Daga Laraba - podcast cover

Daga Laraba

Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.

Last refreshed:
Follow this podcast in the Metacast mobile app to refresh it and see new episodes.
Download Metacast podcast app
Podcasts are better in Metacast mobile app
Don't just listen to podcasts. Learn from them with transcripts, summaries, and chapters for every episode. Skim, search, and bookmark insights. Learn more

Episodes

Abin Da Ke Sa Maza Shan Maganin Karin Kuzarin Auratayya

S han maganin karfin maza ya zama ruwan dare a wannan zamani, ta yadda masu sayar da shi ke yi a bainar jama'a, ba tare jin ko dar ba, sakamakon yadda suke cinikinsa. Shin mene ne dalilin da maza ke shan maganin karfin maza? Shirin Daga Laraba na wannan mako ya ji ta bakin maza da ke shan Wadan nan magunguna, ya tuntubi mata da aka ce ana sha saboda su, ya kuma ji ta bakin likitoci.

Oct 18, 202328 min

Gaskiyar Abin Da Ke Kawo Cutar Basir

Cutar basir daya ce daga cikin cututtukan da jama'a ke sha wa magani ba tare da sun nemi sahhalewar likita ba. Shin da gaske zaki da maiko na haddasa cutar basir? Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci na tafe bayani dangane da abin da ke haddasa cutar basir, da kuma hanyoyin kauce masa a likita ce.

Oct 11, 202328 min

Me Ya Sa Waɗanda Suka Kammala Jami'a Ke Komawa Sana'ar Girke-Girke

A yadda wasu masu sana’o'in suka ginu, ko da za a ajiye musu aikin albashi sun gwammace si cigaba da sana’o’in su. A shirin daga Laraba na yau mun duba yadda matasan da suka kammala jami'a ke komawa sana'ar girike-girke da kayan maƙulashi. To me ya sa matasan suka fara yiwa kansu ƙiyamul-laili, ko cigaba hakan ke haifarwa. Ku biyo mu cikin shirin.

Oct 04, 202329 min

Dalilin Da Ba Za Mu Bari Likita Na Miji Ya Duba Matanmu Ba

A yanayi na rashin lafiya a kan ga wasu maza na tuburewa likita namiji ba zai duba musu iyali ba, musamman wajen haihuwa a asibitoci. Amma akwai matan da su ma a ganin su, kunya kan hana su sakin jiki likitoci maza su duba su. Shirin Daga Laraba na wannan makon ya yi nazari a kan meyasa wasu basu yarda likita namiji ya duba matansu a asibiti.

Sep 27, 202329 min

Matakan Nasara Wajen Neman Aure A Soshiyal Midiya

Samari da 'yan mata da dama sun samu abokan rayuwar su a shafukan sada zumunta, wasu kuma sun gamu da ƙaluabale. Shin da gaske ana aure a soshiyal midiya ko nishaɗi kawai ake yi? Masu haɗa aure a shafukan sada zumunta sun bayar da matakan da za a ɗauka idan ana so a yi nasara. Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba wasu mahimman abubuwa da ya kamata ku sani gameda neman aure a shafukan sada zumunta.

Sep 20, 202327 min

Da Wuya Talakan Najeriya Ya Iya Zuwa Aikin Hajjin Bana

Tun bayan da hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce maniyatta aikin Hajjin 2024 su fara neman kafin alkalamin Naira miliyan 4 da rabi, yan ƙasa ke ta cece-kuce kan wannan labari. Wasu na ganin anya wannan lamari ba zai gagari talaka ba, yayinHda kuma masana da hukumomin ke kare kansu a kan wannan mataki. A cikin shirin daga laraba na wannan mako mun duba dalilan karin kudin aikin Hajji, da kuma abin da yan kasar ya kamata su duba gameda wannan ƙari

Sep 13, 202329 min

Me Ya Sa Juyin Mulki A Wasu Kasashe Ya Dami Tinubu?

Juyin mulkin da ake yi a ƙasashen Afrika a 'yan kwanakin nan yana tayar da hankalin shugabannin yankin, inda suke ta ƙoƙarin ganin an dawo mulkin dimokraɗiyya. Sai dai wasu na ganin yawan tsoma baki da shugaban Najeriya Bola Tinubu ke yi, bai kamata ba musamman ƙasashen da ba su cikin yankin ECOWAS da yake jagoranta. Duk da yake akwai masu ganin girman Najeriya a Afrika ya sa dole ya yi magana. Shirin Daga Laraba na wannan makon ya yi nazari akan abin da ya sa shugaba Tinubu ke saurin tsoma baki...

Sep 06, 202330 min

‘Yadda Rashin Gaisuwa Ya Kashe Aure’

A al’adan bahaushe, gaisuwa wata abu ce mai matuqar muhimmaci a cikin zamatakewar sa ta yau da kullum kuma Gaishe da mutum na daya daga cikin alamomin girmama shi. A ‘yan kwanakin dai nan ana ta taƙaddama akan wane ne ya kamata ya fara gaida wani tsakanin ma’aurata, shin miji ne ko mata. A shirin Daga Laraba na wannan mako, mun duba yadda batun gaisuwa tsakanin ma'aurata yake neman lalata wasu gidajen.

Aug 30, 202330 min

Mun Fi Son Mulkin Sojoji —Al’ummar Nijar

A yanzu ana sati na 4 da juyin mulkin jamhuriyar Nijar da aka yi a ranar 26 ga watan Yulin 2023. Ana ta kai ruwa rana domin ganin an dawo kan tsarin dimokradiyya, inda ECOWAS ta ke son ganin an samu daidaito da ƙarfin soji. Amma 'yan Nijar na bukatar sojoji su ci gaba da mulki a ƙasa, sakamakon yadda suke zanga-zangar nuna goyon baya Shirin Daga Laraba na wannan mako, ya duba dalilin da ya sa ECOWAS ta nace a dawo tsarin dimokraɗiyya idan har 'yan kasar ba su buƙata....

Aug 23, 202327 min

Mece Ce Ribar Kai Gwamnati Ƙara

A duk lokacin da gwamnati ta yunƙuro domin yin wani abun da ya saɓa da ra’ayin talakawa a kan samu ƙungiyoyi masu ƙalubalantar wannan matakin a kotu. Amma irin waɗannan kararraki da kungiyoyin ke shigarwa a kotu da kalubalantar gwamnati suna tasiri kuwa? Meyasa ba kasafai ake jin sun yi nasara ba? Abin da shirin mu na Daga Laraba ya duba a wannan makon kenan.

Aug 16, 202325 min

Matsalolin Zama Nesa Da Iyali

Rayuwar ma'aurata na buƙatar kasancewa kusa da juna domin taimakekeniya da kuma shaƙuwa. Saidai ma'aurata kan shiga damuwa da zarar aka yi nesa da juna, musamman wajen da ya kasance ba makawa sai an je kamar irin su sauyin wajen aiki ko kuma kasuwanci. A cikin shirin Daga Laraba na wannan mako mun duba yadda rayuwar ma'aurata ke kasancewa a lokacin da suka yi nesa da juna.

Aug 09, 202330 min

Abin Da Ya Sa Muke Yin Ciko —’Yan Mata

Shin me ke sa mata sarrafa surar jikinsu ta yadda suke zama son kowa, son wanda ya samu. A shirin Daga Laraba na wannan karo, ’yan mata sun fede biri har wutsiya kan dalilan da ke sa su yi wa surarsu ciko, da kuma tasirin da hakan ke musu. Domin jin taƙaddamar da ke tsakaninsu da maza game da mata masu ciko a jikinsu, sai ku saurari shirin Daga Laraba na wannan makon

Aug 02, 202329 min

"Wahalar Da Mu Ka Sha A Wurin Iyayen Riko"

Sau da yawa ana samun labaran cuzgunawa tsakanin iyayen riko da 'ya'yan riko, sai dai kowa na zargin kowa ne a cikinsu. Mene ne gaskiyar abin da ke faruwa tsakanin 'ya'yan riko da iyayen gidan nasu? Shirin Daga Laraba na wannan mako ya yi nitso cikin wannan tsohuwar matsala, ya bankado gaskiyar abin da ya ke faruwa.

Jul 26, 202329 min

"Dole Ne Mace Ta Yiwa Mijinta Wanki"

Muhawarar ya kamata ko bai kamata mace ta riƙa yiwa mijin ta wanki ba, ya sa ana ta tada jijiyoyin wuya tsakanin maza da mata. Wasu na ganin daya daga cikin ayyukan mace shine wanke kayan mijinta da dai sauran aikace-aikacen gida domin ƙara danƙon soyayya da zamantakewa. To amma nauyin hakan ya rataya a wuyan namiji ne ko mace? Shirin Daga Laraba na Yau, ya yi nazari akan ko ya kamata mata su riƙa yiwa mazajen su wanki a matsayin wajibi ko kuma kyautatawa....

Jul 19, 202329 min

Da Gaske Ana Iya Canza Injin Janareta Ya Koma Amfani Da Gas?

Tsadar man fetur a Najeriya ya tilastawa jama’a masu injin Janareta a gida da wuraren kasuwanci sauya masa tsari ya koma amfani da Gas na girki. Wannan dai wata fasaha ce da wasu mutane suka ƙirƙira bayan sun yi nazari a kai. A cikin shirin Daga Laraba na wannan mako, mun duba alfanu ko akasin hakan da za a iya samu gameda wannan sabon salo da aka ƙirƙira.

Jul 12, 202329 min

Yadda 'Yan Najeriya Suke Shiga Tasku a Kasashen Waje

Daga cikin ‘yan Najeriya musamman matasa akwai da dama da ke da burin guduwa daga Najeriya zuwa kasashen Turai ko na Larabawa, ido rufe. Ko masu irin wadannan burika sun san abubbuwan da ke tattare da zama a kasar da ba taka ba? A wannan karon, mun dubi yadda matasa ke hankoron tafiya wadansu kasashe neman arziki ido rufe. Mun ji dalilansu, mun kuma ji ta bakin wadanda suka samu tsallakawa, sannan mun tuntubi ta bakin masana kan alfanu da kuma hadurran da ke tattare da irin wannan tafiya....

Jul 05, 202328 min

Dalilan Lalacewar Al'adun Sallah

A yayin da ake bikin babbar Sallah a Najeriya da sauran ƙasashen Musulmin duniya, shirin Daga Laraba na wannan mako ya dubi yadda al'adun bikin sallah suka canza zuwa wani abu na daban. Mene ne dalilan da al'adun bikin sallah suka lalace a kasar Hausa? Saurari bayanai daga bakin dattawa, masana, da kuma matasa kan wannan maudu'i na lalacewar al'adun bikin sallah.

Jun 28, 202330 min

Martanin 'Yan Najeriya Kan Bashin Kudin Karatu

Batun bada rancen kudin karatu ga daliban jami'o'i na matakin digiri a Najeriya na ci gaba da daukar hankalin 'yan ƙasar. Wace fahimta 'yan Najeriya su ka yi wa wannan batu na bashin kudin karatu ga dalibai masu neman digiri? Saurari shirin Daga Laraba na wannan lokaci domin jin martanin 'yan Najeriya kan wannan batu da kuma matsayin kungiyar ASUU.

Jun 21, 202330 min

Yadda Kungiyoyi Ke Neman Hana Zaman Aure

Kungiyoyin bada agaji masu zaman kansu na kasashen yammacin duniya da aka fi sani da NGO na neman hana mata zaman aure a Jihar Borno, Arewa maso Gabashin Najeriya. Ko ta wadanne hanyoyi wadannan kungiyoyi na NGO ke shiga sha'anin zamantakewar aure? Saurari shirin Daga Laraba domin jin inda gizo ke saka.

Jun 14, 202330 min

Yadda Cire Tallafin Mai Ya Shafi Rayuwar 'Yan Najeriya

Tun ranar 29 ga watan Mayun 2023 da aka rantsar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban Najeriya ya bayyana cewa babu tallafin mai a cikin kasafin kudin da ya gada da zai kama aiki daga 1 ga Yunin da muke ciki, saboda haka batun tallafin mai ya tafi ke nan. Ko ta wadanne bangarori cire tallafin mai ya shafi rayuwar 'yan kasar? Shirin Daga Laraba na wannan lokaci na tafe da gamsassun bayanai daga bakin wadan da cire tallafin mai ya shafi rayuwarsu kai tsaye, da kuma bayanan masana kan wannan bat...

Jun 07, 202330 min

Abin Da 'Yan Arewa Ke Son Tinubu Ya Yi Musu

Litinin 29 ga watan Mayun 2023 aka rantsar da sabuwar gwamnati a Najeriya bayan sabon shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya lashe zaben da aka yi ranar 25 ga Fabrairun wannan shekara. Shin wadanne abubuwa al'ummar Arewacin Najeriya ke fata sabon shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi musu? Shirin Daga Laraba na wannan mako ya tattauna da wadansu 'yan Arewacin Najeriya daga Jihohi 7. Ga yadda tattaunawar ta kasance. A yi sauraro lafiya.

May 31, 202330 min

Yadda Rashin Sanin kimar Waliyyai Ke Shafar Zamantakewar Aure

Matsalar rashin zaman lafiya da tausayin juna a tsakanin ma'aurata a wannan zamani daya ne daga cikin matsalolin da ke ciwa mutane da dama tuwo a kwarya, lura da cewa, wadannan matsaloli na zama sanadiyyar mace-macen aure. Shin ko kun san baya ga matsalolin da ke samo asali daga ma'aurata da abokan huldar su akwai sako-sako da walittaka a cikin musabbaban tabarbarewar zamantakewar ma’aurata da lalacewar aure a wannan zamani? Binciken Shirin Daga Laraba na wannan mako ya gano sako-sako da walitta...

May 24, 202330 min

Yadda Hausawa Ke Shiga Kungiyoyin Asiri A Kudu

A da, ba a san ‘ya’yan Hausawa da shiga kungiyar asiri ba, sai dai wasanni irin su dambe da farauta da kokawa da sauransu. Mene ne ya canza yanzu aka fara samun ‘ya’yan Hausawa a kungiyoyin asiri? Shirin Daga Laraba na wannan Mako ya dubi yadda ‘ya’yan Hausawa suka fadawa kungiyoyin asiri a kudancin Najeriya.

May 17, 202330 min

Zama Da Uwar Miji A Gida Daya: Inda Gizo Ke Saka

Rigingimu tsakanin ma'aurata dake samo asali daga zama wuri daya da iyayen miji musamman uwa na daya daga cikin matsalolin da ake fama da su a Arewacin Najeriya da ma duniya baki daya. Tarihi ya nuna, an yi zamanin da iyaye da 'ya'ya ke zama wuri guda lafiya, mene ne ya canza da a wannan zamanin ba a iya zama wuri guda da iyaye kuma a zauna lafiya? Shirin Daga Laraba ya tattauna da wadanda abin ya shafa, ya ji ta iyayen, ya ji ta 'ya'yan, ya kuma nemi shawarwarin masana kan mafita....

May 10, 202330 min

Yadda Iyaye Ke Kashe Wa 'Ya'yansu Aure A Arewa

Mutuwar aure daya ce daga cikin matsalolin da ke ci wa mutanen Najeriya musamman 'yan Arewacin kasar tuwo a kwarya. Ko kun san wadansu iyayen ne da kansu suke janyo mutuwar auren 'ya'yansu? Shirin Daga laraba na tafe da karin bayani, ciki harda wanda aka kashewa aure. A yi sauraro lafiya.

May 03, 202330 min

Amfanin Kishiya A Zamantakewar Aure

Musulunci ya halatta auren mace fiye da daya ga mazan da ke da hali kuma wadanda za su iya yin adalci, amma kuma a rayuwarmu ta yau babu abin da ke ganin adawa da shan kushe kamar karin aure, Shin mene ne amfani kishiya? Wannan karo shirin Daga Laraba ya yi kokarin gano muhimmancin kishiya da kuma amfaninta.

Apr 26, 202330 min

Yadda Mutane Ke Zubar Da Ladan Azuminsu Kafin Sallah

Malamai na karfafa wa mabiya addinin Islama guiwa a watan Azumin Ramadana wurin tsayuwar daka wurin Ibada, amma wani abin mamaki shine yadda a karshen watan azumin mutane ke shagalta har su kai ga haramun wurin bikin Sallah. Shin kun san labarin masu tara kudi domin shirya bikin tarbar shaidan? Shirin Daga Laraba na wannan karon ya dubi hanyoyin da maza da mata ke bi wurin zubar da ladan ayyukan da su ka yi a cikin watan Azumin Ramadana.

Apr 19, 202330 min

Yadda Rashin Ruwan Sha Ke Lakume Rayuka A Kano

Jihar Kano na daya daga cikin jihohin da suka ci gaba a fannoni da yawa na rayuwa. Sai dai wani bincike da muka gudanar ya bankado yadda ake shan wahalar ruwa a wasu yankunan wannan jiha. Mene ne ya sa har yanzu ake tsananin wahalar ruwa a Jihar Kano? A saurari shirin DAGA LARABA na wannan mako a ji yadda ya bankado bakar wahalar da mutane ke sha sakamakon rashin ruwa a wasu yankunan Jihar Kano.

Apr 12, 202326 min

Hukuncin Saka Hotunan Sadaka A Soshiyal Midiya

A watan azumin Ramadan an kwadaitar da Musulmai falalar yawaita sadaka da kyauta domin neman yardar Allah. Shin mene ne hukuncin masu daukar hotunan sadaka da kyautar da suka bayar su saka a kafafen sada zumunta na zamani wato oshiyal midiya? Shirin Daga Laraba na wannan lokaci na tafe da bayanan hujjojin masu saka wadannan hotuna da kuma matsayin Malaman addinin Musulunci a kan wannan dabi’a.

Apr 05, 202330 min

Dalilin Da 'Yan Siyasa Ke Kin Karbar Kaye A Najeriya

A tsarin zabe dole a samu wanda ya ci, a kuma samu wanda ya fadi. Amma wannan ka'ida har yanzu ba ta samu wurin zama a fagen siyasar Najeriya ba, don kuwa duk wanda ya fadi baya yarda ya fadi sai ka ji suna kiran "Magudi aka yi, amma ni na ci zabe". Mene ne dalilin da 'yan siyasar Najeriya ke kin karbar kaddarar faduwa? Saurari shirin Daga Laraba domin jin dalilin 'yan siyasa na kirkirar wannan dabi'a ta kin karbar kaye a matsayin kaddara da ke shafawa Najeriya bakin fenti a idanun duniya....

Mar 29, 202330 min
Hosted on Buzzsprout
For the best experience, listen in Metacast app for iOS or Android