Daga Laraba - podcast cover

Daga Laraba

Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.

Last refreshed:
Follow this podcast in the Metacast mobile app to refresh it and see new episodes.
Download Metacast podcast app
Podcasts are better in Metacast mobile app
Don't just listen to podcasts. Learn from them with transcripts, summaries, and chapters for every episode. Skim, search, and bookmark insights. Learn more

Episodes

Yadda kwacen waya ke ajalin jama'a a Najeriya

A wasu sassan Najeriya, rike wayar salula kan zama hadarin da ka iya haifar da sara ko suka ko ma mutuwa idan ajali ya yi. A wannan karon, "Daga Laraba" ya duba yadda wannan matsala ke karuwa da illar da take haifarwa da kuma hanyoyin magance ta ko kauce wa fada mata.

Jun 30, 202132 minSeason 1Ep. 7

Hidimar aure: Wa ya fi jin jiki tsakanin dangin ango da na amarya?

Sau da yawa, iyayen yarinya kan dage ranar aure saboda ba su kammala shirye-shiryen biki ko sayen kayan daki ba. Samari da dama kan bayar da uzuri cewa tsarabe-tsarabe - kama daga dukiyar aure, zuwa ga sadaki zuwa ga lefe - sun yi yawa shi ya sa suka kasa aure. Wai shin, a tsakanin dangin amarya da na ango, wa ya fi shan wahala ko kashe kudi yayin bikin aure? Wannan ne batun da shirin Daga Laraba ya yi nazari a kai a wannan karon.

Jun 23, 202124 minSeason 1Ep. 6

Shin Ana Damawa da Nakasassu a Najeriya?

A wannan makon, shirin DAGA LARABA ya yi nazari a kan halin da masu nakasa suke ciki a Najeriya da kuma inda aka kwana game da aiwatar da dokar kyautata rayuwarsu a kasar.

Jun 16, 202123 minSeason 1Ep. 5

Shekara 22 baya: Wanne alfanu Najeriya ta samu daga Dimokuradiyya?

Asabar 12 ga watan Yuni ce Ranar Dimokuradiyya a Najeriya. Kafin a sauya ranar wannan biki, a da akan yi shi ne ranar 29 ga watan Mayu, ranar da kasar ta koma kan turbar Dimokuradiyya bayan shekaru da dama na mulkin soji. A bana dai shekara 22 ke nan tun bayan komawa kan tsarin na Dimokuradiyya. Ko me wannan tsari ya tsinana wa Najeriya a wadannan shekaru? Mun tattauna da yan Najeriya a kan cigaban da aka samu; sun kuwa bayyana ra'ayoyinsu sun bayar da shawarwari....

Jun 09, 202130 minSeason 1Ep. 4

Wacce hanya za a bi a hana satar mutane?

Shirin Daga Laraba na wannan mako yayi duba izuwa hanyoyin da ya kamata abi domin da'kile satar mutane da biyan kudin fansa a Najeriya. kana ya bayyana adadin kudaden da ake ganin an baiwa masu satar mutane a cikin shekaru tara.

Jun 02, 202118 minSeason 1Ep. 3

Taskun da Ibo Musulmi ke shiga

A wannan shirin mun yi tattaki zuwa yankin Kudu Maso Gabashin Najeriya don ganin irin taskun da Musulmai 'yan kabilar Ibo suka ce suna shiga saboda addinin da suka zaba. A yi sauraro lafiya

May 26, 202116 min

Sharar Fage

A wannan shiri, wanda shi ne na farko a jerin shirye-shiryen "Daga Laraba", muna gabatar muku da muryoyin da za ku rika ji, ciki har da Halima Djimrao, tsohuwar ma'aikaciyar Sashen Hausa na VOA. Za ku kuma ji bayani a kan mene ne podcast, bambancinsa da rediyo, da abin da ya sa Aminiya ta yanke shawarar fara podcast.

May 19, 20219 min
Hosted on Buzzsprout
For the best experience, listen in Metacast app for iOS or Android