Ana sa ran a tashi da Azumin watan Ramadan mai albarka ranar Alhamis idan Allah ya yarda. Shin kun san matakan samun nasara a cikin ibadar wannan wata? Shirin Daga Laraba na wannan karo ya tattaro bayanai da shawarwari na alheri game da yadda za a rabauta da alheran da ke cikin watan azumin Ramadan.
Mar 22, 2023•30 min
Shirin Daga Laraba na wannan mako ya leka banki da kasuwa kuma ya gano yadda jama’a ke fama da rashin kudi, ga shi kuma wasu ’yan kasuwa sam ba sa karbar tsohuwar Naira, sai sabuwa ko taransfa. Ko yaushe za’a sakar wa ’yan Najeriya Naira? Saurari Daga Laraba domin jin amsar wannan tambaya, dama wadansu masu alaka. Za ku so karanta wadannan
Mar 15, 2023•30 min
Shirin Daga Laraba na wannan karo ya yi wasu tambayoyi masu kalubale ga shugaban kasar Najeriya mai jiran gado game da lafiyarsa, da kuma kaifin basirarsa. Shin Bola Ahmed Tinubu zai iya tafiyar da harkokin mulkin Najeriya fiye da Muhamadu Buhari? Ku surari shirin Daga Laraba na wannan mako ku ji amsoshin duka tambayoyin namu.
Mar 08, 2023•29 min
Ku biyo shirin Daga Laraba na wannan karo ku ji yadda sakamakon zaben shugaban kasa da ’yan majalisun tarayya na shekarar 2023 ya zo da sabon salon da watakila ba a taba ganin irinsa a wannan zamanin ba. A cikin shirin, za ku ji yadda gwamnoni masu ci suka sha kasa a yunkurinsu na zuwa Majalisar Dattawa.
Mar 01, 2023•31 min
Ranar Asabar 25 ga Watan Fabrairun da muke ciki ne ake sa ran gudanar da zaben shugaban kasa da ’yan majalisun tarayyar Najeriya. Shin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta shirya gudanar da wannan gagarumin aiki? Shirin Daga Laraba ya leka lungu da sako a Najeriya domin sanin matakin shirin hukumar zaben da kai.
Feb 22, 2023•30 min
Nan da kwana tara ’yan Najeriya za su zabi sabon shugaban da zai mulke su na tsawon shekaru hudu idan Allah ya yarda. Bisa la’akari da yadda yakin neman zabe ke gudana, wane ne cikin ’yan takarar ke da alamun nasara a zaben na mako mai zuwa? Shirin Daga Laraba ya tattauna da kwamitin yakin neman zaben manyan ’yan takarar da ake sa ran daya daga cikinsu zai zamaz zababben shugaban kasar Najeriya, inda kowannensu ya bayyana yadda yake kallon nasara da kuma kalubalen da ke gabansu. A yi sauraro laf...
Feb 15, 2023•31 min
Sabuwar dabi’ar neman miji ta kafofin sada zumunta da ’yan mata ke yi na neman zama ruwan dare. Bisa al’adar bahaushe dai, namiji ne ke ganin mace ya ce yana so; To amma sai ga shi ’yan mata sun dukufa tallata kansu ga mai so a kafofin sada zumunta. Shin me ke faruw ne? Shirin Daga Laraba ya tattauna da wasu ’yan mata kan abin da ke sa su dora hotunansu a kafofin sada zumunta don neman miji; mun kuma ji ta bakin samari kan yadda suke kallon matan da ke yin hakan....
Feb 08, 2023•30 min
A farko babu wanda ke yarda yana dan taba karya lokaci bayan lokaci. Amma idan aka dan matsa da bincike sai a samu jama’a da dama na dan tabawa. Ko mene ne ya sa mutane ke yin karya? Shirin Daga Laraba ya tattauna da wadansu da suka yarda suna yin karya, sun fadi dalilansu, mun kuma ji ta bakin masana kan dalilin yin karya da kuma hukuncinta.
Feb 01, 2023•30 min
Matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa ta tilasta wa 'yan Najeriya sauya yadda suke rayuwa. Shin kun san irin halin da jama'a ke ciki, kawo yanzu? Shirin Daga Laraba ya binciko hakikanin halin da ake ciki, ya kuma tuntubi dalilai.
Jan 25, 2023•30 min
Batun alaka tsakanin ’yan aiki da iyayen gidansu ya jima yana daukar hankali a fagen musayar ra'ayi. Shin tsakanin ’yan aikin da masu daukarsu, wa ke da alhakin abin da ke faruwa? Shirin Daga Laraba ya kutsa lungu da sako, ya zakulo ’yan aiki ya kuma ji ta bakin masu daukar aikin.
Jan 18, 2023•27 min
Muhawara kan abin da ke sa maza tsoron matan da suka yi karatun boko mai zurfi ko masu dukiya, batu ne da ya jima yana daukar hankalin jama’a da dama. Shin ko matan da suka yi karatun boko mai zurfi sun san dalilan da maza ke tsoronsu? Shirin Daga Laraba ya binciko wadan nan dalilai, ya kuma baje su a gadon fida, inda masana suka fede biri har wutsiya.
Jan 10, 2023•30 min
A kwankin baya mun kawo muku shiri na musamman akan yadda ake aure da ciki a wannan zamani. Wannan karon, shirin ya dubi yadda yaudara ta zamo ruwan dare a tsakanin masu shirin aure. Shin kunsan yadda yaudara ta zamo rigar ado a wannan zamani? Shirin Daga Laraba na tafe da bayanai masu ratsa zuciya, da kuma mafita kan yaudara a fagen soyayya.
Jan 04, 2023•30 min
Zumunci wani jigo ne a tsarin rayuwar malam Bahaushe a shekarun baya, amma yanzu yana neman zama tarihi. Shin yaya aka yi yanzu zumunci ke neman zama labari a tsakanin al’umma? Shirin Daga Laraba na kunshe da bayanai. A yi sauraro lafiya.
Dec 28, 2022•30 min
Shin idan ka gano cewa da cikin wani amaryarka ta shigo gidanka wane mataki za ka dauka? Shirin Daga Laraba na wannan mako ya bankado al’ada yin aure da juna biyu a Arewacin Najeriya. Shin da sanin angwaye ake daura musu aure da mata masu ciki? Gyara zama domin jin yadda ta kaya tsakanin wadansu angwaye da amarensu suka zo musu da cikin wasu.
Dec 21, 2022•29 min
Matsalar yawon talla ta dade tana ci wa al’ummar Arewacin Najeriya tuwo a kwarya. Me ya sa aka fi dora wa ’yan mata talla ta kasar Hausa kuma tsakanin amfani da illolin talla wanne ne a gaba? Shirin Daga Laraba ya dubi maganar talla da idon basira, don neman mafita ta hanyar tattaunawa da hukumomi da masana a fannin ilimin addini da na duniya .
Dec 14, 2022•31 min
Shin me ya sa kayayyaki marasa inganci suka zama ruwan dare a Najeriya? Wani lokacin kayayyaki na jabu ko lalatattu da ake sarrafawa ko sayar wa ’yan Najeriya na hallaka da dama a cikinsu. Me hukumar da ke kula da ingancin kayayyaki ke yi don hana kawo wa ’yan Najeriya kayayyaki marasa inganci? Saurari shirin Daga Laraba na wannan lokaci domin jin wainar da ake toyawa.
Dec 07, 2022•31 min
Zubar da ciki al'amari ne mai ba da tsoro saboda hadarinsa da kuma alhakin da ake iya dauka idan an yi ba bisa ka’ida ba. Shin ko mene ne dalilin da zubar da ciki ya zama ruwan dare a tsakani ’yan mata da matan aure a Najeriya? Saurari cikakken shirin Daga Laraba na wannan lokaci domin jin yadda matan aure da ’yan mata suka maida zubar da ciki abin wasa.
Nov 30, 2022•30 min
Shirin Daga Laraba na wannan mako ya mayar da hankali ne a kan maganin karfin maza, amfaninsa, illolinsa da kuma shawarwarin masana a kai. Wannan kari ne a kan shiri na musamman da muka kawo muku a baya kan maganin mata, wanad aka fi sani da kayan mata da yadda ya samu karbuwa a tsakanin mata musamman a Arewacin Najeriya.
Nov 23, 2022•30 min
Shirin Daga Laraba na wannan lokaci ya dubi yadda matsalar lalata tsakanin iyaye da ’ya’yansu ko tsakanin yayyu da kanne ta zama ruwan dare ne. Mun tattaro bayanai masu nuna yadda kwamacalar take kara kamari a wannan zamani.
Nov 16, 2022•30 min
Me ya sa ake yawan samun mutane masu manyan shekaru da ke afka wa kananan yara mata ko mazayarinya ko karamin yaro? Shin wane dalili ke sa kawo yawaitar wannan kazamar dabi’a ta lalata da kananan yara? Shirin Daga Laraba ya dubi yadda wannan matsala ta zama ruwan dare, musamman a Arewacin Najeriya. A yi sauraro lafiya.
Nov 09, 2022•30 min
Duk lokacin da aka ambaci zafin kishi, to da dama mata ke zuwa zukatan jama’a. Shin yaya maza ke kishi, kuma me suke iya aikatawa saboda tsananin kishi? Shirin Daga Laraba na wannan mako ya tattauna da masu ruwa da tsaki game da tsananin kishin maza, abin da yake iya sa su da kuma yadda ya kamata a yi kishin.
Nov 02, 2022•30 min
Ana samun korafe-korafe game da yaduwar zinace-zinace tsakanin ma’aurata a Najeriya? Shin me ya faru ma’aurata suka tsunduma ka’in-da-na’in a harkar alfashar da a baya an fi dangantawa da marasa aure marasa kamun kai? Shirin Daga Laraba na wannan mako ya tsananta bincike da tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan wannan batu domin gano inda gizo ke saka, domin fid-da jaki daga duma.
Oct 26, 2022•31 min
Taimakon juna na daya daga cikin hallayyar da ake kwatanta mutane masu nagarta da shi, amma a yanzu abin yana neman zama tarihi. Shin me ya sa taimakon juna ya yi karanci a wannan zamanin? Saurari labarin wadansu da aka zalunta a gaban jama’a amma ba a kawo musu dauki ba. Mun kuma tattauna da masana kan yadda aka tsinci kai a halin rayuwar ba ruwan kowa da kowa.
Oct 19, 2022•30 min
Shirin Daga Laraba na wannan mako ya tattauna da Farfesa Mahmood Yakubu, Shugaban Hukumar INEC, kan zaben 2023 da ke tafe. Shin kana bukatar sanin inda INEC ta kwana kan shirye-shiryen zaben 2023? Saurari shiirn Daga Laraba na wannan lokaci.
Oct 12, 2022•30 min
Wata kididdiga da jaridar Vanguard ta fitar a 2017 ta bayyana cewa akwai kabilu da ke amfani da harsuna 371 a fadin Najeriya. Ta yaya wadannan kabilu za su fahimci junansu su zauna lafiya har su amfani kansu da kasarsu? Saurari cikakken shirin Daga Laraba domin jin yadda masana da ’yan Najeriya suka bayyana hanyoyin da za a bi wurin cudar guna da man jikinta.
Oct 05, 2022•29 min
Zargin sakaci da rayukan marasa lafiya, musamman mata masu ciki a Asibitin Kwararru na Murtala da ke Kano ya karade kafafen sadarwa a ’yan kwanakin nan. Ana zargin yadda ma’aikatan asibitin ke nuna halin ko-in-kula da rayukan jama’a na sanadiyyar mutuwar mata da jarirari kusan kowace rana. Shin me ya sa asibitin Murtala ya yi kaurin suna haka a wurin jama’a? Shirin Daga Laraba ya tattauna masu korafi kan asibitin da kuma masu fafutukan kawo gyara....
Sep 28, 2022•30 min
Samari na daga cikin mutanen da ba a cika damuwa a san abin da ke ci musu tuwo a kwarya ba. Amma shin kun san irin mawuyacin halin da matasa maza ke ciki kuwa? Akan dauka cewa halin da suke ciki ba abin damuwa ba ne, kuma bai dace su nuna gazawarsu ba, ballantana har su saki jiki su nema ko a ba su shawara kan matsalolin da ke addabar rayuwarsu. Shirin Daga Laraba na wannan mako ya yi nazari mai zurfi dangane da halin da samarin ke ciki, kuma suke boyewa. A yi sauraro lafiya....
Sep 21, 2022•30 min
Cigaban da aka samu a bagaren sadarwar zamani ta sa abubbuwan da ake yi a zahiri yanzu an koma yin da yawa daga cikinsu ta kafafen sadarwa, ciki harda cinikayya da kuma shawarwari kan zamantakewar rayuwa da na auratayya. Shin wadanda ke da irin wadannan shafukan kwararru ne kuwa, wace irin nasara a ke samu in an dauki shawarar, ko kuma dai barna a ke yi mai-makon gyara? Shirin Daga Laraba na wannan mako ya yi nazarin irin wadannan shafuka da irin tasirin da su ke yi wurin inganta ko lalata zaman...
Sep 14, 2022•30 min
Dan Adam na rayuwa da cin abinci da shan abin sha daidai bukatar jikin. Shin wane abinci ne jikin dan Adam ya fi bukata, kuma a wane lokaci? Lura da yadda cututtuka sanadiyyar abinci ke kara yawaita, shirin Daga Laraba na wannan mako ya dubi batun abinci da ababe shan da ake mu'amala da su yau da kullum, domin neman mafita kan yadda za a gujewa kamuwa da cutuka sanadiyyar abinci
Sep 07, 2022•30 min
Yawaitar ta'addancin 'yan bindiga a Najeriya ya sa 'yan kasar sauya tunaninsu da yadda suke rayuwa. Shin sauya tunani da yadda ake rayuwa a Najeriya domin tsoron ta'adancin 'yan bindiga mafita ce kuwa? Shirin Daga Laraba na wannan makon ya dubi yadda kasashen da suka ci gaba ke yakar ta'addanci da yadda 'yan kasar ke magance matsalolin ta hanyar kin sauya yadda suke tunani da mu'amala.
Aug 31, 2022•30 min