Yadda bukin wasanni na ƙasa ke gudana a Abeokutan Najeriya
Shirin 'Duniyar Wasanni' a wannan makon tare da Khamis Saleh yi yi dubi ne kan bikin wasannin na ƙasa da ke gudana a jihar Ogun da ke Najeriya.
A kowace Litinin da Juma'a a shirye-shiryen Safe da Dare ana gabatar da Shirin Duniyar Wasanni akan batutuwa daban-daban da suka shafi wasanni a sassan duniya.
Shirin 'Duniyar Wasanni' a wannan makon tare da Khamis Saleh yi yi dubi ne kan bikin wasannin na ƙasa da ke gudana a jihar Ogun da ke Najeriya.
A wannan makon shirin zai ɗora ne akan wanda muka kawo a baya, wanda ya yi bita a game da wasu shahararun ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na arewacin Najeriya da suka taimaka wajen ƙyanƙyasar fitattun ƴan wasa da suka yi shura a fagen ƙwallon ƙafa a ƙasar. Shirin ya yaɗa zango ne a Kano, inda ya gana da wasu tsaffin fitattun ƴan wasa, musamman na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Racca Rovers.
A wannan makon, shirin Duniyar Wasanni ya ɗora ne kan shirin mu daya gabata, wanda yayi duba kan yadda manyan ƙungiyoyin da suka taimakawa Najeriya wajen ƙyanƙyansar shahararrun ƴan wasa daga yankin Arewacin ƙasar suka durkushe. A wannan makon shirin zai yada zango ne a garin Jos na jihar Filato, wanda ke zama gida ga ƙungiyar Mighty Jets FC. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh..........
Shirin Duniyar Wasanni a wannan makon ya yi duba ne kan yadda manyan ƙungiyoyin da suka taimaka wa Najeriya wajen ƙyanƙyansar shahararrun ƴan wasa daga yankin Arewacin ƙasar suka durkushe. A baya yankin Arewacin Najeriya ne ke kan gaba wajen samar da manyan ƴan wasan da ake ji dasu a ƙasar, kuma mafi yawancin ƴan wasan sun fito ne daga ƙungiyoyi na cikin gida irinsu DIC Bees da ke Kaduna wacce ta koma Ranchers Bees da Racca Rovers da ke Kano da Mighty Jets da ke garin Jos da dai sauransu. Sai da...
Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon, ya yi duba ne kan wasan ƙarshe da aka yi na gasar Copa del Rey tsakanin Barcelona da Real Madrid, inda Barca ta samu nasarar lashe kofin karo na 32 a tarihi. Haka nan shirin ya duba nasarar lashe gasar Firimiyar Ingila da Liverpool ta yi a wannan kaka. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh.........
Shirin Duniyar Wasanni tare da Khamis Saleh a wannan makon ya mayar da hankali kan tasirin masu horarwa na cikin gida a ci gaban ƙwallon ƙafar nahiyar Afirka. A baya-bayan nan ƙasashen na nahiyar Afirka sun mayar da hankali wajen ɗaukar masu horarwa na cikin gida tun bayan rawar da Morocco ta taka a gasar cin kofin Duniya ta 2022 karon farko da aka ga irin hakan daga wata ƙasa a nahiyar ta Afrika. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.
A makon da ya gabata ne dai Hukumar Ƙwallonn Kafar Afirka CAF ta gudanar da zaɓenta, inda aka sake zabar Patrick Motsepe a matsayin shugaba a karo na biyu. Bayan haka ne aka gudanar da zaɓen wakilan nahiyar a Hukumar Ƙwalllon Ƙafa ta Duniya, FIFA, inda Afirka ke da wakilai 6, har da shugaban CAF mai kujerar kai-tsaye..
Shirin a wannan makon zai yi duba ne kan matsalar nan ta nuna wariyar launin fata da wasu ƴan wasa ke fuskanta. Nuna wariyar launin fata a wasannin motsa jiki musamman ma kwallon ƙafa na ɗaya daga cikin ƙalubalen da ƴan wasa baƙaƙe ke fuskanta, matsala da ta shafe shekaru aru-aru ana fama da ita. Wani lokaci ƴan wasa baƙar fata dai na fuskantar cin zarafin daga magoya baya ko masu horaswa, ta hanyar zagi kai tsaye ko wata alama ta nuna kaskanci ko kuma cin fuska, duk da cewa hukumomi na ɗaukar k...
Shirin ''Duniyar Wasanni'' tare da Khamis Saleh, a wannan makon ya mayar da hankali kan yadda Hukumar Kula da Kwallon Ƙafa ta Najeriya NFF ta naɗa alkalan wasa 30, waɗanda hukumar Kwallon Ƙafa ta Duniya FIFA ke bai wa bajo, don jagorantar manyan wasanni a duniya. A baya, Najeriyar na da irin waɗannan alkalai 27 ne, sai dai a bana an samu ƙarin guda uku, lamarin da ya sanya adadinsu ya kai 30, wannan adadi kuwa ya ƙunshi 22 maza sai kuma mata guda 8. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken sh...
A makon da ya gabata ne Hukumar Kula da Kwallon Ƙafar Turai UEFA, ta fitar da jadawabin yadda wasannin zagayen ƴan 16, na gasar zakarun Turai zai gudana. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh..........
Shirin ''Duniyar Wasanni'' tare da Khamis Saleh a wannan mako ya mayar da hankali kan yadda matsalolin alƙalanci ke ƙoƙarin yin illa ga gasar La liga guda cikin manyan lig-lig biyar da aka fi ji da su a nahiyar Turai, la’akari da irin zaratan ƙungiyoyi da kuma ƴan wasa dama masu horaswar da ke fafatawa a cikinta tsawon lokaci. A bana, salon alƙalanci a gasar ta La Liga na ɗaukar hankali, musamman ganin yadda alkalai ke bayar da katin gargaɗi da kuma na kora babu ƙaƙƙautawa, alal misali anga yadd...
Shirin ''Duniyar Wasanni'' tare da Khamis Saleh a wannan makon zai yi duba ne kan yadda ƴan kasuwa suka fara zuba jari a ɓangaren gina filayen wasanni, matakin da masana ke cewa zai ƙara ƙarfafa ɓangaren na wasanni musamman ga yara masu tasowa. Rashin kyauwun filiyen wasanni a nahiyar Afrika, na ɗaya daga cikin abubuwan da ke mayar da harkar wasan kwallon ƙafa baya, a matakin kwararru ko masu koyo ko kuma ga masu motsa jiki a faɗin nahiyar. Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin....
Shirin Duniyar Wasanni a wannan mako ya yi duba kan gasar zakarun Turai da aka kammala wasannin rukuni. A ranar larabar makon da ya gabata ne dai aka kallama wasanni rukuni na gasar zakarun Turai, wacce ita ce karo na 70 tun bayan faro gasar kuma karo na 33 bayan sauyawa gasar suna, sannan kuma wannan ne karo na farko da aka faro sabuwar gasar da aka sauya mata fasali. Latsa alamar sauti domin sauraren shirin....
Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokacin ya ziyarci gasar Firimiyar Ingila ne don duba sabon tarihin da ɗan wasan Liverpool Mohammed Salah ya kafa a gasar. Mohammad Salah dai a yanzu ya shafe tarihin Thierry Henry na zura kwallaye 175 a gasar Firimiyar Ingila, bayan da ya jefa kwallo a karawar da suka yi da Ipswich. A yanzu dai Mohammed Salah ne na 7 a jerin ƴan wasan da a tarihi suka fi yawan jefa kwallo a raga a babbar gasar ta Ingila. Ƴan wasan da a tarihi suka fi yawan jefa kwallo a gasar dai...
Shirin Duniyar Wassani a wannan makon ya yi duba ne game da kyautar gwarzon ɗan wasan Afrika da aka bayar. A ranar Litinin din da ta gabata ne dai Hukumar da ke kula da kwallon ƙafar nahiyar Afrika wato CAF, ta bayar da kyautar gwarzon nahiyar Afrika wanda yafi bajinta a wannan shekarar da muke bankwana da ita. Ɗan wasan gaba na tawagar Super Eagles ta Najeriya Ademola Lookman ne ya samu nasarar lashe wannan kyauta, biyo bayan irin bajintar da ya nuna ga ƙasar da kuma ƙungiyarsa ta Atlanta. Samu...
Shirin Duniyar Wasanni a wannan makon, yayi duba ne game da gasar kokuwar gargajiya a Jamhuriyar Nijar, wacce za a faro a ranar 20 ga wannan wata na Disamba nan a jihar Dosso da ke rike da takobi ko kambun gasar, inda ƴan wasa 80 daga Jihohi 8 na Nijar za su fafata har zuwa 29 ga watan, don samun sabon sarkin ƴan kokuwa wanda ke lashe kyautar takobi da kuɗaɗe da sauran kyautuka. Sai dai wani hanzari da ba gudu ba shi ne yadda a bana aka samu wasu sabbin sauye-sauye musamman ɓangaren dokokin wann...
Shirin Duniyar Wasanni a wannan makon ya yi duba ne kan yadda ƴan wasa a Lik din Najeriya ke fuskantar barazana a tafiye tafiye ta mota da suke yi don yin wasa. Yin amfani da motoci wajen jigilar ƴan wasan da ake fafatawa a gasar Lik ɗin Najeriya ba sabon abu bane, ganin yadda mafi yawancin ƙungiyoyin da ke fafatawa a wannan gasa sun fi amfani da motoci wajen kai ƴan wasansu jihohin ko garuruwan da za su fafata wasa. Irin waɗan nan tafiye tafiye dai na haifar da barazana ga rayuwar ƴan wasan mus...
Shirin Duniyar Wasanni na wannan mako yayi duba ne kan yadda aka kammala wasanni sojoji na nahiyar Afrika. Wannan ne dai karo na biyu da tawogogin ƙasashe 20 suka fafata a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, inda kuma tawagar ƴan wasan sojoji ta Najeriya ta zamo zakara, bayan da ta samu nasarar lashe lambar zinari 114 da azurfa 65 sai kuma tagulla 55 a jumlace ke nan ta samu lambobin yabo 234. Ƙasar Aljeriya ke bi mata a matsayin na 2 da lambar zinari 53 da azurfa 22 sai kuma agulla 21, a jum...
Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci ya yi duba ne kan yadda aka kammala wasannin neman gurbin shiga gasar lashe kofin Afrika. Kuma a tsakiyar makon daya gabata ne aka kammala wasannin neman gurbin zuwa gasar cin kofin AFCON da ke gudana tsakanin ƙasashen Afrika, gasar da Morocco za ta karɓi baƙunci a watan Disamban shekarar 2025. A yanzu dai dukkanin ƙasashe sun san makomarsu kuma ƙasashen 24 da za a ga haskawarsu a gasar ta baɗi sun ƙunshi ita mai masaukin baƙi Morocco da Burkina Faso da Kam...
Shirin Duniyar Wasanni a wannan makon ya yi duba ne kan irin gudummawar da cibiyoyin horar da matasa wasan kwallon ƙafa ke bayarwa wajen zakulo matasan ƴan wasa da horar da su a Nigeria. Wannan dai wani bangare ne na gudummawarsu ga ci gaban wasan kwallon ƙafa a Nigeria, tsofin ƴan wasan tawagar Super Eagles na ƙasar, sun fara kafa cibiyoyi masu zaman kan su, da su ke zakulowa tare da horar da matasa don yin fice a harkar ta kwallon kafa. Irin wadannan cibiyoyin horar da matasa wasan na kwallon ...
Shirin 'Duniyar Wasanni' na wannan makon ya yi dubi ne akan yadda aka gudanar da bikin bada kyautar Ballon d’Or ta shekarar 2024.
Shirin Duniyar Wasanni na wannan makon yayi duba ne kan yadda wasan El-Clasico ya gudana da kuma hukuncin da Hukumar Kwallon Ƙafar Afrika CAF tayi kan danbarwar Najeriya da Libya. A ƙarshen mako ne dai kwamin ladaftarwa na hukumar CAF, ya zartar da hukuncin cewa Najeriya ce tayi nasara da ci 3 da nema kan Libya, tare da tarar dala dubu 50. Haka nan shirin ya duba yadda wasan El-Clasico ya gudana tsakanin Real Madrid da Barcelona da aka yi a ƙarshen mako.
Shirin Duniyar Wasanni a wannan lokaci yayi duba ne kan danbarwar da aka samu tsakanin Najeriya da Libya. A makon daya gaba ne dai aka fara kai ruwa rana tsakanin bayan da tawagar Super Eagles ta Najeriya ta yi tattaki zuwa Libya don karawa da takwaransu ta ƙasar a wasa na biyu na neman gurbin zuwa gasar lashe kofin Afrika da za ayi a Morocco a shekara mai zuwa. Wannan al’amari dai ya haifar da cece-kuce a duniyar kwallon ƙafar, ganin yadda Super Eagles ta zargi hukumomin kwallon ƙafar Libya da ...
Shirin a wannan makon ya maida hankali ke kan yadda aka faro gasar Firimiyar Ingila, inda akwa yanzu kowace ƙungiya ta samu nasarar buga wasanni 7-7. Tuni gasar ta soma nisa, inda Liverpool take a saman teburi da maki 18, yayinda Arsenal da Manchester City ke biye mata da maki, 17, kowannen su. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Khamis Saleh......