Don't just listen to podcasts. Learn from them with transcripts, summaries, and chapters for every episode. Skim, search, and bookmark insights. Learn more
Mata da dama a duniya ba su samun damar tsaftace kansu ko ma samun audugar mata yayin jinin al'ada na wata-wata. Za a ji yadda Maryam Muhammad da ke jihar Kano a Najeriya ta baiyana mana dalilin da ya sa ta fara dinka audugar mata.
Shirin ya tattauna da Fatima Fuad Hashim mai shafin @opendiariesng kan ayyukan da kungiyarta ke yi na horas da mata sana'o'in hannu don dogaro da kansu da kuma ayyukan samar da rijiyoyi a wasu kauyukan da ke da karancin ruwan sha a arewacin Najeriya.
Wannan kashin ya yi nazari kan matsayin mace da irin rawar da mata ke takawa da kuma gudunmawarsu cikin al'umma. Shirin ya tattauna da Hajiya Khadija Sa'ad, shugabar kungiyar Babbar Mace da ke jihar Kaduna a Najeriya, kana Zinatu Musa ta baiyana mana irin rawar da take takawa a matsayinta ta uwa.