Episode description
Yau shirin ya yada zango ne ƙasar Ghana, inda ya mayar da hankali kan matakin gwamnatin ƙasar na bai wa ƴan ƙasashen waje wa'adin ficewa daga kasuwancin zinare.
Ƙasar Ghana ta bai wa ƴan ƙasashen waje da su fice daga harkokinta na kasuwancin zinare a ƙarshen wannan wata na Afirilu a wani mataki na bunƙasa kananan masu hakar zinare na cikin gida da kuma samun ƙudin shiga.
Ƙasar ta yammacin Afirka dake kan gaba a samar da zinare a nahiyar na ƙokarin tsaftace harkokin harƙar zinare ta hanyar daidaita cinikin zinari daga kananan masu hakar ma'adinai.
For the best experience, listen in Metacast app for iOS or Android
Open in Metacast