A duk lokacin da akace an kammala zangon karatu, dalibai kan samu hutu don hutawa da yin wadansu abu na dabam da kuma basu damar shakuwa da ‘yan uwa da abokan arziki. Kamar yadda masana harkar masana harkar ilimi suka saba fadi, yawan karatu kan taho da nashi irin matsalolin, ya kuma kamata ace ana warewa dalibai wasu lokuta na musamman don samun hutu daga karatun da suka koya. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan abubuwan da ya kamata yara su ringa yi yayin hutun makaranta....
Jul 23, 2025•29 min
Masana da masu sharhi suna ganin cewa rasuwar shugaba Muhammadu Buhari ta haifar da babban gibi a siyasar Najeriya, musamman a Arewa. Wasu ma suna ganin rasuwar Buhari ka iya kawo tasgaro ga jamiyya mai Mulki, wadda take ganin shi danta ne, da ma sabuwar hadakar ’yan adawa, wadanda suke ganin yana tare da su. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne a kan yadda siyasar Najeriya za ta kasance bayan rasuwar tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari....
Jul 16, 2025•24 min
Mai yiwuwa masu sauraro sun san wani bawan Allah wanda kusan a kullum, kuksan a ko yaushe a cikin nema yake, amma Allah bai kawo ba.. Wasu dai na ganin yawan fadi-tashin da mutum yakan yi ba shi ne zai ba shi kudaden da yake bukata ba, yayin da wasu suke ganin jajircewar mutum tana da nasaba da yawan abin da zai samu. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan kujiba-kujibar da mutane suke yi don samun arziki da tambayar ko zafin nema yana kawo samu?
Jul 09, 2025•19 min
Burodi ya zama daya daga cikin abincin da ‘yan Najeriya basa iya yi babu shi. Yayin da wasu ke cin shi a matsayin abin Karin kumallo da safe, wasu kuwa na cin shi a matsayin abincin rana a wasu lokutan ma har da na dare. A duk lokacin da aka ce masu sarrafa burodi sun shiga yajin aiki, ko fulawa tayi karanci hakan kan haifar da raguwar burodi a kasuwa wadda kan jefa masu cin shi a cikin mawuyacin hali. Shirin Najeriya A Yau na wannan makon zai yi nazari ne kan sinadaran da ake amfani da su wajen...
Jul 02, 2025•29 min
Hare haren ‘yan ta’adda na kara ta’azzara a yankuna daban daban na fadin kasar nan wanda hakan ke nuni da Karin rashin tsaro da ya dade yana ciwa alumma da ma gwamnati tuwo a kwarya. Ko a kwana kwanan nan an ga yadda jihar filato tayi ta fama da irin wadannan hare hare da kuma hare haren ramuwar gayya. Wani kididdiga kungiyar dake tattara bayanan hare haren ta’addanci ta fitar ya nuna cewa Najeriya ta taso daga mataki na 8 zuwa na 6 a batun ta’addanci a duniya. Kazalika a kwanakin nan wani hari ...
Jun 18, 2025•29 min
An ayyana 12 ga watan Yunin kowace shekara a matsayin Ranar Dimokuradiyya a Najeriya don tunawa da ranar da aka gudanar da zaben da aka yi amanna cewa shi ne mafi sahihanci da inganci a tarihi. Sai dai bayan fiye da shekara 30 da wannan zabe da fafutukar da ta biyo baya, wasu masana suna ganin har yanzu kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba. Ko mece ce hujjarsu? Wannan ne batun da shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari a kai.
Jun 12, 2025•28 min
Asibiti ko dakin shan magani ko wani bigire mai kama da wadannan wuri ne da marasa lafiya kan je ko ake kai su don neman waraka a duk lokacin da bukatar haka ta taso. Wuri ne da akan ware domin ceto rayukan wadanda suka jikkata suke kuma bukatar agajin gaggawa. A bisa al’ada kuma, ana sa ran samun tausayi da jinkai da sadaukarwa wajen yin dukkan mai yiwuwa kuma a ko wane lokaci don ceton rayuka daga jami’an lafiya. Sai dai ’yan Najeriya da dama sun dade suna kokawa da yadda a cewarsu wasu jami’a...
Jun 11, 2025•26 min
Yayin da sallah ya gabato, mutane da dama kan yi fadi tashi don biyan wasu bukatun su na bukukuwan sallah, kuma kamar yadda aka saba, a irin wannan lokaci ne iyalai da dama kan maida hankulan su don ganin sun biya wasu daga cikin bukatun su musamman wadanda suka jibanci bikin sallah. Siyayyan kayan kayan abinci na daya daga cikin wadannan hidindimu, sai dai kayan miya da suka zama dole ayi amfani dasu yayin bikin sallah sun yi tashin gwauron zabo inda alumma da dama ke ta bayyana damuwar su kan ...
Jun 04, 2025•26 min
Rashin iya siyan audugar Alada ga mata na kara jefa su cikin matsaloli da dama, a wasu lokuta ma har da cututtuka da ka iya jawo musu matsaloli. A cewar wani rahoto da Asusun yara na majalisar dinkin duniya UNICEF da WaterAid na shekarar 2021 suka fitar, yace daya daga cikin kowace ‘yan mata goma a ƙasashen Afrika ta Kudu da Sahara na rasa zuwa makaranta lokacin da take jinin al’ada, saboda rashin kayan tsafta, ruwa da kuma tsaftatattun ban daki. Irin wannan matsala na addaban mata marasa galihu...
May 28, 2025•24 min
Dangantaka na kara runcabewa tsakanin Hukumar Tace Fina-finai ta jihar Kano, wato Kano State Censorship Board, hukumar da aka kafa a shekarar 2001 domin kula da tsaftar fina-finai da nishaɗi a jihar, musamman a fannin kiyaye al’ada da koyarwar addini wacce daya daga cikin jaruman fina finan Abba El-Mustapha, ke jagoranta. A baya-bayan nan, hukumar ta fitar da sanarwa inda ta dakatar da fina-finai masu dogon zango guda 22. Wannan mataki ya biyo bayan saɓani tsakanin hukumar da wasu masu shirya fi...
May 21, 2025•27 min
Karba-karba wani tsari ne da ya tanadi kewayarwar ludayi a tsakanin kudanci da arewacin Najeriya wajen rike shugabancin kasa. Manufar tsarin, wanda babu shi a Kundin Dokokin Najeriya, ita ce tabbatar da daidaito da haɗin kai da zaman lafiya a ƙasa. Sai dai yunkurin samar wa tsarin mazauni a ta yadda shugabanci zai rika kewaya a tsakanin shiyyoyi shida na kasar nan bai samu shiga ba a Majalisar Wakilai. Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi duba ne a kan wannan tsari na karba-karba da tasirins...
May 14, 2025•27 min
Duk shekara, dalibai kan rubuta jarabawa a matakai daban-daban na makarantu daban-daban. Daya daga cikin nau’ukan jarabawa da daliban Najeriya suke yi ita ce Jarabawar Sharen Fagen Shiga Manyan Makarantu, wato UTME. Kamar kowace shekara, a bana ma dalibai sun rubuta wannan jarabawa kuma a cewar Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB), kashi 78.5 cikin 100 na wadanda suka rubuta jarabawar sun samu kasa da maki 200. Ko wadanne dalilai ne suke kawo faduwa jarabawa a Najeriya? Wannan ...
May 07, 2025•23 min
Tatsuniya wata hanya ce ta ilmantarwa da bayar da tarbiyya da kuma koyar da al’adu da halaye na gari a tsakanin Hausawa. Tatsuniyoyi na ɗauke da darussa na rayuwa, suna kuma koya wa yara da manya jarumta da tausayi da sauran dabi’u kyawawa. Sai dai a yayin da duniya take sauyawa, ba kasafai matasa suke sha’awar sauraron tatsuniya ba. Wannan ne batun da shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari a kai.
Apr 30, 2025•31 min
Wutar lantarki ta zama tamkar gwal a wasu sassan Arewacin Najeriya, inda a wasu yankuna aka ba da rahoton samun sa’o’i biyu kawai a rana, wasu kuma ba sa samun ko daidai da dakika daya. Masu kananan sana’o’i suna kallon rayuwarsu da kasuwancinsu suna durkushewa yayin da kayan sana’arsu suke lalacewa saboda rashin wuta. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne a kan wannan matsala da yadda take taba rayuwar al’umma da hanyoyin magance ta.
Apr 23, 2025•26 min
Duk wanda aka haifa ya tashi a kasar Hausa ya san al’adar nan ta bayar da ko karɓo ɗa ko ‘ya riƙo. A wasu lokutan mutum ne ke nema a ba shi rikon, a wasu lokuta kuma iyayen ne suke bayarwa don ƙashin kansu. Wannan alada ana yin ta ne da zimmar yauƙaƙa danƙon zumunci, amma a wasu lokuta kwalliya ba ta biyan kuɗin sabulu. Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne kan matsalar ’ya’ya da iyayen riko.
Apr 16, 2025•23 min
Tun kaka da kakanni an san Hausawa da kawaici da kunya da kuma girmama na gaba da su. Mai yiwuwa wadannan dabi’u ne suka sa matar Bahaushe ba ta iya hada ido da mijinta, balle ta kira shi da sunansa na yanka. To amma a zamanin yau ba abin mamaki ba ne a samu matar aure ta kalli kwayar idon mijinta, ta kuma kira shi da sunansa na yanka. A kan wannan al’ada – asalinta da alfanunta da dalilan sauyawarta – shirin Daga Laraba na wannan makon za iyi nazari.
Apr 09, 2025•24 min
Tun bayan kisan mafarauta 16 dake hanyar su ta dawowa gida a garin Uromi dake karamar hukumar Esan dake jihar Edo ne dai al’umma da dama ke ta aikewa da sakon alhini ga ‘yan uwa da abokan arziki yayin da wasu kuma ke ta neman amsoshin tambayoyi game da lamarin da ya shige musu duhu. A yayin da wasu ke ganin a matsayin su na ‘yan kasa masu cikakken ‘yanci, suna da damar kutsawa lungu da saƙo na ko ina a fadin kasar nan, wasu kuwa tambaya suke shin me ya kai ‘yan Arewa har kudancin kasar nan don y...
Apr 02, 2025•30 min
A duk lokacin da aka ce lokutan bukukuwa sun karato, akan samu sauyi a dukkan alamura. Daya daga cikin irin wadannan sauyi da ake samu shine na farashin kayayyakin masarufi. A wasu lokuta, akan samu tashin farashin irin wadannan kayayyaki, a wasu lokutan kuma akasin haka. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai tattauna ne kan farashin kayayyakin masarufi gabanin bikin sallah.
Mar 26, 2025•27 min
A karshe dai hasashen da wasu ke yi a Ribas ya tabbata, inda Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya ayyana dokar ta-baci, ya dakatar da zababben gwamnan da mataimakiyarsa, da ma ''yan majalisar dokokin jihar. Sai dai bayan ayyana wannan doka da shugaban kasar ya yi 'yan Najeriya da dama suna ta bayyana ra’ayoyinsu kan wannan lamari. Yayin da wasu suke cewa tuni ya kamata Shugaban Kasar ya dauki wannan mataki, wasu kuwa cewa suke yi ba shi da hurumin dakatar da zababben gwamna. Shirin Daga Laraba na ...
Mar 19, 2025•27 min
Bayan dunbum falala, da yawan samuwar ibadun dake kara kusanta bayi ga ubangijin su, da azumin watan ramadana ke zuwa dashi kamar yadda malamai suka saba fada mana, Hakazalika Kuma a watan na Ramadan dai na zuwa da wata alada mai dimbin tarihi dake debe wa alumma musamman na arewacin Najeriya kewa. Wannan aladar itace ta tashe da ake fara yinta da Zarar watan azumi ya kai kwanaki goma. Maza da mata na gudanar da wannan alada ta hanyar yin shigar kwaikwayo tare da bat da kama, su ringa zagayawa g...
Mar 12, 2025•28 min
Kowane Musulmi da yadda yakan shiga watan Ramadana – wani kan shiga da shiri, wani kuma da shiririta. Sai dai wasu watan kan zo musu da kalubale – ba don sun shirya mishi b aba kuma don sun gaza shiryawa. Wani rukunin wadannan mutane shi ne na zawarawa, wadanda galibi ba su da masu agaza musu. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne a kan rayuwar mata zawarawa musamman a watan Ramadana.
Mar 05, 2025•31 min
A duk lokacin da aka ɗaura aure, wata addu’a da ’yan uwa da abokan arziki kan yi ita ce “Allah Ya kawo ƙazantar ɗaki”. A al’adance, ɗaya daga cikin manyan dalilan yin aure shi ne samun haihuwa. Sai dai a wasu lokuta, wasu mazan kan nuna a fili ba su da muradin hakan. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne kan waɗannan mazan da ba sa son haihuwa da kuma dalilan su.
Feb 26, 2025•23 min
Yanayin tattalin arziki da ma wasu dalilai kan tilasta wa mutane da dama, ciki har da masu karbar albashi a karshen wata, neman wata hanya ta daban dake kawo Karin kudade. Shin mene ne yake kawo hakan, kuma mene ne tasirinsa a kan rayuwar masu buga-bugar da ma al’umma? Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne a kan irin buga-bugar da ’yan Najeriya suke yi don sama wa kansu mafita.
Feb 19, 2025•23 min
Zanen fuska na da dadadden tarihi a Arewacin Najeriya musamman a kasar Hausa. Sai dai wannan dadaddiyar al’ada tana kan hanyar gushewa domin kuwa ba kasafai ake samun wadanda suke yin ta a wannan zamani ba. Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne a kan wannan al’ada da kuma dalilin gushewar ta.
Feb 12, 2025•30 min
A da akan kwashe kwanaki ana bukuwan aure a kasar Hausa, kama daga kamu, zuwa sa lalle, yinin bik da zaman ajo zuwa budar kai da sayen baki. Sai dai wadannan al’adu sannu a hankali suna ta gushewa. Ko mene ne dalilin wannan sauyin? Wannan ne batun da shirin Daga Laraba zai duba a wannan makon.
Feb 05, 2025•30 min
Son haihuwar ‘ya’ya maza fiye da ‘ya’ya mata abu ne da ake samu tun tale-tale a tsakanin alummomi daban-daban. A tsakanin wasu al’ummomin, samun da namiji abin alfahari ne wanda kuma yake nuni da cigaba da dorewar ahali; sai dai ba a cika bai wa haihuwar ‘ya mace irin wannan muhimmancin ba. Ko wadanne dalilai ne suka sa wasu mutane suka fi son samun ‘ya’ya maza a kan ‘ya’ya mata? Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi duba ne a kan dalilan da suka sa mutane suka fi son haihuwar ’ya’ya maza a k...
Jan 29, 2025•30 min
Samun ingattattun malamai a makarantun firamare da sakandare na taka muhimmiyar rawa wajen samar da tubalin ingantaccen kuma nagartaccen ilimi a cikin al’umma. Ɗorewar wannan fafutuka ta samar da ingantaccen ilimi kuma ta dogara ne a kan samun haziƙan matasa da za su maye gurbin malaman da ake da su yanzu. Sai dai a Najeriya, alamu suna nuni da yadda matasa da dama suke gudun aikin koyarwa, musamman a kananan makarantu. Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari a kan dalilan da suka sa hak...
Jan 22, 2025•27 min
Duk wanda aka haifa ya tashi a kasar Hausa ya san al’adar nan ta bayar da ko karɓo ɗa ko 'ya riƙo. A wasu lokutan mutum ne ke nema a ba shi rikon, a wasu lokuta kuma iyayen ne suke bayarwa don ƙashin kansu. Wannan alada ana yin ta ne da zimmar yauƙaƙa danƙon zumunci, amma a wasu lokuta kwalliya ba ta biyan kuɗin sabulu. Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne kan matsalar ’ya’ya da iyayen riko.
Jan 15, 2025•23 min
A tsakanin Hausawa, sunaye masu alaka da harshen Larabci sun kusan maye gurbin na gargajiya irin su Tanko da Talle da Audi da dai sauran su. Sai dai yayin da a da sunayen da Hausawa kan sanya wa ’ya’yansu na Annabawa ko Sahabbai ko mashahuran malaman Muslunci ne, a baya-bayan nan wasu iyaye kan aro wasu kalmomi su rika kiran ’ya’yansu da su. Mene ne dalilin hakan, yaushe kuma daga ina ya samo asali, kuma mene ne tasirinsa a al’adance da ma a addinance? Amsoshin wadannan da ma wasu tambayoyi maka...
Jan 08, 2025•28 min
A da soyayya na kafuwa ne sakamakon gaskiyar mutum, ko nasabarsa, ko tarbiyyarsa ko kuma riko da addininsa. Mace kan so saurayinta ko da kuwa ba shi da ko anini, a wasu lokutan ma ko da wani mai hannu da shuni ya fito takan tubure ta ki shi. Sai dai a wannan zamani mata da dama kan fito fili suna bayyana irin saurayin da suke so, a galibin lokuta mai abin hannu. Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan dalilan matan wannan zamanin na kin auren talaka....
Jan 01, 2025•28 min