Lafiya Jari ce - podcast cover

Lafiya Jari ce

RFI Hausawww.rfi.fr

Shirin Lafiya Jari ce na tattaunawa da likitoci da mahukunta a game da kiyon lafiyar jama’a, sanin sabbin magunguna da binciken kimiya ya samar. Ana gabatar da shirin a ranar Littinin da hantsi, tare da maimaici a ranar Jumma'a da safe.

Episodes

Sharhi kan ƙiba fiye da ƙima da ke baraza ga matasan Afirka

Shirin 'Lafiya Jari Ce na wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan hasashen da wata ƙungiya ta yi cewar nan da shekarar 2025 raɓin al'ummar Afirka masamman matasa za su fuskanci cutar ƙibar da ta wuce ƙima ko Obesity a turance.

May 26, 202510 min

Ƙaruwa masu kamuwa da cutar tarin fuka a sassan Jamhuriyar Nijar

Shirin namu na wannan makon zai mayar da hankali ne kan ƙaruwar mutanen da ke kamauwa da cutar babban tari, ko kuma tarin fuka, ko kuma TB a sassan Jamhuriyar Nijar, lamarin da ke zuwa a lokacin da ake fuskantar ƙarancin agajin magangunan yaƙi da wannan cuta. Wanmnan cuta na sahun daɗaɗɗun cutuka masu yaɗuwa, waɗanda wani kan iya goga wa wani.Abin da ya sa ya zama wajibi a rika wayar da kan al'umma akan hanyoyin kariya daga ita.

May 19, 202510 min

Yadda aka sake samun ɓullar cutar Polio a Najeriya

Shirin Lafiya jari ce a wannan makon ya yi duba na musamman game da dawowar cutar Polio a Najeriya, cutar da alamu ke nuna nasarar yaƙarta ke yiwa ƙasar kwan gaba kwan baya, lura da yadda a lokuta da dama ake sake ganin ɓullarta bayan nasarar kawar da ita, kodayake ƙwararru sun ce wadda ta ɓulla a wannan karon ba wadda aka saba gani ba ce kuma bata kai waɗanda suka gabace ta illa ba. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu...............

May 12, 202510 min

Annobar ƙyanda ta tilastawa mahukunta Nijar yin rigakafin ƙasa baki ɗaya

Shirin Lafiya Jari ce na wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan shaushawar ƙyandar da mahukuntan Jamhuriyar Nijar suka jagoranta sakamakon ɓullar cutar wadda a duk lokacin da aka ga bazuwarta ta ke yiwa ƙananan yara illa matuƙa. Dai dai lokacin da duniya ta gudanar bikin makon rigakafi a ƙarshen watan Mayun da ya gabata, a Jamhuriyyar Nijar annobar ƙyanda ce ke ci gaba da yaɗuwa tare da galabaitar da ɗimbin ƙananan yara, lamarin da ya tilasta mahukunta ɗaukar matakan yiw...

May 05, 202510 min

Yadda cuɗanya wajen amfani da moɗa ko cokali ke taimakawa wajen yaɗa cutuka

Shirin Lafiya Jari ce na wannan makon, ya mayar da hankali ne kan nau’ikan cutukan da ke bazuwa sakamakon cuɗanyar da jama’a ke yi wajen amfani da kayayyakin da bisa ƙa’ida yakamata kowanne mutum ya yi amfani da nasa shi kaɗai. Har yanzu ana samun waɗanda ke yin gamayya wajen amfani da moɗar-shan ruwa ko cokali ko kuma kwanon cin abinci dama sauran kayakin da basu cancanci amfanin gamayya ba, lura da yadda cikin sauƙi hakan ke iya yaɗa cutuka. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin t...

Apr 28, 202510 min

Matakan da ya kamata a ɗauka yayin kai ɗaukin gaggawa a lokacin faruwar haɗari

Shirin Lafiya Jari ce a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan matakan da ya kamata mutane su riƙa ɗauka gabanin kai ɗaukin gaggawa a lokacin afkuwar haɗari ko ibtila'i, waɗanda rashinsu a wasu lokutan ke kaiwa ga asarar rayuka ko kuma haddasa gagarumar illa ga mutanen da haɗarin ya rutsa da su. Shirin ya shawarci jama'a game da samun ilimin iya kai ɗaukin gaggawa don kaucewa haddasa matsala ba tare da sani ba ga mutanen da ake ƙoƙarin ceton rayuwarsu. Ku latsa alamar sa...

Apr 21, 202510 min

Ana samun ƙaruwar masu kamuwa da cuta mai karya garkuwar jiki a Ghana

Shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan ƙaruwar masu kamuwa da cuta mai karya garkuwar jiki ko kuma HIV AIDS ko sida tsakanin matasan Ghana a shekarun baya-bayan nan, wadda masana ke ɗora alhakin yawaitarta kan rashin ɗaukar matakai. Wannan ƙaruwar alƙaluma na zuwa a dai dai lokacin da duniya ke ganin ƙarancin magunguna rage kaifin cutar sakamakon matakin Amurka na zaftare tallafin da ta ke bayarwa ƙarƙashin ƙungiyar USAID. Ku latsa alamar sauti don sauraron cika...

Apr 14, 202510 min

Mutane na ɓoye cutukan ƙwaƙwalwa saboda fargabar alaƙantasu da hauka

Shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan makon ya yi duba na musamman kan cutuka ko kuma lalurar ƙwaƙwalwa, dama rabe-rabenta baya ga nazarin yadda mutane ke ɓoye irin wannan lalura saboda kunyar kar a alaƙanta su da ciwon hauka. Alƙaluman hukumar lafiya ta duniya WHO a shekarar 2017 sun nuna cewa kashi 19 na yawan al’ummar duniya na fama da matsalar ƙwaƙwalwa walau a babban mataki ko kuma a mataki na ƙasa, matsalar da kuma bayanan hukumar ke cewa yafi tsananta a ƙasashe masu ta...

Mar 24, 202511 min

An samu ɓullar cutar sankarau a wasu jihohin arewacin Najeriya

Shirin 'Lafiya Jari Ce' na wannan makon ya mayar da hankali ne akan cutar sankarau, wanda ke yin ƙamari a cikin yanayi na zafi da ake ciki, musamma a ƙasashenmu na nahiyar Afrika. Tuni aka samu ɓullar cutar sankarau a sassa daban-daban na Najeriya inda ta kashe gomman mutane a jihohin Kebbi da Sokoto, wadda aka bayyana ta da annoba. Masana a ɓangarorin lafiya da kuma yanayi, na ci gaba da gargaɗi kan yiwuwar ɓullar tarin cutuka sakamakon tsananin zafin da ake fuskanta a wasu daga cikin jihohin N...

Mar 17, 202510 min

Ƙarancin magungunan kuturta da abubuwan da ke haddasa cutar

A wannan makon shirin na lafiya jari ce ya mayar da hankali kan cutar kuturta ko kuma Lebrosy ko albaras, cutar da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ke ganin sam bai kamata a samu ɓirɓishinta a banƙasa ba. Rayuwar masu wannan lalura ta kuturta rayuwa ce mai cike da ban tausai, musamman waɗanda ke killace a asibitin na Bela wanda Turawan mishan daga Netherlands suka samar tun a shekarar 1928 wato tun gomman shekaru kafin ƴancin Najeriya. Alƙaluma sun nuna cewa, duk shekara Najeriya na ganin fiye da mu...

Mar 10, 202510 min

Rashin kulawa ta sanya wasu asibitoci a jihar Kano komawa Kufai

Shirin ''Lafiya Jari Ce'' tare da Azima Bashir Aminu a wannan makon, ya kai ziyara wasu asibitocin yankunan karkara a arewacin Najeriya, inda sashen Hausa na RFI ya ganewa idonsa tarin matsalolin da suka dabaibaye irin waɗannan asibitoci da bisa al’ada ke matsayin masu kula da lafiya a matakin farko. Tarin asibitocin yankunan karkarar jihar Kano na fama da matsaloli kama daga rashin malaman jinya da kuma rashin wadatattun kayakin aiki, koma rashin ginin Asibitin ɗungurugum, ta yadda da dama daga...

Mar 03, 202510 min

Tiyatar fitar da jarirai daga cikin Uwa na yawaita a sassan Najeriya

Shirin Lafiya jari ce a wannan mako tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan yadda fasahar cire ɗa ta hanyar CS ke taimakawa wajen ceto rayukan uwa da ɗa da nufin rage asarar rayukan da ake fuskanta a lokacin haihuwa. Duk da cewa haihuwa 3 cikin 100 ce kaɗai ake yi ta hanyar tiyata ko kuma CS a Najeriya bisa alƙaluman 2019, amma a baya-bayan nan ana ganin yawaitar matan da ake yiwa CS gabanin haihuwa kama daga nau'in matan da basa zuwa asibiti da kuma mata masu shekaru da yawa ko waɗan...

Feb 24, 202510 min

Mahukuntan Najeriya sun tsawaita shekarun aiki ga likitoci da jami'an lafiya

Shirin ''Lafiya Jari Ce'' tare da Azima Bashir Aminu a wannan mako ya yi duba ne kan matakin gwamnatin Najeriya na tsawaita lokacin ritayar likitoci da malaman jinya a wani yunƙuri na ganin sun ci gaba da bayar da gudunmawa ga al’ummar wannan ƙasa wadda ke fama da ƙarancin ƙwararrun likitoci. Matakin na gwamnatin Najeriya ya nuna cewa Likitocin ko kuma sauran jami’an lafiya na da zaɓin ƙarin shekaru 5 akan ainahin shekarunsu na ritaya, ta yadda za su kai har shekaru 65 na haihuwa a bakin aiki ma...

Feb 17, 202510 min

Lafiya Jari Ce: Illar rashin zuwa awon ciki ga lafiyar mata da jariransu

Shirin ''Lafiya Jari ce'' tare da Azima Bashir Aminu a wannan mako ya yi duba ne kan matsalar rashin zuwa awo da ke matsayin babban ƙalubalen ga mata masu juna biyu a yayin goyon ciki ko kuma haihuwa, matsalar da aka fi ganin ta’azzararta a yankunan karkara, wadda a lokuta da dama ke kaiwa ga asarar rayukan walau uwa ko jariri. Ƙorafe-ƙorafen jami’an lafiya na ci gaba da yawaita kan matsalolin da suka dabaibaye tsarin renon ciki da kuma haihuwa a yankunan karkara, matsalar da wala’alla ake ganin...

Feb 10, 202510 min

Barazanar da fannin lafiya ke fuskanta kan ficewar likitoci daga Najeriya

Shirin lafiya Jari ce na wannan makon ya taɓo batun yadda kwararrun likitoci ke tserewa daga Najeriya, inda wasu alkaluma suka nuna cewa a cikin shekaru biyar da suka gabata, sama da likitoci dubu 16 suka fice daga ƙasar don yin aiki a wasu ƙasashen ketare, lamarin da ke barazana ga tsarin kula da lafiya a ƙasar. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir Aminu............

Jan 27, 202510 min

Ƙoƙarin da ƙungiyoyi ke yi don magance cutar yanar ido tsakanin al'ummar Nijar

Shirin Lafiya jari ce bisa al'ada tare da Azima Bashir Aminu na yin duba ne kan wasu batutuwa da suka shafi kiwon lafiya, kuma a wannan makon ya yada zango a Jamhuriyyar Nijar inda wasu ƙungiyoyin agaji suka yiwa tarin mutanen da ke fama da matsalar cutar yanar ido aiki a ƙokarin dawo musu da ganinsu. A cikin shirin za ku ji yadda kusan kashi 2 cikin 100 na al'ummar wannan ƙasa ta yankin Sahel ke fama da matsalar lalurar ta yanar ido a wani yanayi da mahukunta tare da taimakon ƙungiyoyin ƙasa da...

Jan 20, 202510 min

Tsarin tazarar Iyali ya fara samun karɓuwa a yankunan karkara

Shirin lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu bisa al’ada kan taɓo batutuwan da suka shafi kiwon lafiya ko kuma a lokuta da dama ya lalubo ƙalubalen da fannin lafiyar ke fuskanta don ankarar da mahukunta da nufin ɗaukar matakan gyara. A wannan makon shirin na Lafiya Jari ce ya mayar da hankali kan tazara ko kuma tsarin iyali ko Family Planning wanda ke sahun shawarwarin kiwon lafiya da ke ganin kakkausar suka musamman a arewacin Najeriya wala’alla saboda yadda tsarin ya ci karo da al’adun al’...

Jan 06, 202510 min

Cutar sanƙarau ta fara fantsamuwa a sassan jihar Maradi ta Nijar

A wannan makon shirin na lafiya jari ce tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan yadda aka samu ɓarkewar cutar sankarau a wata Makaranta da ke jihar Maradin Jamhuriyar Nijar, cutar da tuni ta harbi tarin ɗalibai, a wani yanayi da masana ke gargaɗi kan haɗarin da ke tattare da wannan cuta musamman nau’in wadda ake ganin ɓullarta a lokacin sanyi. Kafin yanzu akan ga ɓullar cutar sanƙarau ne a lokaci na zafi sai dai a shekarun baya-bayan nan ana ganin yadda wannan cuta kan sauya salo tare...

Dec 30, 202410 min

Barazanar da hunturu ke yi ga keɓantattu ko kwantattun cutuka

Shirin lafiya jari ce na wannan mako ya mayar da hankali ne kan yadda lokacin sanyi ko kuma hunturu kan zo da wasu keɓantattu ko kuma tayar da wasu kwantattun cutuka. Nau’ikan cutukan da suke barazana ko kuma tashi a irin wannan lokaci na hunturu sun ƙunshi mura ko tari, ko ciwon hakori baya ga saɓar fata kana yawan fitsari ko cutuka masu alaƙa da zuciya yayinda cutuka irin sikila ko asma kan tashi duk dai a wannan lokaci. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Azima Bashir A...

Dec 23, 202410 min

Yadda ƙungiyar ALIMA ta Faransa ke taimakawa wajen yaƙi da cutar yunwa a Najeriya

Shirin lafiya jari ce a wannan makon ya mayar da hankali kan ta’azzarar cutar Tamowa ko kuma rashin sinadaran abinci mai gina jiki da ke addabar ƙananan yara a Najeriya, a wani yanayi da asusun UNICEF ke cewa duk yaro 1 cikin 3 na fama da matsalar ƙarancin abinci a ƙasar, wanda ke wakiltar kashi 37 cikin 100 na yawan yaran ƙasar ko kuma adadin yara miliyan 6. Duk da cewa tsawon lokaci wannan cuta ta ɗauka ta na addabar yara a Najeriyar, a wannan karon cutar ta tsananta a jihohin arewacin ƙasar w...

Dec 16, 202410 min

Irin kulawar da ya kamata iyaye su bai wa ƴaƴansu a yanayi na hunturu

Shirin lafiya jari ce a wannan makon ya yi duba ne kan cutukan da ke barazana a lokacin sanyi, baya ga shawarwari kan yadda iyaye za su kula da lafiyar yaransu a irin wannan lokaci, musamman ganin cewa yaran ne sanyi ya fi yiwa illa fiye da manya. Dai dai lokacin da iskar hunturu ta fara kaɗawa a sassan jamhuriyar Nijar, jihar Difffa na sahun jihohin da wannan matsala ke tsananta matuka ta yadda a kowacce shekara ake ganin tarin waɗanda sanyi kan yiwa lafiyarsu illa. Ku latsa alamar sauti don sa...

Dec 09, 202410 min

Adadin masu kamuwa Cancer zai ninka sau 10 a Najeriya- Masana

Shirin Lafiya Jari ce tare da Azima Bashir Aminu a wannan makon ya mayar da hankali kan yadda cutar Cancer ko kuma Daji ko Najeriya ke ta'azzara a Najeriya a wani yanayi da ake da ƙarancin wayar da kai kan cutar duk kuwa da illar da ta ke ci gaba da yiwa jama'a. Hankulan masana a ɓangaren kiwon lafiya ya tashi ne matuƙa bayan hasashen da ke nuna yiwuwar alƙaluman masu kamuwa da cutar duk shekara a Najeriyar da yawansu ya kai dubu 70 ya iya ruɓanyawa fiye da ninki 10 nan da shekaru ƙalilan masu z...

Dec 02, 202410 min

Matsalar mace-macen mata masu juna biyu ta sake ta'azzara a Nijar

Shirin Lafiya Jari ce a wannan makon tare da Azima Bashir Aminu ya mayar da hankali kan matsalar mace-macen mata masu juna biyu da jarirai walau a lokacin haihuwa ko kuma goyon ciki, matsalar da ke tsananin ta'azzara a Jamhuriyyar Nijar bayan da alƙaluma suka nuna yadda matsalar ke kwan-gaba-kwan-baya sakamakon dawowarta a baya-bayan nan bayan daƙileta a shekarun baya. Masana sun alaƙanta matsaloli masu alaƙa da rashin cin abinci mai gina jiki ko kuma rashin kulawar lafiya baya da rashin garkuwa...

Dec 02, 202410 min

Yadda ake samun ƙaruwar mace-macen kwab-ɗaya ko kuma mutuwar fuju’a

Shirin Lafiya Jari ce a wannan makon ya nazarci yawaitar mace-macen kwab-ɗaya ko kuma mutuwar fuju’a da ake ganin ta’azzararsu a wannan lokaci musamman a sassan Najeriya a wani yanayi da matsi ko kuma tsadar rayuwa ke ci gaba da galabaitar da jama’a. Dai dai lokacin da masana ke alaƙanta wannan matsala ta mutuwar far ɗaya da wasu kwantattun cutuka da yanayi kan tayar da su a lokaci guda, wani bincike baya-bayan nan ya danganta tsananin damuwa da yawaitar tunane-tunne halin rayuwa a matsayin ummu...

Nov 25, 202410 min
For the best experience, listen in Metacast app for iOS or Android
Open in Metacast