Daga Laraba - podcast cover

Daga Laraba

Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.

Last refreshed:
Follow this podcast in the Metacast mobile app to refresh it and see new episodes.
Download Metacast podcast app
Podcasts are better in Metacast mobile app
Don't just listen to podcasts. Learn from them with transcripts, summaries, and chapters for every episode. Skim, search, and bookmark insights. Learn more

Episodes

Waiwaye: Yadda Rufe Hanyoyin Sadarwa Ya Shafi Harkokin Kasuwanci

Wayar tarho da intanet sun kama hanyar zama jinin jikin al’umma a wannan karni na 21. Alakar mutane da harkokin sadarwa ta zamani ta sa kusan harkokin kasuwanci sun tasamma komawa intanet, a wasu lokutan kuma ana amfani da wayar tarho ne wurin assasa harkokin kasuwanci da kuma tabbatar da su. Shirin Daga Laraba na wannan mako ya yi waiwaye kan irin halin ni-’yasun da harkokin kasuwancin suka shiga a sakamakon rufe layukan sadarwa a kwanakin baya a Jihar Katsina.

Jan 26, 202229 min

Hanyoyin Warware Matsalolin Bayan Jefa Kuri’a

So da dama bayan an kammala jefa kuri’u, masu zabe kan dakata su ga abin da zai ture wa buzu nadi – suna kasawa su tsare, a kirga, a kuma sanar da sakamako. Hakan na faruwa ne saboda wasu matsaloli da kan kunno kai bayan an gama kada kuri’u, wani lokaci har a yi ta kai ruwa rana. Don haka masu zabe ke son su san ko ’yan takarar da suka zaba sun kai bantensu. Shirin Daga Laraba na yau za ku ji irin abubuwan da ke biyo bayan jefa kuri’a, kama daga kidaya kuri’u, har ma da dalilan da zabe ke kasanc...

Jan 19, 202224 min

Yadda Za A Magance Matsalolin Ranar Zabe

’Yan Najeriya na fuskantar matsaloli da dama a lokacin zabe, musamman ranar zabe, duk kuwa da cewa za a iya magance matsalolin idan aka bi hanyoyin da suka dace. Shirin Daga Laraba na wannan makon, ya zakulo irin matsalolin da ake fuskanta a lokacin zabe da kuma hanyoyin da za a bi domin warware su.

Jan 12, 202231 min

Matakan Yin Katin Zabe Domin Kawo Sauyi

Zabe na yi wu wa ne idan a kwai masu zabe, nan da watanni 13 za’a gudanar da babban zabe a Najeriya. Shin kun san yadda zaku yanki katin zabe? Idan kun sauya unguwa ko gari wadanne hanyoyi zaku bi wurin karbar sabon katin da zai baku damar zabe a duk inda kuke? Shirin Daga Laraba na wannan makon ya tattaro bayanan matsalolin da a ke fuskanta wurin yankar katin zabe, da hanyoyin da za’abi wurin warwaresu a cikin sauki.

Jan 05, 202230 min

Yadd kuri'arku za ta iya sauya rayuwarku

Tun da aka dawo mulkin Dimokuradiyya a Najeriya a 1999, yawan masu kada kuri’a sai raguwa yake ta yi, ko mene ne dalili? Anya masu zabe sun san irin karfin da kuri’arsu take da shi kuwa? Shirin Daga Laraba na wannan lokaci na tafe da amsar wannan tambaya har ma da bayanin amfanin zabe da muhimmancinsa wurin kawo sauyin rayuwa mai ma’ana. A yi sauraro lafiya.

Dec 29, 202129 min

Karfin Ikon Talakawa A Dimokuradiyyar Gaskiya

An fara mulkin dimokuradiyya ne a Karni na 17 bayan kafa kasar Amurka, jim kadan bayan juyin juya hali. Shi ne tsarin mulkin da ya bai wa ′yan kasa damar fadin yadda suke so a mulke su. Hakan ta sa suke da damar tofa albarkacin bakinsu a harkokin gwamnati ta hanyar wakilansu da suka zaba zuwa majalisu a matakai daban-daban. Shirin Daga Laraba na wannan karon na kunshe da bayani kan nau’ikan tsarin dimokuradiyya da kuma yadda take tafiya a Najeriya, Afirka da ma sauran kasashen da suke morar tsar...

Dec 22, 202135 min

Illolin da rashin kaunar juna ke yi wa mata

A shirin Daga Larabar da ya gabata, mun yi duba ne a kan Dalilan Da Mata Ba Sa Kaunar Junansu. A kashi na biyu da za ku saurara a wannan karon kuma, shirin ya mayar da hankali ne kan yadda rashin kaunar juna a tsakanin mata ke hana musu ci gaba a fannoni da dama na rayuwa. A yi sauraro lafiya.

Dec 15, 202131 min

Dalilan Da Mata Ba Sa Kaunar Junansu

Mata na yawan ambaton kansu da zumunci a tsakaninsu har sukan bugun kirji da cewa ‘ciwon ’ya mace na ’ya mace ne.’ Amma a zahiri ko takarar siyasa mace ta tsaya, ’yan uwanta mata ke fara yaƙarta kafin maza? Me ya sa kishi ya yi yawa a zukatan mata har ba sa iya bari mijinsu ya auro kawarsu su zama abokiyan zama? Ina ciwon ’yan macen? Shin ko’ina haka abin yake, ko a Najeriya ne kadai? Shirin Daga Laraba na wannan lokaci ya rairayo manyan dalilan da mata ke yawan samun rashin jituwa a tsakaninsu....

Dec 08, 202130 min

Yadda 'Yan Siyasar Kano Ke Hana Jihar Ci Gaba

Masana sun bayyana yadda ’yan siyasar Kano ke hana Jihar ci gaba, lura da yadda siyasar gaba ta maye gurbin siyasar hamayya da kishin jihar. Shirin Daga Laraba na wannan karon ya yi waiwaye kan yadda aka faro siyasar Kano, wuraren da aka wuto, da kuma halin da ake ciki a yau.

Dec 01, 202131 min

Kunci da wulakancin da zawarawa ke fuskanta

sanin gaskiyar halin da zawarawa ke ciki sai in ka sauraresu, wai me ya sa ba'a son auren bazawara, wa ya kamata ya dauki nauyin ta, shin zawarci zabin kai ne, ko kuma kaddara ce, ya ya mutane ke kallon bazawara? Saurari irin halin kuncin da mata ke samun kansu da zarar sun rasa auren su.

Nov 24, 202130 min

Auren Wuf: Soyayya ko kwadayi?

Mutane na yiwa auren wuf ko auren caraf fassara daban-daban lura da yadda auren yake. wasu na ganin auren wuf a matsayin auren cin kasuwar bukata, amma a zahiri me yasa akeyin auren wuf, meye alfanun yin shi, yanada illa ko kuwa?

Nov 17, 202130 min

Illolin da bilicin ke haifar wa lafiyar masu yi

A shirin Daga Laraba da ya gabata, mun tattauna dabi’ar bilicin, wato jeme launin fatar jiki daga baka ta koma fara. A yau za ku ji illolin da bilicin ke haifar wa lafiyar masu yi, kuma za ku ji yadda wannan dabi’a ta bilicin ta mamaye, daga maza har mata.

Nov 10, 20211 hr

Me ya sa ake bilichin?

A wannan karon, shirin Daga Laraba ya mayar da hankali ne a kan masu canza wa kan su kama. Masu canza launin fatar jikinsu daga baka ta koma fara. Wato masu Bilichin. A kashin farkon shirin, mun duba dalilan da ke sa mutane su na canza kamanninsu da Allah Ya halicce su da shi.

Nov 03, 202133 min

Abin Da Ke Sa Mace Ta Fara Neman Namiji Da Aure

Shirin Daga Laraba ya yi duba na musamman a kan dalilan da ke sa mace ko hana ta fara neman na da miji aure idan har yana da nagartar da ta dace da zabinsu na abokin rayuwa. Me ya sa ita mace jira take yi sai an zo? Ba a taba yi ba ne a tarihin magabata? Saurari cikakken shirin domin jin amsoshin wadannan tambayoyin.

Oct 27, 202136 min

Dalilan Mutuwar Kishin Kasa A Zukatan 'Yan Najeriya

Jama'a da dama na mamakin yadda 'yan Najeriya basa kishin kasarsu. Shirin Daga Laraba na wannan karon ya bankado dalilan da suka harzuka da yawa daga cikin 'yan Najeriyan har aka wayi gari kasar ta fita daga ransu. Wasudai na ganin soyayya tana wanzuwa idan kowane bangare na amfana, amma 'yan Najeriya sunce manyan kasar ba ta su sukeyi ba. Ayi Sauraro lafiya.

Oct 06, 202148 min

Wane Ne Ke Yada Labaran Karya?

Yaya za ki ji idan, ana saura kwana kadan a daura aurenki, angon ya ce ya fasa saboda an turo mishi wani sako da ke nuna wani aibi da bai sani ba game da ke? Kuma me ya sa? Mai yiwuwa tunani na farko da zai zo zuciyarki shi ne, wane ne ya yada wannan karyar a kanki? A zamanin nan, labaran karya na yaduwa kamar wutar daji, yana kuma haddasa rudani a rayuwar mutane da dama.

Sep 29, 202145 min

Anya Camfi Zai Fita Daga Zukatan Mutane Kuwa?

Camfi wani abu ne da mutane a ko wanne bangare na duniya kan yi amanna da shi kuma ya zama bangare na al'ada. Mene ne asalin camfi? Zai iya fita daga zukatan mutane kuwa? A wannan karon, shirin Daga Laraba ya yi nazari a kan camfi da tasirinsa a rayuwar al'umma.

Sep 22, 202141 min

Yadda Aka Ceto Mutum 638 Da Ake 'Bautarwa' A Arewacin Najeriya

Yaran da ake kaiwa birni da sunan aiki na cikin halin ni-'yasu - abin dai ya yi kama da bauta. Hukumar Yaki da Safarar Mutane ta Najeriya (NAPTIP) shiyyar Arewa Maso Yamma ta ce ta ceto mutum 638 da ake bautatarwa a cikin wannan shekarar.

Sep 15, 202140 min

Fina-Finan Hausa: Gina Al'umma Ko Ruguza Tarbiya?

An jima ana takun saka tsakanin masu ruwa da tsaki a harkar shirya fina-finan Hausa, Kannywood, da wani bangare na al'umma bisa zarge-zarge ko korafe-korafe daban-daban. Daya daga cikin zarge-zargen shi ne na bata tarbiya. Ko me ya sa har yanzu masu harkar suka kasa sauya ra’ayoyin jama’a game da wannan zargi? Ku biyo mu ku ji yadda Dokta Abdallah Usman Gadon Kaya ya yi ragargaza, da kuma yadda Ali Nuhu ya kare masana'antar.

Sep 08, 202141 min

Yadda 'Yan Siyasa "Ke Mayar Da Matasa 'Yan Kwaya"

Idan kuna biye da mu a shirye-shiryenmu biyu da suka gabata, mun tattauna a kan matsalar shaye-shaye, sannan muka duba wadanda ke amfana da harkar shaye-shayen a Najeriya. A wannan karon kuma mun mayar da hankali ne a kan rawar da ake zargin ’yan siyasa na takawa wajen gurbata wa matasa tarbiyya, da lalata musu makoma ta hanyar saka su shaye-shaye don su cimma wata manufarsu ta siyasa.

Sep 01, 202130 min

Wane Ne Ke Amfana Da Kayan Shaye-Shaye A Najeriya?

A shirin Daga Laraba da ya gabata, mun tattauna a kan matsalar shaye-shaye da yadda ta addabi al'umma a Najeriya. A wannan karo za mu duba mu ga shin su wane ne suke amfani da kayan maye?

Aug 25, 202129 min

Halin Ni-'Ya-Su: Wa Ya Kamata Ya Jikan 'Yan Gudun Hijira?

Mummunan halin da 'yan gudun hijira ke ciki a sansanoni daban-daban a wasu sassan Najeriya ba bakon abu ba ne. Abin da kan zama bako shi ne samun wani mawadaci ko kungiyar mawadata su tallafa wa wadannan mutane. A wannan shiri na Daga Laraba mun duba abin da ya sa masu hannu da shuni ba su cika taimaka wa wadannan bayin Allah ba.

Aug 11, 202131 min

Abin da ke kawo yawan sakin aure a kasar Hausa

Mutuwar aure kullum karuwa take yi a Arewacin Najeriya. Mene ne dalili, kuma laifin wane ne? Daga ina matsalar ta samo asali? Mece ce mafita? A wannan karon, shirin Daga Laraba ya yi kokarin nemo amsoshin wadannan tambayoyi da ma fahimtar masana a kan wannan matsala.

Aug 04, 202131 min

Abin Da Ya Sa ’Yan Najeriya Ke Rashin Lafiyar Kwakwalwa

Matsalar rashin lafiyar kwakwalwa da jirkicewar tunani larura ce da kwararrun likitoci ne kadai ke iya maganinta An dai kiyasta cewa 'yan Najeriya miliyan 20 ne ke fama da wannan larura. A wannan karon, mun tattauna a kan me ke kawo matsalar, da kuma hanyoyin da za a bi domin kauce mata, da magance ta.

Jul 28, 202131 min

Tsadar kayan abinci: 'Yan Najeriya na dandana kudarsu

A wannan karon, shirin "Daga Laraba" ya baje tsananin tsadar kayan abinci a faifai don gano abin da ya haddasa ta, wane ne ya haddasa ta, dalilin haddasa ta, da hanyoyin magance ta. 'Yan kasuwa da masana da sauran masu ruwa da tsaki sun bayyana dalilan tsadar, sun kuma bayar da shawarwari a kan yadda za a rage radadin da talaka ke fama da shi.

Jul 21, 202131 minSeason 1Ep. 10

Yadda Hadurra ke lakume Rayukan Dubban 'yan Najeriya

Wasu alkaluma da Hukumar Kiyaye Hadurra ta Tarayya (FRSC) ta fitar sun nuna cewa a wata guda kawai mutane 1,059 ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon hadurran mota a Najeriya. A wannan karon, "Daga Laraba" ya duba yawan hadurra da dalilan da ke haddasa su da masu haddasa su da yadda za a yi a rage su.

Jul 14, 202127 min

Yadda Cin Hanci Da Rashawa Ke Kassara Rayuwar Al'umma

Ko kun san cewa da dama daga cikin matsalolin da talakan Najeriya ke fuskanta a yanzu haka cin haanci da rashawa ne suka haddasa su? A wannan karon, shirin "Daga Laraba" ya yi nazari a kan alakar wadannan abubuwa - wato cin hanci da rashawa da kuma bakin talaucin da wahalar da al'umma ke fama da su. Ku biyo mu don jin yadda aka yi aka haihu a ragaya.

Jul 07, 202134 min
Hosted on Buzzsprout
For the best experience, listen in Metacast app for iOS or Android