HausaRadio.net - podcast cover

HausaRadio.net

HausaRadio.net
HausaRadio.net - Online Hausa Radio
Last refreshed:
Follow this podcast in the Metacast mobile app to refresh it and see new episodes.
Download Metacast podcast app
Podcasts are better in Metacast mobile app
Don't just listen to podcasts. Learn from them with transcripts, summaries, and chapters for every episode. Skim, search, and bookmark insights. Learn more

Episodes

"Daga Laraba" 001 na Aminiya da Daily Trust Podcast Tare da Halima Djimrao

Daga Laraba 001 na Aminiya da Daily Trust Podcast Tare da Halima Djimrao Ga shirin mu na podcast wanda Halima Djimrao ce ta jagoranta tare da sauran abokan aiki. Shiri ne akan yadda ƴan ƙabilar Igbo Musulmi ke cikin tsangwama da barazana a yankin su na kudu maso gabashin Najeriya, saboda haka da yawan su, sun gwammace su yi hijira zuwa arewa. Podcast Trailer: https://youtu.be/qzLb2V9521U...

May 24, 202116 min

Komai muka samu mu fassara zuwa yaren mu Hausa - Malam Habibu Sani Babura

Allah akbar! Wannan muryar marigayi, Malam Habibu Sani Babura kenan, yayin da yake lacca a wajen taron daliban Hausa a Jami'ar Bayero ta Kano. Yau shekara biyu da rasuwar Malam (3/8/2018. Allah ya jikansa da rahama. Allah ya gafarta masa. Allah ya Sada shi da Annabi, Allah ya bashi aljanna Firdausi).

Sep 04, 20203 min

#RanarHausa 2020 - Shirin Daga Taskar Hausa Daga Guarantee Radio 94.7 Kano

Shirin Daga Taskar Hausa inda aka tattauna da Farfesa Aliyu Muhd Bunza da Dakta Abdulƙadir L Koguna da kuma Dakta Muhammad Suleiman A., a kan Ranar Hausa ta Duniya wato 26 ga watan Ogusta 2020. Ku kasance da shirin a yau, Lahadi, ƙarfe 8 zuwa 9 na dare. Daga Guarantee Radio 94.7 Kano a ranar Lahadi Aug 23, 2020. Za ku iya saurara kai tsaye daga ko'ina a www.guaranteeradio.com...

Aug 24, 202039 min

Kaucewa #LabaranBogi (Stopping the spread of #FakeNews in Hausa media)

Kai tsaye acikin shirin #ZararBubu da @CDDWestAfrica ke daukar nauyin kawowa masu sauraro dan wayar da kai game da #LabaranBogi, Dr. Nura Ibrahim ke jawabi game da yadda za'a kaucewa labaran bogi a shafukan sada zumunta na zamani. Related links: https://twitter.com/CDDWestAfrica_H/status/1286959730716545026 https://youtu.be/aOgO9amMnl4 #ADainaYadaLabaranKarya #ADenaYadaLabaranKarya #StopFakeNews #StopSpreadingFakeNews #FakeNews #HausaFakeNews #FakeHausaNews #LabaranBogi...

Jul 25, 202022 min

Asalin Ranar Hausa 2015 - Shirin VOA Hausa na Yau Da Gobe

Jamila Kabiru Fagge da Bashir Ahmad sun tattauna akan #RanarHausa August 26, 2015 Originally released August 28, 2015 on https://www.voahausa.com/a/2918757.html and https://soundcloud.com/voahausa/yau-da-gobe-134 ....

Jul 25, 202019 min

Hausa News Headlines - Kanun Labaran Hausa na 2020.05.08

Full transcript: http://hausadictionary.com/hausaradio/20200508 1 Kanun Labaran DW Hausa - Shirin Yamma 08.05.2020 2 Kanun Labaran VOA Hausa - Shirin Dare 2030 UTC (30:00) - Mayu 08, 2020 3 Kanun Labaran RFI Hausa 20h00 - 20h17 GMT - Labarai 08/05 20h00 GMT 4 Kanun Labaran Talabijin na BBC Hausa 08/05/2020 5 Kanun Labaran Radio VOH 3 - 20200508...

May 09, 20205 min

RFI Hausa News Headlines: Kanun Labarai na Shirin 07h00 Asabar 2019.05.18

Host (mai gabatarwa): Abdullahi Isa K'asashe masu k'arfin tattalin arziki da aka sani da G7 sun gudanar da taro a birnin Paris , taro da ya mayar da hankali zuwa ga batutuwan da suka shafi kiwon lafiya . Yayin da gwamnatin k'asar Venezuela da kuma 'yan adawa da ke cigaba da kai ruwa rana suka soma tattaunawa a Norway. Za ku ji cewa shafin sada zumunta na Facebook ya san da rusar wasu shafuka 216 na k'arya wadanda ake amfani da su domin rubuta kalamai ko kuma batutuwa da ba su dace ba zuwa wasu k...

May 18, 20191 min

VOA Hausa News Headlines: Kanun Labarai na Shirin Safe na 2019.05.17

Hosts (masu gabatarwa): Grace Alheri Abdu, Baba Yakubu Maƙeri US: Shugaban Amurka Donald Trump a jiya Alhamis ya sanar da wani sabon tsarin dokan bakin haure , wanda zai [unintelligible] gurbin baki d’ayan dokan bakin haure a nan Amurka. US: A wata sabuwa kuma Donald Trump ya ce yana k'ir da zaton Amurka ba za ta shiga da yak'i a Iran ba a lokacin da ake k'ara samun tankiya a gabas ta tsakiya . Burkina Faso : Bayan haka , ministan harkokin wajen Burkina Faso ya yi kira ga k'asashen duniya su kaf...

May 18, 20192 min

BBC Hausa News Headlines <> Kanun Labarai na Shirin Safe na 2019.05.17

Host Mai gabatarwa: Aisha Sharif Baffa Yau ce dai ranar yak'i da cutar hawan jini , wato hypertension , ta duniya . Toh ko ya mutum zai kare kansa daga kamuwa da wannan cuta ? " Farko , mutum ya zama cewa yana yawan motsa jiki . Sannan kuma a … Read More at http://bit.ly/BBCHausaSafe20190517 Thank you for subscribing. Share this episode ....

May 17, 20192 min

DW Hausa Shirin Safe na 2019-03-01

DW Hausa Shirin Safe 01.03.2019 [1] Masana tattalin arziki da hada-hadar kudi a Najeriya, sun bada shawarar cewa ya kamata gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, ta bada himma wajen raya tattalin arzikin kasar musamman a yankin arewacinta domin magance matsalolin da ke addabar yankin. Hosts: Muntaqa Ahiwa Nigeria: Cikin shirin za'a ji yadda masana suka soma baiwa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, shawara kan buƙatar zaburar da harkokin tattalin arziƙi, musamman ma na arewacin ƙasar da ke fama da ...

Mar 01, 20191 min

ParsToday Hausa 1 (Thu Feb 14th 2019)

ParsToday Hausa 1 (Thu Feb 14th 2019) [1] [2] Hosts: Abdullahi Salihu* Nigeria Elections 2019: Wasu daga cikin jami'an gwamnatin APC a Najeriya sun nuna ɓacin ransu matuƙa dangane da yadda ƙungiyoyi na dattijan arewa da ma wasu daga ɓangaren kudancin ƙasar suka nuna goyan bayansu ga ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyar adawa ta PDP, wato Alhaji Atiku Abubakar. Ethiopia: Za mu duba yadda masana suke kallon kawo ƙarshen taron shugabannin ƙasashen Afrika, wanda aka gudanar a birnin Adis Ababa n...

Feb 14, 20193 min

BBC Hausa Shirin Rana (Thu Feb 14th 2019)

BBC Hausa Shirin Rana (Thu Feb 14th 2019) [1] [2] Hosts: Sulaiman Ibrahim Katsina Nigeria Elections 2019: A yau ne a Najeriya aka shirya soma rarraba kayan aiki don zaɓen shugaban ƙasa da ke tafe ranar Asabar. Suma masu sa ido, sun buɗe sansaninsu a yau. Wani kuma, wanda da alama ya fi kowa niyar zaɓen, tun jiya ya isa rumfar zaɓen. Inda yake shirin yin kwanaki uku yana jira kafin a soma kaɗa ƙuri'a. "Tun jiya, ƙarfe goma sha ɗaya da rabi (11:30) na bar gida na. Na tattara kayana, na zo na zauna...

Feb 14, 20191 min

BBC Hausa Shirin Hantsi (Thu Feb 14th 2019)

BBC Hausa Shirin Hantsi (Thu Feb 14th 2019) [1] [2] Hosts: Badriya Tijjani Kalarawi Liberia: In gano gawar mutane biyar amma a mahaƙar ma'adinai ta gwal wadda ta rifta a arewacin Liberia a makon da ya wuce. USA, Yemen: 'Yan majalisar Amurka sun gabatar da uzurin da zai janyowa dakarun ƙasar su janye daga Yemen. Nigeria Elections 2019: Yayin da ya rage kwanaki biyu a gudanar da zaɓe a Najeriya, masu larura ta musamman na ƙorafi kan jami'an tsaro a rumfunan zaɓe. "Dubu biyu da sha biyar (2015), na...

Feb 14, 20191 min

BBC Hausa Shirin Safe (Thu Feb 14th 2019)

BBC Hausa Shirin Safe (Thu Feb 14th 2019) [1] [2] Hosts: Badriya Tijjani Kalarawi Nigeria: A Najeriya, an kai wa waɗansu tagwayen hare-hare kan ayarin gwamnan jihar Borno a lokacin yaƙin neman zaɓe a garin Gamboru . Nigeria Elections 2019: Jam'iyar PDP ta zargi gwamnatin APC da yi mata kwitingila na hana ta yin filin yin taro a Abuja: "Gashi bayan mun yi gangamin mutane, daga ko'ina sun taho, har da masu hawan jakuna da dawakai. Da muka je, muka tarar an sa kwaɗo, an hana." Sai dai kuma, ana ta ...

Feb 14, 20191 min

VOA Hausa Shirin Hantsi (Thu Feb 14th 2019)

VOA Hausa Shirin Hantsi (Thu Feb 14th 2019) [1] [2] Hosts: Muhammad Hafiz Baballe, Ibrahim Ka-Almasih Garba. Nigeria: Ministan tsaron Najeriya, Janar Mansur Dan Ali mai ritaya, ya ƙaryata jita-jita da ake yi na cewa jami'an ƙasar basu da kayan aiki. "Ko ƙasar America, ko ƙasar Ingila (England), ko ƙasar Russia, ba za su ce suna da isasshun kaya da suka ishe su ba. Muƙaddashin shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya, wato EFCC, Ibrahim Mago , ya ce za su gurfanar da masu siyan d...

Feb 14, 20191 min

VOA Hausa Shirin Safe (Thu Feb 14th 2019)

VOA Hausa Shirin Safe (Thu Feb 14th 2019) [1] [2] Hosts: Muhammad Hafiz Baballe, Ibrahim Ka-Almasih Garba. USA, Iran: Amurka tana tuhumar wata tsohuwar jami'ar sojan samanta wadda ta canja sheƙa zuwa ɓangaren Iran da yin mata leƙan asiri. USA: Shugaban Amurka Donald Trump ya ce har yanzu bai tsaida shawarar rattaba hannu ko a'a kan ƙudurin bai ɗaya da jam'iyyu suka cimma ba wanda ya tanadi kuɗin gina katanga. USA: Majalisar wakilan Amurka mai rinjayin 'yan Democrats, ta kaɗa kuri'ar rage tallafi...

Feb 14, 20192 min

DW Hausa Shirin Safe (Wed Feb 13th 2019)

DW Hausa Shirin Safe (Wed Feb 13th 2019) [1] [2] Cikin shirin za a ji yadda wasu al'umomi ke bayyana muhimmancin kafar sadarwar rediyo a rayuwarsu ta yau da kullum, dai lokacin da ake ranar rediyo ta duniya. A Najeriya kuwa mazauna yankunan karkara ne ke damuwa da yawan alkawura da 'yan siyasa ke dauka ba tare da cikawa ba. Host: Munta Gayuwa* Nigeria: Za mu ji yadda mazauna yankunan karkara a Najeria suke cewa suna cikin halin taƙaici na roman baka da 'yan siyasar ƙasar ke yi musu, tsawon sheka...

Feb 13, 20192 min

BBC Hausa Shirin Hantsi (Wed Feb 13th 2019)

BBC Hausa Shirin Hantsi (Wed Feb 13th 2019) [1] [2] Hosts: Badriya Tijjani Kalarawi South Korea: Hukumomin Koriya ta Kudu, sun musunta iƙirarin shugaba Trump kan ƙara yawan kuɗaɗen da take baiwa sojin Amurka a ƙasar ta. Sudan: Jami'an tsaro sun cafke wasu daga cikin farfesoshin jami'o'i a birnin Khartoum. Nigeria: Kwanaki uku kafin a yi zaɓen shugaban ƙasa, matasa da suka fito takaran muƙamai sun ce salon mulkin su zai banbanta da na 'yan baya. "Almazaranci da kuɗin mutane, da rashin tsaro da ya...

Feb 13, 20191 min

BBC Hausa Shirin Safe (Wed Feb 13th 2019 - 6:30am NGT)

BBC Hausa Shirin Safe (Wed Feb 13th 2019 - 6:30am NGT) [1] [2] Hosts: Badriya Tijjani Kalarawi Venezuela: Shugaban 'Yan adawa a Venezuela, ya sha alwashin shigar da kayan agaji. Duk kuwa da cewa shugaba Maduro ya ƙi amincewa da hakan. Nigeria: Ana cigaba da cece-kuce kan shugaba Muhammadu Buhari a jihar Zamfara. Da ake cewa hakan zai iya haddasa fitina. Toh sai dai kuma magoya bayanshi sun ce an yi masa mummunar fahimta. Shin kuma ko wace rawa ce rediyo ke takawa a rayuwar al'umma? Muna ɗauke da...

Feb 13, 20191 min

BBC Hausa Shirin Yamma (Tue Feb 12th 2019 - 8:30pm NGT)

BBC Hausa Shirin Yamma (Tue Feb 12th 2019 - 8:30pm NGT) [1] [2] Hosts: Aminu Abdulkadir Sudan: Jami'an tsaron ƙasar Sudan sun tsare wani rukunnin shegunnan malamai na jami'o'i. Da suka yi zanga-zangar ƙin jinin shugaba Umar Al-Bashir a Khartoom - babban birnin ƙasar. Nigeria: Rundunar 'yan sanda ta ce ta kama wasu mutane dangane da gobarar da tashi a wani ofishin hukumar zaɓe, yau a jihar Anambara. Gobarar ta haddasa ɓarna. "Toh, har yanzu dai ba mu kai ga tantance yawan adadin wannan na'uran, k...

Feb 13, 20192 min

BBC Hausa Shirin Hantsi (Tue Feb 12th 2019 - 7:30am NG)

BBC Hausa Shirin Hantsi (Tue Feb 12th 2019 - 7:30am NG) [1] [2] Hosts: Badriya Tijjani Kalarawi India: 'Yan sanda Indiya sun ce mutane sha bakwai ne suka mutu, sakamakon wata gobara da ta tashi a wani otel da ke birnin Delhi. Haiti: Masu zanga-zanga sun yi ta ƙona tayoyi a titunan ƙasar Haite tare da jefan jami'an tsaro da duwatsu. Nigeria: Wasu 'yan Najeriya sun ce sun gaji da alƙawarin da gwamnati ke musu na bunƙasa harkar sufurin jirgin ƙasa a sassan ƙasar. "Muna jin daɗin yanda aikin kasance...

Feb 12, 20191 min

Kanun Labaran BBC Hausa Shirin Safe (Tue Feb 12th 2019 - 6:30am NG)

BBC Hausa Shirin Safe (Tue Feb 12th 2019 - 6:30am NG) [1] [2] Hosts : Badriya Tijjani Kalarawi USA: 'Yan jam'iyyun Democrat da Republican, sun cimmawa matsayar kaucewa sake dakatar da ayyukan gwamnati a Amurka. Nigeria: Ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyar PDP, ya ce rashin kayan aiki ne ke dawo da hannun agogo baya a yaƙi da ta'addanci a ƙasar. "I beleive our military are not getting the best of equipment... &lt;&gt; Na yi imani sojojin mu basa samun ingantattun kayan yaƙi. Wasu lokuta ma, za k...

Feb 12, 20192 min

DW Hausa Shirin Safe 10.02.2019 Headlines

DW Hausa Shirin Safe 10.02.2019 [Cikakken Shirin / Full broadcast] Za ku ji cewar kasar Turkiya tayi Allah wadai da irin cin zarafin da kabilar Uighur ke fuskanta a kasar Chaina Host: Zulaiha Abubakar Kibiya African Union : Ƙungiyar tarayyar Afika ta AU, za ta gudanar da babban taron ta na kwanaki biyu a birnin Adis Ababa na ƙasar Habasha (Ethiopia) inda shugwabannin ƙasashen Afrika za su tattauna batun kwararar baƙin haure daga nahiyar zuwa ƙasashen turai. Daidai lokacin da a cigaba da lalubo d...

Feb 10, 20191 min

BBC Hausa Shirin Hantsi 10/02/2019

BBC Hausa Shirin Hantsi 10/02/2019 [14] Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya. Hosts: Umaymah Sani Abdulmumin Turkey, China: Turkiyya ta buƙaci ƙasar Sin da ta gaggauta ta rufe sansanonin da take tsare musulmi 'yan ƙabilar Uyghur. UK: Yarima Philip na Birtaniya ya ajiye lasisinsa na tuƙi. Nigeria's corn farmers: Manoma masara sun bayyana irin yabon da suka ce sun samu a noman bara. Mun samu cigaba wajen bunƙasuwan masara daga shekara ta dubu biyar da...

Feb 10, 20191 min

BBC Hausa Shirin Safe 10/02/2019

BBC Hausa Shirin Safe 10/02/2019 [12] Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya. Hosts: Umaymah Sani Abdulmumin Nigeria Elections 2019 / Zaɓe 2019: APC! APC! Today I want to teach Atiku a lesson. --Uban jam'iyyar APC Bola Ahmed Tunibu a yayin yaƙin neman zaɓen jihar Lagos ya ke cewa yau zan koyawa Atiku darasi. Za mu ji me yayi zafi da kuma yadda yaƙin neman zaɓen ya kasance. Sokoto Governor Debate: A yau BBC ke cika alƙawarinta na kawo muku mahawara tsa...

Feb 10, 20191 min

BBC Hausa Shirin Yamma 09/02/2019

BBC Hausa Shirin Yamma 09/02/2019 [10] [11] Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya. Hosts: Ibrahim Mijinyawa Nigeria Elections 2019: Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP (the major opposition party), ta yi zargin cewa an hana ta gudanar da gangamin yaƙin neman zaɓe a Abuja. Har mun tura mutanen mu waɗanda za su je su shiya mana wurin tsayawa a yi magana ( podium )... sai aka ce musu wannan wuri ba za a ba mu shi ba. Don haka sai dai mu nemi wani. Chad: Run...

Feb 10, 20191 min
For the best experience, listen in Metacast app for iOS or Android