Rabon gado a wurin musulmi tarbiyyace da ta samo asali a cikin addinin, amma a yanzu magada da dama na kukan yadda 'yan uwansu ke cinye musu gado da aka bari kafin a raba ko kuma in an raba. Ko kun san dalilan da ke sa a cinye gado a wannan zamanin kuwa? Shirin Daga Laraba na wannan mako ya dubi irin mawiyacin halin da rabon gado ya stinci kansa a ciki, wanda ke jefa magada da dama cikin tasku.
Aug 24, 2022•30 min
Maganin mata da aka fi sani da kayan mata ya samu karbuwa a tsakanin mata musamman na Arewacin Najeriya. Amma wai da gaske ne waɗannan hade-haden da mata ke sha wani lokacin kuma su yi kunzugu dashi na amfanin da ake saya domin sa? Shirin Daga Laraba ya bigi jaki ya bigi taiki, domin kuwa ya tattauna da masu hada irin wadannan magunguna da masu saya, da ma wadanda ake saya domin su da kuma likitoci domin fayyace gaskiyar amfani da illar kayan mata. Domin sauke shirin kai tsaye latsa nan...
Aug 17, 2022•30 min
’Yan Arewacin Najeriya akalla 200 ne ke tsare a hannun jami’an tsaron yankin Kudu maso Yammcin Najeriya (Amotekun), cikinsu har da fasinjoji 19 da suka shafe wata 10 a tsare. Shin Amotekun halastacciyar kungiya ce a Najeriya kuma tana da harumin tsare ’yan kasar haka kawai? A shirin namu na yau, za ku ji halin da ’yan Arewa da Aamotekun ta tsare suke ciki da matsayin doka a kan kungiyar da kamen da ta yi da kuma yadda za a shawo kan lamarin.
Aug 10, 2022•31 min
Shin da gaske ne ‘Kurkura’ na maganin basir, ko dai shigo-shigo ba zurfi ake yi wa jama’a su fara shaye-shaye? Kurkura wani magani mai guba da kuma sa maye nan take idan an zuba shi a baki. Sai dai kuma duk da haka, yana ci gaba da samun kasuwa a tsakanin jama’a musamman a Arewacin Najeriya da sunan maganin basir da karin kuzari. Shirin Daga Laraba na wannan makon ya yi wa wannan batu duba na musamman ta hanyar tattaunawa da masu sayarwa, masu sha da kuma likitoci.
Aug 03, 2022•31 min
Hukumar Zabe ta kasa, INEC; za ta rufe Yin rajistar katin Zabe ranar Lahadin nan Mai zuwa, wato 31 ga watan nan na Yuli. Idan za a iya tunawa hukumar Zaben ta kara wa'adin yin rajistar katin Zabe na wajen wata daya. Amma duk da haka, jama'a da dama na korafe -korafen cewa lokacin bai ishe su ba, tunda har yanzu akwai mutane adadun da ba su yi rajistar ba. Mun tattauna da 'yan Najeriya, da hukumar ta INEC.
Jul 27, 2022•30 min
Ko me ya sa harkar ilimi, musammam a Arewacin Najeriya sai kara tabarbarewa yake yi, har yana neman mutuwa? A makonnin baya, mun kawo muku yadda harkokin ilimi ke tafiya a jihohin Bauchi, Kebbi, Sakkwato da Zamfara. Yau ga mu a Jihar Kano, inda muka yi tankade da rairaya kan yadda dalibai ke yawan faduwa jarabawar kammala sakandare ta WAEC da NECO da kuma JAMB, wadda ake zanawa domin sharar fagen shiga jami’a. Mun tattauna da dalibai da kuma masu ruwa da tsaki a kan wannan lamari....
Jul 20, 2022•30 min
Idan ana biye da mu, a cikin shirin Daga Laraba na makon jiya, mun tattauna ne a kan harkar ilimin jihar Sakkwato, a wannan makon kuma, mun tabo harkar ilimin jihar Zamfara ne. Ilimi aka ce shi ne gishirin zaman duniya, amma idan ba ilimi, sai jahilci ya yi katutu. Masana da masu ruwa da tsaki a harkar ilimin jihar Zamfara, sun alankanta rashin tsaro a matsayin matsala ta farko kuma babba da ke ci wa ilimi a jihar tuwo a kwarya. Shirin Daga Laraba ya leka Jihar Zamfaran inda ya tattauna ya kuma ...
Jul 13, 2022•30 min
Idan ba ku manta ba, makonni biyu da suka gabata, mun tattauna ne a kan tsarin ilimin Jihar Bauchi da na Jihar Kebbi. A wannan makon kuma mun karkata ne zuwa kan tsarin ilimin Jihar Sawkwato. A yayin da ilimin daliban firamare da sakandare ke tabarbarewa, iyaye da malamai na kokawa kan irin kalubalen da baganren ilimin jihar ke fuskanta. Laifin waye kuma ina mafita? Shirin Daga Laraba ya tattauna da masu ruwa da tsaki.
Jul 06, 2022•30 min
Batun lalacewar harkar ilimi a Jihar Kebbi ba sabon labari bane a kunnuwan 'yan Najeriya, musamman batun daliban da ke jarrabawar sharar fagen shiga jami'a. An jima ana kwarmata batun lalacewar gine-gine da rashin kwararrun malamai da kayan koyarwa a jihar, domin samar da ilimi mai inganci. A wannan karon, shirin Daga laraba ya yada zango a bangaren ilimin Jihar Kebbi domin bankado irin badakalar da bangaren ke ciki da niyyar neman mafita.
Jun 29, 2022•30 min
Rahotanni kan halinda makarantu da karatun boko ke ciki a Jihar Bauchi na cigaba da janyo takaddama a tsakanin jama'a. Biyo bayan sabbin tsare-tasren da gwamnatin jihar ta kawo. Wadanne tsare-tsare ne wadannan da jama'a ke tattaunawa akansu, kuma ta wadanne hanyoyi suka shafi rayuwar jama'a. Shirin Daga Laraba na wanna mako ya yada zango a Jihar Bauchi domin binciko gaskiyar abinda ke faruwa.
Jun 22, 2022•30 min
A yan shekarunnan amfani da bidiyon tsiraici domin cinma burika ke neman zama ruwan dare a cikin jama'a. Mene ne akayi ba dai-dai ba har wannan dabi'a ta samu karbuwa a tsakanin matasa da wadansu manyan? Mun tattauna da masu ruwa da tsaki domin gano bakin zaren.
Jun 15, 2022•30 min
Sau da dama ana samun rashin jituwa tsakanin dangin miji da matar dan uwansu, a wadansu lokutan ma har ya kai ga ya shafi 'ya'yansu. Daga ina matsalar take, sannan me ake yi ba daidai ba? Mun tattauna da masu ruwa da tsaki domin neman mafarin wannan fitina da kuma hanyoyin da za a bi domin warware ta.
Jun 08, 2022•30 min
Mutane da dama na tura 'ya'yansu wurin kakanninsu da sunan ziyara ko su zauna su rayu dasu da sunan taimakon kakannin. Anya taimako ne kuwa? lura da yadda rainon mutum yake da wahala, kaiwa mutum mai shekaru raino ba janyo sabuwar wahala bane? Shirin namu na yau ya mayar da hankali akan wannan dabi'a. mun tattauna da wadansu kakanni da kuma malaman addini domin sanin gaskiyar abinda ya sa ake hakan. Sun kuma bada shawara domin inganta zamantakewa.
Jun 01, 2022•30 min
A cigaba da ayyukan 'yan ta'addan IPOB a Kudu maso Kudancin Najeriya, yan kungiyar sun kai farmaki yankunan da Hausawa ke zaune inda suka hallaka wata mata mai dauke da cikin wata tara da 'ya'yan ta hudu a Isolo dake Jihar Anambra. Bayan nan rahotanni da muka samu sun nuna cewa a kasa da awa 24 bayan kashe matar nan da 'ya'yanta, yan haramtacciyar kungiyar sun sake kashe wasu yan acaba 4 sun kuma kone gawar daya daga cikin su, sannan kuma sun kashe wani mahauci. Ko wane hali 'yan Arewa mazauna y...
May 25, 2022•30 min
A makon da ya gabata mun binciko matsalolin matasan Arewa da kuma dalilan da aka bar su a baya. A shirinmu na wannan karon mun tattauna da wadansu matasan yankin, wadanda da suka san matsalolinsu da kuma maganin matsalolin. Matasan sun bayyana ainihin abin da ke hana su ci gaba, sun kuma bayar da shawarwari kan hanyoyin da za a shawo kan matsalolin nasu.
May 18, 2022•30 min
Yara manyan gobe, inji Hausawa; amma anya matasan Arewacin Najeriya sun samu damar zama manyan goben yadda ya kamata? In aka yi la'akari da halin da matasan Arewan ke ciki, wani abin tambaya shi ne, ko dai su a yarintar za su kare? Me ke kawo musu wannan tarnaki? Shirin Daga Laraba ya tattaro fahimtar masana da matasa kan ababen da ke mayar da matasan Arewa koma baya.
May 11, 2022•30 min
Ta'addancin 'yan bindiga ya zamo ruwan dare a Najeriya. Domin babu nau'in da ba a gwada irinsa a kasar nan ba. Anya akwai ranar da wannan ta'addanci zai zamo tarihi kuwa? Mene ne ya kamata ayi domin a gaggauta kawo karshen ta'addanci, wane ne ya kamata a sa a gaba domin neman mafita, mene ne ake yi daidai kuma mene ne ake bukatar a gyara? Mazauna yankunan da 'yan ta'adda ke ciwa tuwo a kwarya sun yi mana bayanan halin da suke ciki da kuma tunaninsu dangane da yiwuwar kawo karshen ta'addanci. Mun...
May 04, 2022•30 min
Rashin tsaron da ya addabi yankin Arewa maso Yammacin Najeriya na nema ya gagari kundila. Mene ne ake yi ba daidai ba, wa ya kamata ya amsa tambayoyin da jama'a ke yi kan yadda za a warware matsalolin tsaron? Masana sun yi wa Shirin Daga Laraba na wannan makon bayani kan hanyoyin da suka dace a bi domin warware matsalar da ta ki ci, ta ki cinyewa .
Apr 27, 2022•30 min
Yawan hare-haren da ’yan ta’adda ke kaiwa kan jama'ar da ba su ji ba, ba su gani ba a jihohin Katsina, Zamfara, Sakkwato, Kebbi, Neja da Kaduna, ya sa shakku a zukatan ’yan Najeriya bisa kokarin da Gwamnati ke cewa tana yi. Shirin Daga Laraba na wannan mako ya binciko irin kokarin da gwamnatin ke yi a matakin kasa da jihohin da abin ya fi shafa.
Apr 20, 2022•30 min
Satar mutane domin karbar kudin fansa ya zama ruwan dare a Najeriya. A wane hali mutanen da ake sacewa ke tsintar kansu a hannun masu garkuda da mutane da kuma bayan an sako su? Shin yaya wadanda ke satar mutane ke tunani?
Apr 13, 2022•30 min
A makon da ya gabata, cikin shirin Daga Laraba mun kawo muku bayanin asalin ta'addanci a Arewa maso Yammacin Najeriya, inda kuka ji yadda abubuwa suka faro daga Jihar Zamfara A wannan karon, shirin ya bankado irin asarar rayuka da dukiyoyin da aka yi da kuma yadda zamantakewa ta lalace tsakanin jama'ar wannan yanki a sanadiyyar ta’addancin ‘yan bindiga.
Apr 06, 2022•30 min
Jihar Zamfara ta yi suna a duniya a shekarar 2000, sanadiyyar kaddamar da shari’ar Musulunci. Jama’a sunyi ta zancen Jihar da sa albarka, suna kuma kallon ta a matsayin wani wuri da za a samu wanzuwar adalci saboda abinda ake sa ran wannan sabon tsarin mulkin zai tabbatar. Sai dai a baya-bayanan, Jihar ta tsinci kanta a bakin jama’a a wannan karon ana tir da abinda ke fitowa na ta’addanci da duk wani irin rashin mutunci da mai tunani zai tunano. Daga ina wannan matsala ta samo asali? Su wa ake z...
Mar 30, 2022•31 min
Makonni biyar ke nan da shirin Daga Laraba ya fara fede biri har wutsiya kan batun labaran karya domin gano asalinsa da masu amfana da shi da masu yadawa da kuma amfanin da su ke samu. Yadda Ake Gane Labaran Karya ne batun da shirin Daga Laraba na makon da ya gabata ya mayar da hankali a kai. A wannan makon kuma shirin ya karkata ne kan Irin Kallon Da Addini Ke Yi Wa Labarin Karya. Mun tattauna da malaman addinin Islama da na Kirista domin sanin makomar masu yada shi a wurin ubangiji....
Mar 23, 2022•25 min
Ta wace hanya mutum zai gane labarin karya a kafar intanet ko kuma a kafofin sada zumunta? Wani lokaci bambance labaran karya abu ne mai sarkakiya ta yadda hatta amintattun kafafen yada labarai kan fada a tarko, su dauke su a matsayin sahihan labarai. Tambayar da ke yawan ci wa jama’a da dama tuwo a kwarya ita ce, ta yaya mutum zai gane labarin karya? Shirin Daga Laraba na tafe da bayanan hanyoyin gane labaran karya da zarar an yi ido hudu da su.
Mar 16, 2022•30 min
Makwanni biyu da su ka gabata mun karkata akalar shirin Daga Laraba zuwa batun labaran Karya. Mun dubi wadanda ke yadashi da masu kir kirarshi. A wannan karon, mun tura shirin gaba ta yadda mu ka dubi tasirin da illar labaran Karya ke haifarwa jama'a. Mun tattauna da masu yada labarai ta intanet, da 'yan siyasa da kuma masana a wannan fage domin fede biri har wutsiya.
Mar 09, 2022•29 min
Labaran karya sun samu wurin zama a fagen siyasa, kusan ko’ina aka leka za a iske ’yan saiya na gudanar da harkokinsu ta hanyar amfani da labaran kanzon kurege a matsayin hanyar neman magoya baya da kashe farin jinin abokan hamayya. Shirin Daga Laraba na wannan karon ya yi nazari kan yadda ’yan siyasa ke amfani da kafafen sada zumunta wurin yada labaran bogi domin sace zukatan jama’a da kuma kayar lagon abokan hamayyarsu.
Mar 02, 2022•27 min
Galibi idan aka ambaci labaran karya abin da ke fara zuwa zuciyar mutane shi ne soshiyal midiya, wato kafofin sadarwa na zamani. Amma ko masu sauraro sun taba tunanin cewa yayin hira a majalisa ko teburin shayi, wani ka iya ba da labaran da basu da tushe balle makama? Shirin Daga Laraba na wannan makon na tafe da karin bayani
Feb 23, 2022•32 min
A shirin Daga Laraba da ya gabata kun ji ta bakin wani karamin yaro mai kwacen waya da ya kashe mutum uku, ya raunata wasu akalla 25 sannan ya karbe wayoyi da dama. A yau kuma za ku ji yadda wata baiwar Allah ta safe wata 10 tana fama da irin lalurar da ta samu a sakamakon harin da masu kwacen waya suka sumar da ita sannan suka kashe dan uwanta.
Feb 16, 2022•30 min
Waya na daya daga cikin abubbuwan da ake saurin sacewa amma a fakaice, saboda in a ka kama barawon waya, to yana dan dana kudarshi. Sai dai wani babban abun mamaki shine yadda birni kamar Kano, mai yawan al’umma da tarin jami’an tsaro, ya tsinci kanshi a cikin mawucyacin hali saboda aika-aikar masu kwacen waya a bainar jama’a dare da rana Shirin Daga Laraba na wannan mako, ya zaga birnin Kano domin bin diddigin matsalar, da kuma gano masu aikata laifin, abin da ke sa su, da kuma wuraren da aka f...
Feb 09, 2022•29 min
Samuwar fasahar sadarwa ta zamani ta fadada damar da mutane suke da ita ta samarwa da kuma yada labarai ta hanyoyin zamani musamman kafofin sada zumunta. A hannu guda kuma hakan ya haifar da fantsamar labaran kanzon kurege da a wasu lokuta suke yin illa ga mutuncin jama'a har ma da tayar da zaune tsaye. Shirin Daga Laraba na wannan karon ya bankado yadda aka fara samun labaran bogi, wadanda suka fi yada su da kuma hanyoyin da labaran karyan ke hana ruwa gudu a cikin al'umma. A yi sauraro lafiya....
Feb 02, 2022•31 min