Daga Laraba - podcast cover

Daga Laraba

Shiri ne da ke tattaunawa mai zurfi a kan batutuwan da suka shafi al'umma kai-tsaye, da nazari a kan tasirin da za su iya yi, da nemo hanyar magance ko kauce wa illolin da za su iya hifarwa bayan jin ta-bakin wadanda abin ya shafa.

Last refreshed:
Follow this podcast in the Metacast mobile app to refresh it and see new episodes.
Download Metacast podcast app
Podcasts are better in Metacast mobile app
Don't just listen to podcasts. Learn from them with transcripts, summaries, and chapters for every episode. Skim, search, and bookmark insights. Learn more

Episodes

Ƙalubale Da Ci Gaban Dimokraɗiyar Najeriya Cikin Shekara 25

Najeriya ta cika shekara 25 cikin tsarin dimokradiyya ba tare da katsewa ba. Ana kan tsari ne na shugaban kasa mai cikakken iko tun daga 1999 a ranar 29 ga watan mayu, duk da yake an sauya bikin wannann rana zuwa 12 ga watan Yuni. Toh shin wane irin ci gaba ko akasin haka aka samu cikin wadannan shekaru 25? Shirin Daga Laraba na wannan mako ya tattauna kan wannan cikar Najeriya shekara 25 cikin mulkin dimokradiyya.

May 29, 202429 min

Abin Da Ke Sa Fararen Hula Su Raina Sojoji

Mu’amalar farar hula da sojoji a Najeriya ta mutuntuwa ce wadda zarar aka hangi soja a cikin gari jiki har karkarwa yake. Sai dai a ‘yan kwanakin nan a iya cewa yadda labarai ke yawan fita game da yadda fararen hula ke yin tsaurin ido wajen takalar sojoji da fada yana karuwa. Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba abin da ya sa fararen hula ke kokarin daga hannunsu kan jami’an tsaro musamman na soji.

May 22, 202423 min

Abubuwan Da Aka Haramta Wa Mai Aikin Hajji

Yau Laraba rukunin farko na maniyyata Hajjin bana daga Najeriya za su tashi zuwa kasa mai tsarki Duk da matsin tattalin arziki da ake ciki a kasar nan, akalla mutum sama da 50,000 ne ake sa ran za su sauke faralin daga Najeriya. Shin wane abu maniyyatan ya kamata su maida hankali a kai? NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Sa Masu Gidajen Haya Suke Tsuga Kudi DAGA LARABA: Dalilan Da Za A Hana ’yan kasa da shekara 18 shiga jami’a Shirin Daga Laraba na wannan mako yana dauke da amsohin wadannan bayanai game...

May 15, 202430 min

Dalilin Da Za A Hana ’Yan Ƙasa Da Shekara 18 Shiga Jami’a

Idan aka zagaya jami’o’i ana samun dalibai da dama wadanda ba su wuce shekara 15 ba a aji. A yanzu zamani ya sauya, abin ya zama Ruwan dare. Mai yiwuwa a lokacin da kuke makarantar firamare ko sakandare kun hadu da wadanda aka yiwa tsallaken aji, wato a bai wa dan aji 4 damar rubuta jarabawar kammala firamare ko kuma dan SS2 damar rubuta WAEC ya wuce jami’a Wannan ne ya sa gwamnatin tarayya ta ce za a tabbatar da dokar hana duk wanda bai kai shekara 18 ba zuwa matakin gaba da sakandare. Shirin D...

May 08, 202424 min

Muna Rayuwa A Cikin Ƙunci - Ma’aikatan Najeriya

Yau ce ranar 1 ga watan Mayu da aka ware a Najeriya da wasu sassan duniya domin jinjina ga rawar da ma’aikata ke takawa wajen ci gaban kasa. Sai dai yayin da 'yan Najeriya da dama ke kuka da halin da aka shiga na ƙuncin rayuwa, ma'aikata na kan gaba wajen bayyana yadda suka ce suna tagayyara kuma aikin ba riba ta wani ɓangaren. Shirin Daga Laraba na wannan makon ya duba yadda rayuwar ma'aikata a Najeriya ke kasancewa da sauyin da ake fatan samu.

May 01, 202426 min

Me Ya Sa Kamfanonin Lantarki Suke Fifita ‘Yan ‘Band A’?

Bayan komawa tsarin rukuni daban-daban na bayar da wutar lantarki Idan kamfanoni na neman afuwa to yawancin ga ‘yan rukunin farko ne. Wasu na ji a ransu kamar su ba kwastomomi bane ga kamfanonin domin kulawar da ake ba su ta nuna ba a tare da su. Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba abin da ya sa hankalin kamfanonin wutar lantarki ya karkata wani fanni.

Apr 17, 202426 min

Yadda Sabbin Ma'aurata Ke Morewa A Ramadan

A watan Ramadan sabbin ma'aurata na alfahari da azuminsu na farko a gidan aure. Shin mene ne abin da yake kayatar da gidan aure musamman a wannan lokaci na Ramadan? Ya ya kamata ma'aurata su kasance? Shirin Daga Laraba na wannan mako ya tattauna yadda ma'aurata ke samun tabarruki da falala a yanayinsu na farko.

Apr 03, 202423 min

Abubuwan Da Ba A So Mai I'itikafi Ya Aikata

I’itikafi sunna ce mai karfi a wannan lokaci, kuma jama’a masu sukunin shiga na kwashe kwanaki kusan goma a masallaci wajen ibada. To amma me ya kamata ku sani gameda shiga itikafi kuma wadanne abubuwa ake son mutum ya kiyaye a lokacin? Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba matakan yin i'itikafi da abubuwan da ya kamata ku sani gameda hakan.

Mar 27, 202423 min

Abin Da Ake Yi A Goman Tsakiyar Ramadan A Addini Da Al'ada

A yayin da ake shiga goman tsakiya na watan Ramadan, malamai na kira ga al’umma da su dage wajen ibadu domin samun dacewa. A al’adance a wannan goma ta tsakiya akwai wasu al’adu musamman na tashe da kuma kirarin goma ta wuya bayan ta marmari. Shirin Daga Laraba ya yi tsokaci ne a kan wasu abubuwa da da ake yi a goman tsakiyar Ramadan a addinance da al'adance.

Mar 20, 202429 min

Abin Da Addini Yace Game Da Azumin Ƙananan Yara

Watan ramadana na jefa shauki a zukatun yara masu tasowa ta yadda har rige-rige ake tsakanin juna na ganin an kai wannan munzali. Shin ta wace hanya ya kamata iyaye su bi domin koya wa yarasu azumin ramadana? Shirin Najeriya a Yau ya duba matakan koyawa yara azumin ramadana cikin sauki.

Mar 13, 202422 min

'Amfani Da Tsaffin Takardun Naira Zai Iya Jefa Mutum A Matsala'

Mutane da dama sun shaida cewa takardar Nairar Najeriya na saurin lalacewa. Wasu na ganin masu liki a wajen bukukuwa da yadda ake kasuwancin sabbin kudi na taka rawa. Toh amma me ya kamata a yi, me kuma doka tace kan kudin da suka tsufa suka lalace. Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba halin da mutum zai iya jefa kansa idan har aka same shi da wulakanta takardun Naira da yadda za a bada gudummuwa wajen inganta kudin.

Mar 06, 202424 min

"Ruwan 'Fiyowata' Na Neman Ya Gagari Talaka"

Tsadar rayuwa ta sa ruwan leda wato 'fiyowata' ya fara zama abin tattaunawa gameda yadda yake tsada. Wasu na ganin shine ruwan da ake samu mai dama-dama wajen tsafta idan mutum na so ya sha ruwa, sai dai yadda yake kara tsada a sassa daban-daban na Najeriya ya sa ana komawa shan ruwa mara tsafta a wasu wuraren. Sai dai masu sarrafa ruwan na cewa ba daga su ba ne, inda har ta kai ga wasu na rufe kamfanoninsu. Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba dalilin da suka jawo hakan....

Feb 28, 202422 min

Harshen Uwa: Dalilin Da Mutane Ke Mance Yarensu Na Asali

Wannan rana ce majalisar dinkin duniya ta ware a matsayin ranar harshen uwa ta duniya. Majalisar Dinkin Duniya ta ce kashi 40 cikin 100 na al’ummar duniya ba sa samun ingantaccen ilimi ne saboda rashin amfani da yarukansu na asali. Wasu harsuna na fuskantar barazanar shafewa a duniya saboda iyaye sun daina koyar da ’ya’yansu yadda za su yi magana da harshen. Shirin Daga Laraba na dauke da karin bayani.

Feb 21, 202429 min

Ranar Masoya: 'Da Wuya A Samu Soyayyar Gaskiya A Yanzu'

Ranar masoya kan dauki hankali a ranar 14 ga watan Fabreru, inda yawancin masoya ke kure malejin soyayyarsu. Amma akwai masu ganin ba lallai a samu soyayyar gasakiyaa yanzu ba. Sai dai ko kun san yadda aka yi wannan ta samo asali? Albarkacin ranar masoya Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba tasirin wannan rana da salsalar ta.

Feb 14, 202426 min

Yadda ‘Yan Arewa Za Su Samu Kuɗi A Soshiyal Midiya

Kafafen sada zumunta sun zama farfajiyar baje kolin basira, yayin da ta kan zame musu hanyar bayyana damuwa da share kokensu. Ana yawan buga misali da cewa an yiwa yankin Arewacin Najeriya nisa wajen samun tagomashin a soshiyal midiya. Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba dabarun da masu amfani da shafukan za su bi wajen ganin sun amfana yadda ya kamata.

Feb 07, 202426 min

Yadda Takura A Wajen Aiki Ke Ta'azzara Rayuwar Ma'aikaci

A duk lokacin da ma’aikaci ya tsinci kanshi a ofishi mai matsin lamba da takura, masu sharhi na ganin aiki bai cika tafiya daidai ba. Wasu wuraren aiki na fuskantar matsin lamba daga oganni ko kuma tsarin aiki da zai sa a yi ta korafi. Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba yadda wuraren aiki masu matsin lamba ke takura rayuwar ma’aikata da yadda za a warware damuwa a irin wannan yanayi.

Jan 31, 202429 min

Matakan Kariya Daga Kwantawa Rashin Lafiya

Lafiya dai ita ce uwar jiki, babu mai fushi da ita. A yanayin da aka ciki babu mai son ya ga ya kwanta rashin lafiya, domin ana lallaba halin da ake ciki. Jama’a na kokawa a fannoni da dama yayinda wasu kyale batun ziyartar asibiti ko shan magani ko da sun ji alamar canji a jikinsu. Ku kasance da shirin Daga Laraba na wannan mako domin wasu dabarun da za su taimaka wajen ganin ba ku kwanta rashin lafiya ba.

Jan 24, 202426 min

Yadda Wasan Kanawa Da Zagezagi Ya Samo Asali

Abu ne da za a iya cewa sananne ga al’ummar Kano da Zazzau na tsokanar juna a tsakaninsu. Ana yawan taƙaddama kan shin wane ne mai gida tsakanin Kanawa da Zazzagawa. A cikin shirin Daga Laraba na wannan mako mun duba tasirin wannan wasa tsakaninsu da kuma yadda ta samo asali.

Jan 17, 202426 min

Matsalolin Da Suka Kewaye Kannywood

Rade-radin matsaloli basa karewa dangane da masanaantar shirya finafinai ta Arewacin Najeriya mai cibiya a Kano Kannywood. Shin mene ne abin da ke hana Kannywood cigaba kamar sauran takwarorinta na duniya? Shirin Daga Laraba na wannan mako ya dubi boyayyun matsalolin da suka dabaibaye Kannywood.

Jan 10, 202430 min

Ina Aka Kwana A Binciken Harin Tudun Biri?

Yanzu wata guda kenan tun bayan da sojoji suka yi kuskuren kai hari kan masu Maulidi a garin Tudun Biri dake jihar Kaduna. Harin ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 100, inda hukumomi da gwamnati ba su yi wata-wata ba wajen daukar alhakin hakan da kuma bayyana cewa za a yi abin da ya dace wajen bin hakkin waɗanda lamarin ya shafa. Toh shin zuwa yanzu wane hali ake ciki? Ko an fara bincike kuwa? Ina kudaden da aka tara na tallafi suke? Shirin Daga Laraba na wannan mako ya yi nazari na musamman a k...

Jan 03, 202426 min

Abin Da Zai Faru Idan Mutum Ya Cika Cin Goro

Tasirin goro ga masu cinsa yana zama abu mai wahala mutum iya dainawa. Goro na da mahimmanci a Kudancin Najeriya musamman ga Kabilar Igbo. Haka ma yawanci dattawa a Arewacin Najeriya har ma matasa da mata a wasu lokutan suna cin goro, inda abin ya kan zame musu jiki, yayinda ake amfani da shi a wajen taruka na aure ko suna duk da ba a nomanshi a yankin. Shirin Daga Laraba na wannan makon ya duba abin da ya sa masu cin goro basu iya dainawa da kuma abin da masana suka ce zai iya faruwa idan cinsa...

Dec 27, 202328 min

Mahimmancin Barin Wasiyya Tun Kana Da Rai

Da zarar an ambaci wasiyya sai mutum ya fara tunanin mutuwa, ko wani abun na daban a rai. Wasu kan bar wasiyya ko da za su yi tafiya zuwa anguwa saboda gudun riskar wa'adi a lokacin da ba shiri. Shin ya mahimmancin wasiyya take da kuma tasirin hakan? Ku biyo mu shirin Daga Laraba na wannan makon domin jin mahimmancin barin wasiyya tun mutum na raye.

Dec 20, 202327 min

Dalilin Da Maza Ke Haura Shekar 40 Babu Auren Fari

Maza da dama na son aure amma kuma su kan ce fargabar ɗawainiya ta hana su. Wasu kuma na cin karo da ƙalubale tun a wajen nema, lamarin da ya sa suke zarta shekarun samartakansu ba aure. Toh shin da gaske ne abinda suke fada na cin karo da kalubale bayan aure Ku biyo mu cikin shirin Daga Laraba na wannan makon inda muka duba yadda wasu mazan kan shafe sama da shekara 40 ba aure.

Dec 13, 202327 min

Da Gaske Shan Garin Kwaki Na Kashe Ido?

Shin kun yarda cewa garin kwaki na kashe ido ko zuƙe ruwan jiki? Wasu na shan gari a matsayin abinci su koshi, yayinda wasu ke sha dan marmari. A cikin shirin Daga Laraba na wannan makon mun duba gaskiyar zancen cewa garin kwaki yana kashe lafiyar ido ko akasin haka.

Dec 06, 202325 min

Yadda Za Ku Gane Kuna Da Ƙarancin Suga A Jikinku

Mutune kan ziyarci asibiti domin gwaji inda a wasu lokutan ake bayyana musu cewa suna da karancin suga a jikinsu. Akwai alamomin da masana ke cewa su ke nuna mutum na da karancin suga a jiki, amma kuma akwain abubuwan da ke haddasa hakan. Shirin Daga Laraba na wannan makon ya duba yadda za ku gane kuna da karancin suga a jikinku da kuma matakan kariya.

Nov 29, 202326 min

Abin Da Ya Sa Kotu Ta Tsige Gwamnonin Arewa Huɗu

Bayan watanni tara da kammala zaben 2023 da zubar da wasu jiga-jigan yan siyasa, bangaren shari’a ma na cigaba da zartar da hukunci, inda zuwa yanzu aka tsige akalla gwamnoni hudu daga jam’iyyu daban-daban. Wasu na ɗiga ayar tambaya kan saƙaƙiyar da alƙalai ke amfani da su wajen yanke hukunci a kotunan. Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba ainihin dalilan da suka sa kotunan tsige gwamnonin huɗu zuwa yanzu.

Nov 22, 202325 min

Ƙalubalen Da Matan Aure Ma'aikata Ke Fuskanta

Mutane na tunanin matan aure dake aiki ba sa iya sauke haƙƙoƙin da suka rataya a wuyansu saboda tarin uzuri a wuyansu da kuma kula da iyali Ko da yike akwai matan da suke da jajircewa a wajen aikinsu matuka. A shirin Daga Laraba na wannan mako mun yi nazarin rayuwar matan aure masu aiki da irin yadda suke magance kalubalen da suke fuskanta.

Nov 15, 202328 min

Abin Da Ya Sa Ba a Ɗaukar Hoton Alƙali a Kotu

Duk wanda ya taɓa halartar zaman kotu zai iya bayar da shaidar cewa ba wurin wargi bane, ya zama wajibi mutum ya kama kansa tare da girmama alƙalai. Mutane na yawan tambayar ko me ya sa ba a barin jama’a su ɗauki hoto ko bidiyon alƙalai a lokacin shari’a a Kotu? Shirin Daga Laraba na wannan mako ya duba abin da doka tace gameda hana ɗaukar hoton alƙalai a kotu

Nov 08, 202330 min

Yadda Amare Suka Mai Da Ankon Bikinsu Hanyar Tara Kuɗaɗe

Ƙawayen amarya na yawan korafi a duk lokacin da suka ji labarin kawar su za ta yi aure kuma lokaci ya matso kusa, ba wai dan ba su son ta yi ba, aa sai dan tunani da zura ido domin ganin samfurin ankon da za a fitar. Wasu amaren kan tsuga kudi a kan ankon bikinsu kuma su tilasta kawaye a lalai tilas sai sun siya a hannun su, baki isa kije kasuwa ki siya ba, idan ma kin samu din toh lallai wannan kulli watakila zai kasance zuciyar amarya har tsawon lokaci. Shirin Daga Laraba ya duba yadda wasu am...

Nov 01, 202323 min

Dalilin Da Aka Kasa Magance Rikicin Manoma da Makiyaya

Gwamnati ta sha bullo da tsare-tsare da nufin magance tashe-tashen hankulan tsakanin makiyaya da manoma a sassan kasar nan. Sai dai lamarin ya ki ci, ya ki cinyewa, inda wasu ke ɗora laifin hakan a kan yadda bangarorin suka kasa gane cewa kowannensu na bukatar dan uwansa. Shirin Daga Laraba na wannan makon ya duba abin da ya sa rikicin makiyaya da manona a Najeriya ya ƙi ci, ya ƙi cinyewa.

Oct 25, 202328 min
Hosted on Buzzsprout
For the best experience, listen in Metacast app for iOS or Android