tarin yawa, tare da lalata gidaje da ka...

Sep 25, 202410 min

Ƙarin farashin man fetur ya sake jefa iyalai da dama a halin tsaka mai wuya

Shirin kasuwa a kai miki dole tare da Ahmed Abba a wannan mako ya mayar da hankali kan matsi da tsadar rayuwa da kuma yadda wannan matsala ta jefa kaso mai yawa na magidantan Najeriya a halin tsaka mai wuya, matsalar da ke da nasaba da sabbin manufofin gwamnati ciki har da ƙarin farashin man fetur.

Sep 11, 202410 min

Yadda gwamnan CBN ya kashe naira biliyan 60 wajen siyen motocin alfarma

Shirin "Kasuwa akai miki dole" tare da Ahmed Abba a wannan makon ya mayar da hankali ne kan matakin Babban Bankin Najeriya CBN na sayen motocin sulke na katsaita guda shida da ƙudin su ya haura naira biliyan 60, wanda gwamnan bankin da mataimakansa za su yi amfani da su, daidai lokacinda ƴan ƙasar ke fama da tsananin tsadar rayuwa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Ahmed Abba......

Sep 04, 202410 min

Tasirin da tsarin musayar zinare ga makamashi ya yi ga tattalin arzikin Ghana

Shirin kasuwa akai miki dole tare da Ahmed Abba a wannan mako ya waiwayi shirin gwamnatin Ghana na ban gishiri in baka manda a musayar zinare da man fetir, duk dai a ƙoƙarin da ƙasar ke yi na haɓaka tattalin arziƙinta. Tun a bara ne gwamnatin na Ghana ta ƙaddamar da tsarin na ban gishiri in baka manda, wanda ta ƙarbi tan dubu 40 na man disel da ƙudinsu ya kai dala miliyan 40 wajen musanya da zinare da ƙasar ke da arzikinsa. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin......

Aug 28, 202410 min
For the best experience, listen in Metacast app for iOS or Android
Open in Metacast