Korafe-korafen makallata fina-finan Hausa
Jul 13, 2024•20 min
Episode description
A cikin shirin na wannan mako, zamu sake yin waiwaye kan korafe-korafen makallata fina-finan Hausa, kan yadda mashirya fina-finai suka fi mayar da hankali kan soyayya, tare da fatali da sauran fannonin rayuwa.
Za mu tsallaka Jamhuriyar Nijar, inda zamu duba yadda zamani yayi tafiyar ruwa da wake-waken ‘yan mata da ke tashe a baya.
Muna tafe da tattaunawa da Hadiza Gire, guda daga cikin matan da suka yi tashe a jamhuriyar Nijar lokacin da suke fagen rera wakokin ‘yan mata.
For the best experience, listen in Metacast app for iOS or Android
Open in Metacast