A dukkan kwanakin karshen watan Disambar kowace shekara, lokacin ne da farin ciki ke cika a fuskokin Mabiya Yesu Almasihu don gudanar da bukuwaN ranar tunawa da haihuwar sa wato kirsimeti. Sai dai, wasu darikun addinin kirista da suka hada seventh day Adventist, Jehovah Witness da ma kuma darikar Deeper Life basu yadda da gudanar da wannan biki na kirsimeti ba. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi Nazari ne kan wannan batu don gano dalilan da suka sa wadannan dariku basa bikin kirsimeti....
Dec 25, 2024•28 min
Tururuwar da mutane suke yi zuwa manyan biranen Najeriya na barazana ga wadannan alƙaryu ta fuskar tsaftar muhalli. Misali, wani rahoto da Bankin Duniya ya fitar ya nuna cewa a duk sa'a daya birnin Legas kan yi baƙi 77 – hakan kuma kan haddasa karuwar sharar da ake zubarwa. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan yadda shara ke addabar wasu manyan biranen Najeriya da tasirinta a kan lafiyar jiki da ta muhalli.
Dec 19, 2024•28 min
A karshe dai an ayyana John Mahama a matsayin zababben shugaban kasar Ghana bayan da al’ummar kasar sun yanke shawarar zabensa lokacin da suka kada kuri’a ranar Asabar din da ta gabata. Duk da sauran ‘yan Takara da John Mahama ya kara da su, ciki harda mataimakin shugaban kasar mai ci a yanzu wato Mahamudu Bawumia Musulmi na farko da ya tsaya takarar shugabancin kasar. Shirin Daga Laraba na wannan makon zaiyi Nazari ne kan nasarar da John Mahama ya samu a zaben kasar Ghna da kuma kalubalen da za...
Dec 11, 2024•30 min
Kishin kasa na cikin abubuwan da shugabanni, da sauran masu ruwa da tsaki suke kira ga ’yan Najeriya a kullum a kansu. Muhimmancin kishin kasa ga cigaban al’umma, musamman a kasa mai kabilu da addinai daban-daban irin Najeriya, abu ne da ba zai misaltu ba. Sai dai alamu na nuna cewa yan Najeriya sun fi nuna kishin kabilun da suka fito idan aka kwatanta da kishin kasar da suke da shi. Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne kan wannan batu.
Dec 04, 2024•32 min
Matsalar tsaro na daga cikin batutuwan da suka hana kasar nan cikas a ‘yan shekarun nan. Kuma kamar yadda alumma ke bayyanawa akwai karancin jami’an tsaro da ya kamata ace suna lura, tare da kiyaye rayuka da dukiyoyin alumma a koda yaushe. Karancin jami’an tsaron ne ya sa wasu daga cikin jihohin da rashin tsaron yafi kamari suka samar da wasu jami’an tsaro dake taimaka wa jami’an tsaron gwamnati wajen dakile haren haren da yan ta’adda ke kaiwa a wasu yankunan kasar nan. Shirin Daga Laraba na wan...
Nov 27, 2024•30 min
An daɗe ana muhawara, musamman a Arewacin Najeriya, a kan buƙatar yin garambawul ga tsarin makarantun tsangaya. A baya dai waɗannan makarantu kan samar da mahaddata alqur’ani waɗanda kuma sukan dogara da kai Sai dai a wannan zamani, yaran da suke karatu a ƙarƙashin tsarin sun zama mabarata. Gwamnatoci da dama dai sun yi kokarin yin garambawul ga yadda ake gudanar da tsarin, amma ga alama haƙa ta kasa cimma ruwa. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi Nazari ne kan hanyoyin da za a bi don maga...
Nov 20, 2024•25 min
A zamanin nan, ana alakanta almajirai da bara – hasali ma a lokuta da dama akan yi amfani da kalmar “almajiri” idan ana nufin mabaraci. Amma a da ba haka lamarin yake ba – almajiri bay a bukatar yin bara ko roko kafin ya sami na sakawa a bakin salati. Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne a kan yadda almajirci ya sauya salo a wannan zamani da ma irin halin da almajirai suka tsinci kan su a ciki.
Nov 13, 2024•30 min
Kalmar almajiri ta samo asali ne daga yaren larabci wato almuhajir, dake nufin wanda ya bar garin sa don zuwa wani gari neman ilimi. Mafi yawan alummar arewa inda akafi sanin Kalmar sun taso ne sun ga ana gudanar da karatun allo ko almajirci, wanda hakan ke nufin almajirci ya samo asali ne tun lokacin da musulunci ya fara shigowa Najeriya daga garin Maidugurin Jihar Borno zuwa kasar Hausa. Shirin Daga Larab na wannan mako yayi duba ne kan tarihin almajirci da kuma yadda yake a da can baya....
Nov 06, 2024•24 min
Taron da Kungiyar Gwamnonin Arewa (NGF) ta yi a Kaduna ya bar baya da kuria’a. Daya daga cikin shawarwarin da gwamnonin suka yanke ita ce ta kin amincewa da wani Kuduri da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya kai Majalisar Dokoki ta Kasa. Shin kishin Arewa ne ya sa gwamnonin suka yi Allah-wadai da Kudurin ko kuma son zuciya? Wannan ce muhawarar da ta biyo bayan sanarwar bayan taron na NGF, kuma shirin Daga Laraba zai lalubo amsarta.
Oct 30, 2024•28 min
Tarbiyya kamar yadda aka san ta a al’adance tana inganta ne idan al’umma gaba daya ta hada hannu wajen ladabtar da yara. Duk wanda ya kai shekaru talatin zuwa sama ya san cewa a da can iyaye da sauran jama’ar gari suna iya daukar tsumagiya don ladabtar da shi idan ya kauce hanya. Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi duba ne kan alfanun ko illar hakan wajen ladabtar da yara.
Oct 23, 2024•26 min
Afrika na da dadadden tarihin girmama na gaba, musamman dattawan da ke cikin al’umma. Sai dai a wannan zamani akan samu matashi ya shafa wa idonsa toka ya fito bainar jama’a yana musayar zafafan kalamai da sa’o’in mahaifinsa. Shin me ya sa ake samun irin wannan? Don jin amsar wannan tambaya da ma wasu sai ku biyo mu a cikin shirin Daga Laraba na wannan makon.
Oct 16, 2024•30 min
Sau da yawa akan samu rashin fahimtar juna a duk lokacin da wata mu’amala ta haɗa mata. Misali, a asibiti wajen haihuwa mata sun sha kokawa da yadda suke ce ’yan uwansu suna nuna musu rashin tausayi. Shirin Daga Laraba zai tattauna a kan wannan lamari, ya kuma auna shi a kan mizanin magamar da matan kan yi cewa “Ciwon ’ya mace na ’ya mace ne”.
Oct 09, 2024•30 min
Wata muhawara da ta karade shafukan sada zumunta a kwanakin nan ita ce ko ’yan Arewa, musamman Hausawa, suna fita kasashen waje. Duk da wannan ba wani sabon abu ba ne, batun ya dauki sabon salo ne a shafukan sada zumunta, musamman Facebook da TikTok, inda ’yan kudancin Najeriya suke wallafa fayafayen bidiyo suna tambayar: shin Hausawa suna zuwa kasashen waje? Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne kan wannan batu.
Oct 02, 2024•28 min
Yanayin tattalin arziki da ma wasu dalilai kan tilasta wa mutane da dama, ciki har da masu karbar albashi a karshen wata, neman wata hanya ta daban dake kawo Karin kudade. Shin mene ne yake kawo hakan, kuma mene ne tasirinsa a kan rayuwar masu buga-bugar da ma al’umma? Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne a kan irin buga-bugar da ’yan Najeriya suke yi don sama wa kansu mafita.
Sep 25, 2024•23 min
Sama da mako guda ke nan bayan komawa makarantu domin fara sabon zangon karatu a kusan dukkanin sassan Najeriya. Sai dai rahotanni sun yi nuni da cewa, ana samun karancin komawar dalibai makaranta a wasu sassan kasar. Shirin Daga Laraba na wananan makon zai yi duba ne a kan dalilan faruwar hakan.
Sep 18, 2024•25 min
Dangantaka ko alaka a tsakanin Najeriya da China tana ƙara yaukaka, musamman a baya-bayan nan. Ko a kwanan nan, Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci wata tawaga zuwa kasar ta China domin halartar taron kyautata alakar kasuwanci tsakaninta da kasashen Afirka. Shirin Daga Laraba na wananan mako zai tattauna a kan ko mecece ribar ’yan Najeriya a irin wannan dangantakar?
Sep 11, 2024•29 min
A duk lokacin da dogon hutun zangon karatu na karshe ya kare, iyaye su kan kasance cikin taraddadin yadda zasu fuskanci komawar Yara makaranta, saboda dumbin bukatu da yanayin ke zuwa dasu. Shin, me ya kamata, iyaye da masu makantu su fi mayar da hankali a kai, musamman la'akari da irin yanayin tsadar kayayyaki da kuncin rayuwa da ake fama dasu a Najeriya? Shirin Daga Laraba na wananan mako, zai tattauna ne kan wannan batu na komawa makanta bayan hutun dogon zango....
Sep 04, 2024•22 min
Duk da cewa, a wuni daya ne ake bikin ta, amma muhimman al'adun Hausawa da ake tattaunawa game dasu a ranar Hausa Ta Duniya, suna da tasiri a rayuwar al'umma ta yau da Kullum. Wata dadaddiyar al'ada da aka san al'ummar Hausawa da ita, ita ce al'adar nan ta fito da Abinci daga gidajen makota, inda ake haduwa aci tare musamman ma a Kullum da daddare. Shirin Daga Laraba na wananan mako, zai tattauna ne kan muhimmancin wannan Al'ada, musamman la'akari da irin halin da ake ciki yanzu a Najeriya....
Aug 28, 2024•26 min
Majalisar dinkin duniya ta ware ranar 21 ga watan Agusta domin tunawa da wadanda ayyukan ta’addanci ya rutsa da su. A duk lokacin da mutum ya fada hannun ‘yan ta’adda ko rikicin ta’addanci ya rutsa da su, sukan dade cikin damuwa a ransu. Shirin Daga Laraba na wannan mako zai tattauna kan wannan rana da abin da ya kamata a yiwa irin wadannan mutane.
Aug 21, 2024•26 min
A Najeriya babban bankin kasa CBN ya bayar da wa’adi ga bankunan domin tara adadin wasu kudade a matsayin jarinsu ko kuma su hade guri daya da masu karamin karfi a bankuna. A halin yanzu wasu har sun fara hadewa da wasu bankunan, duk da yake ba sabon abu ba ne hadewar bankuna waje guda a Najeriya. To amma me ke faruwa indan bankunan suka hade? shin lamarin na shafar kwastomomi? Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi bayani kan abin da ke faruwa a duk lokacin da bankuna suka yi maja a waje da j...
Aug 14, 2024•23 min
Gwamnati na fidda shafukan da ‘yan kasa za su iya neman bashi ko tallafi, a lokaci guda kuma masu zamba ta intanet na bullo da shafukan bogi domin yaudarar al’umma. Yana da kyau mutum ya iya tantance shafin da za a iya yi masa kuste musamman abin da ya shafi kudi. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi bayani kan yadda za ku tantance shafukan intanet na tallafin gwamnati na bogi da na gaske.
Aug 07, 2024•24 min
Lokaci na tafiya kuma matasa na turjiya kan shirinsu na zanga-zanga, duk da matakan da gwamnati ke ta dauka. Ana ta kokarin ganin zanga-zangar ta yiwu cikin lumana, domin kauce wa rikidewa zuwa ta tarzoma. Shirin Daga Laraba zai tattauna kan hanyoyin da suka kamata gwamnati ta bi domin samun mafita kan zanga-zanga.
Jul 31, 2024•28 min
A wannan yanayi na damina kusan kullum wuni ake yi ana tafka ruwan sama a wasu sassan Najeriya. Akwai masu sana’o’in da sai sun fita za a samu taro da sisi amma kuma babu hali. Shirin Daga Laraba zai tattauna lan dabarun da ya kamata masu sana’o’i su yi amfani da su domin ganin ruwan sama bai dagula musu lissafi ba.
Jul 24, 2024•23 min
Tun bayan janye tallafin man fetur, gwamnati ke ta rarraba kayan abinci ga talakawa domin rage musu radadi. A wannan makon Shugaban Kasa Bola Tinubu ya bayar da umarin raba tirela 20 ga kowace jiha a Najeriya da Birnin Tarayya duk da wasu na wannan salo ba ya tasiri. Shirin Daga Laraba ya duba yadda tallafin abincin daga gwamnatin zai magance damuwar talakan Najeriya.
Jul 17, 2024•25 min
Kusan ko wace damina sai hukumomi sun gargadi mazauna wasu yankuna game da yiwuwar samun ambaliyar ruwa. A bana ma Hukumar Hasashen Yanayi ta Najeriya (NiMET) ta yi gargadin cewa jihohi kusan 31 za su fuskanci ambaliyar da rushewar gine-gine. Shirin Daga Laraba ya tattauna kan abin da ya kamata a yi domin kauce wa asara sakamakon ambaliya.
Jul 10, 2024•30 min
Ana ci gaba da tafka muhawara a kan abin da ya kamata mutum ya fi bai wa muhimmanci a tsakanin digiri da sana’a. Shin wanne ne daga ciki mafi a'ala a rayuwar mutum? Shirin Daga Laraba zai yi muhawara a kan wannan batu.
Jul 03, 2024•30 min
Yayin da ake kammala taron yini biyu a kan matsalar tsaro a shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya, hankali ya karkata zuwa ga mataki na gaba. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai duba yadda gwamnonin yankin suka shirya aiwatar da abin da aka cimma.
Jun 26, 2024•23 min
Hawan Daushe al’ada ce ta sarakunan Kasar Hausa a lokacin bikin Sallah. A masarautar Zazzau a kan yi wannan hawa a ranar ukun Sallah da yamma, kuma yakan tara ‘yan Kallo daga wurare daban-daban ciki har da Kano. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai duba yadda aka yi hawan na bana da yadda ya samo asali musamman a masarautar Zazzau.
Jun 19, 2024•29 min
Yayin da wasu mazan suke kyale matansu su yi aiki, wasu kan yi kememe su ki bari nasu matan su yi. Shin barin matar aure ta yi aiki ne ya fi alheri ko hana ta? Wadanne dalilai kowanensu ke da su? Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba a cikin wannan lamari.
Jun 12, 2024•25 min
A yanayi na rashin lafiya a kan ga wasu maza na tuburewa likita namiji ba zai duba musu iyali ba, musamman wajen haihuwa a asibitoci. Amma akwai matan da su ma a ganin su, kunya kan hana su sakin jiki likitoci maza su duba su. Shirin Daga Laraba na wannan makon ya yi nazari a kan meyasa wasu basu yarda likita namiji ya duba matansu a asibiti.
Jun 05, 2024•29 min