Barazanar da mamayar ƴan China ke yi ga kasuwanci a sassan Najeriya - podcast episode cover

Barazanar da mamayar ƴan China ke yi ga kasuwanci a sassan Najeriya

Apr 02, 202510 min
--:--
--:--
Listen in podcast apps:
Metacast
Spotify
Youtube
RSS

Episode description

Shirin Kasuwa A Kai Miki Dole tare da Ahmed Abba a wannan makon ya yi dubi ne kan halin da fannin kasuwanci ke ciki a Najeriya sakamakon barazana ko ƙoƙarin mamaya da ƴan ƙasar China ke yi, wanda aka tabbatar da irin illar da ayyukansu ke haifarwa ga ƴan kasuwa da kuma tattalin arziƙin ƙasar.

Ba sabon abu bane yadda ake samun ƴan ƙasar China da ke aikata abubuwan rashin ɗa'a kama daga ɓangaren haƙar ma'adai ba bisa ƙa'ida ba, yin kutse ga ƴan kasuwa, zamba cikin aminci a intanet da sauransu.

Sai dai ana zargin har izuwa yanzu, babu wani tsatsauran mataki na azo a gani da gwamnatin ƙasar ta ɗauka wurin kawo ƙarshen irin waɗannan laifuffukan da ake samun ƴan ƙasar na yi a Najeriya. 

Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.

For the best experience, listen in Metacast app for iOS or Android
Open in Metacast
Barazanar da mamayar ƴan China ke yi ga kasuwanci a sassan Najeriya | Kasuwanci podcast - Listen or read transcript on Metacast