Episode description
Shirin 'Kasuwa a kai Miki Dole' na wannan makon ya mayar da hankali kan asarar da ƴan kasuwar Kantamanto na ƙasar Ghana suka tafka sakamakon gobarar da ta lakume kasuwar ƙurmus.Hukumomi a Ghana sun ce mummunar gobara da ta tashi a kasuwar kayan gwanjo mafi girma a duniya ranar 2 ga watan Janairun wannan shekara ta 2025 ta lakume sama da shaguna dubu 7 tare da tagayyara ƴan kasuwa sama da dubu 30, inda akalla mutun guda ya mutu wasu 14 suka jikkata.
For the best experience, listen in Metacast app for iOS or Android
Open in Metacast