Matsalar wariyar launin fata da wasu 'yan wasa ke fuskanta - podcast episode cover

Matsalar wariyar launin fata da wasu 'yan wasa ke fuskanta

Mar 10, 202510 min
--:--
--:--
Listen in podcast apps:
Metacast
Spotify
Youtube
RSS

Episode description

Shirin a wannan makon zai yi duba ne kan matsalar nan ta nuna wariyar launin fata da wasu ƴan wasa ke fuskanta.

Nuna wariyar launin fata a wasannin motsa jiki musamman ma kwallon ƙafa na ɗaya daga cikin ƙalubalen da ƴan wasa baƙaƙe ke fuskanta, matsala da ta shafe shekaru aru-aru ana fama da ita.

Wani lokaci ƴan wasa baƙar fata dai na fuskantar cin zarafin daga magoya baya ko masu horaswa, ta hanyar zagi kai tsaye ko wata alama ta nuna kaskanci ko kuma cin fuska, duk da cewa hukumomi na ɗaukar kwararar matakai don magance matsalar.

For the best experience, listen in Metacast app for iOS or Android
Open in Metacast
Matsalar wariyar launin fata da wasu 'yan wasa ke fuskanta | Wasanni podcast - Listen or read transcript on Metacast