Dandalin Fasahar Fina-finai - podcast cover

Dandalin Fasahar Fina-finai

RFI Hausawww.rfi.fr
Fili ne na musamman kan Fina-finai ta hanyar tattauna da masu ruwa da tsaki a wannan fanni a duniya, Tare da wayar wa ma su sauraro kai da kara masu basira dangane da hikimar da Allah ya  bai wa wasu ta fanin shirya fim ko tsara wasan kwaikwayo. Wanda ke zo maku a duk ranar Asabar da safe, tare da maimaici a ranar Lahadi da yamma.

Episodes

Korafe-korafen makallata fina-finan Hausa

A cikin shirin na wannan mako, zamu sake yin waiwaye kan korafe-korafen makallata fina-finan Hausa, kan yadda mashirya fina-finai suka fi mayar da hankali kan soyayya, tare da fatali da sauran fannonin rayuwa. Za mu tsallaka Jamhuriyar Nijar, inda zamu duba yadda zamani yayi tafiyar ruwa da wake-waken ‘yan mata da ke tashe a baya. Muna tafe da tattaunawa da Hadiza Gire, guda daga cikin matan da suka yi tashe a jamhuriyar Nijar lokacin da suke fagen rera wakokin ‘yan mata.

Jul 13, 202420 min

Ko ana 'kan ta waye' a masana'antar Kannywood?

Shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' ya yi nazari ne a kan al'amarin nan da ake kira 'kan-ta-waye'. Shirin ya yi bayani a kan menene 'kan-ta-waye', sannan ya tattauna da baki, wadanda suka fadada bayanin don fahimtar mai sauraro.

Feb 06, 202220 min

Halin da masana'antar Fim ta shiga a makon da ya kare

Kamar yadda aka saba kowane mako shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai tare da Hauwa Kabeer ya tattauna akan wasu daga cikin muhimman al'amuran da ke wakana a masana'antar fina-fina da ke arewaci da kuma kudancin Najeriya.

Jan 09, 202220 min

An kamala zaben wakilan kungiyar yan Fim a jihar Kaduna

A cikin shirin duniyar fina-finai,Hawa Kabir ta samu tattaunawa da masu ruwa da tsaki a harakar fim yan lokuta bayan kamala zaben wakilan MOPAN a jihar Kaduna. Makomar duniyar Fim,hanyoyin kawo karshen baraka a wannan duniya na daga cikin manyan batutuwa da Hawa ta samu tattaunawa da bakin na ta.

Dec 12, 202120 min

An fara daukar shirin 'Gidan Badamasi' zango na 4

Shirin 'Dandalin Fasahar Fina Finai ya leka inda ake daukar shirin barkwancin nan mai dogon zango, wato 'Gidan Badamasi', inda ya gana da jarumai da masu ruwa da tsaki a shirin, cikin su har da babban daraktan shirin, Falalu Dorayi.

Nov 21, 202120 min

Rayuwar Alhaji Umaru Danjuma Katsina da aka fi sani da Kasagi

Kasagi wanda ya rubuta fitaccen littafin da aka yi wa suna ‘Kulba na Barna’ ya rasu ne sakamakon gajeruwar rashin rashin lafiya. Danjuma Katsina na daya daga cikin fitattun masu wasan kwaikwayon da suka yi suna daga shekarar 1980 tare da wasu abokan aikin sa a lokacin irin su Kasimu Yero da Tumbuleke da Malam Mamman da karkuzu Na Bodara da kuma Samanja Mazan Fama. Hawa Kabir a cikin shirin dandalin fasahar fina-fanai ta jiyo ta bakin wasu daga cikin mutanen Danjuma Katsina wanda ke daya daga cik...

Nov 07, 202120 min

Taron kara wa juna sani kan habaka harshen Hausa 2/2

Shirin 'Dandalin Fasahar Fina Finai tare da Hauwa Kabir ya cigaba da tattaunawa ne kan taron kara wa juna sani kan habaka harshen Hausa na kungiyar WTC da ya gudana a garin Zaria, dake jihar Kaduna.

Oct 24, 202120 min

Taron kara wa juna sani kan habaka harshen Hausa

A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina Finai, hauwa Kabir ta leka taron kara wa juna sani kan habaka harshen Hausa na kungiyar WTC da ya gudana a Zaria, jihar Kaduna. Shirin ya gana da shehunan malaman da suka halarci taron.

Oct 03, 202120 min

Rayuwar yan wasan fina-finai a Tarrayar Najeriya

A cikin shirin dandalin Fina-finai,Hawa Kabir ta jiyo ta bakin masu shirya fim a Nollywood,wanda suka kuma yi mata bayyana dangane da rayuwar su da kuma irin wasannin da suke iya kasancewa a cikin su ga baki daya.

Sep 26, 202120 min

Ta'aziyyar mawakin siyasa Isyaku Forest

Shirin 'Dandalin Fasahar Fina Finai' na wannan mako tare da Hauwa Kabir ya kawo mana ta'aziyyar mawakin siyasan nan, Isyaku Forest, wanda ya rasu kwanan nan. Hauwa Kabir ta tattauna da makusanta da aminansa, ciki har da shahararren mawakin siyasa, Rarara.

Sep 12, 202120 min

Mutane na yi wa fim kallon hadarin kaji don ba su ke yi ba - Isa Bello Ja

A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' Hauwa kabir ta kawo abubuwa da dama a bangaren fina-finai, inda ta duba yadda yanzu masana'antar Kannywood ke gogayya da takwararta tav kudancin Najeriya. Ta kuma tattauna da shugaban jaruman Kannywood, Alhassan Kwale wanda ya ce Umma Shehu da Sadiya Haruna ba 'yan Kannywood bane.

Aug 29, 202121 min

Ana shirin ci gaban fim din Hausa na 'Malam Zalimu'

A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' Hauwa Kabir ta duba tattauna da Ado Ahmed Gidan Dabino a game da ci gaban shirin fim din Malam Zalimu. Bayan nan ta leka Nollywood ta kudancin Najeriya, inda ta kawo ta'aziyar rasuwar shahararren mawaki, Sound Sultan.

Jul 25, 202120 min

Masu shirya Fina finan Hausa sun koma cin moriyar Youtube

A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' Hauwa Kabir ta yi dubi da batun kasuwanci a masana'antar Kannywood, tare da duba yadda masu shirya fim din suka koma intanet, ta wajen cin moriyar dandalin Youtube, inda suke dora ayyukansu a kai.

Jul 18, 202120 min

Dandalin Fasahar Fina-Finai: Ta'aziyyar jaruma Zainab Booth

A cikin shirin 'Dandalin Fasahar Fina-Finai' na wannan makon, Hauwa Kabir ta kawo ta'aziyyar jarumar Kannywood da Allah ya wa rasuwa a makon da ya gabata,inda ta tattauna da abokan aikinta na Kannywood. Shirin ya kuma leka Nollywood da Bollywood.

Jul 11, 202120 min
For the best experience, listen in Metacast app for iOS or Android
Open in Metacast