Ilimi Hasken Rayuwa - podcast cover

Ilimi Hasken Rayuwa

RFI Hausawww.rfi.fr

Wannan Shirin ya shafi Fadakar da al'umma game da ci gaban da aka samu a sha'anin Ilimi a fannoni daban-daban na duniya, tare da nazari kan irin ci gaban da aka samu wajen binciken kimiya da fasaha da ke neman saukakawa Dan’adam wajen tafiyar da rayuwarsa a duniya. Shirin kuma zai yi kokarin jin irin bincike da masana ke yi domin inganta rayuwar Bil’adama. Shirin na zo maku ne, a duk ranar Talata a shirye-shiryenmu na safe, a ku maimata ranar Alhamis.

Download Metacast podcast app
Podcasts are better in Metacast mobile app
Don't just listen to podcasts. Learn from them with transcripts, summaries, and chapters for every episode. Skim, search, and bookmark insights. Learn more

Episodes

Yadda Malaman makarantu suka tsunduma yajin aikin sai baba ta gani a Abujan Najeriya

Shirin na wannan mako ya ba da hankali ne kan bikin ranar yara ta duniya wanda aka saba gudanarwa a ranar 27 ga watan mayun kowacce shekara, a Najeriya yayin da ake bikin wannan rana Malaman Makarantun firamare a Abuja babban birnin ƙasar ne ke shiga watanni na uku da fara yajin aikin sai Baba ta gani, sakamakon rashin fara aiwatar da sabin tsarin mafi ƙarancin albashi na naira dubu 70 kamar yadda ƙungiyarsu ta Malaman makarantu ta bayyana. lamarin da ya ta da yajin aikin gargaɗi a baya kafin su...

May 27, 202510 min

Shirin gwamnatin Najeriya na dawo da tsarin koyarawa da harshen uwa

A wannan makon shirin ya mayar da hankali ne kan, shawarar gwamnatin tarayyar Najeriya ta dawo da tsarin amfani da harshen uwa a makarantun firamare da ke fadin kasar. Tsarin amfani da harshen uwa a makarantun firamare, wani tsari ne da aka gabatar a shekarar 2022, wadda ke da nufin inganta amfani da harsunan uwa a matsayin harshen koyarwa a makarantun firamare. Sai dai, a wancan lokaci da aka kaddamar da manufar za a yi amfani da ita ne akan Yara yan aji daya zuwa na makarantun firamare. Hakan ...

May 13, 202510 min

Ɓangaren ilimin wasu jihohin Najeriya sun gaza samun tallafin gwamnatin ƙasar

Shirin na wannan mako ya duba dalilan da suka sanya bangaren ilimi a matakin farko a Najeriya na matakin jihohi ya gaza samun gajiyar tallafin da zai taimaka wajen bunkasa karatun kananan yara, duk da makudan kudaden da gwamnatin ƙasar ta ware a matsayin tallafi. Bisa ga kididdigar da aka yi a baya-bayan nan, akwai yara fiye da miliyan 10 da ya kamata a ce suna makaranta a Nigeria amma a halin yanzu yawo su ke yi loko-loko ba tare da samun kowani irin nau’in ilimi ba. ‘Yan kalilan din da suke sa...

May 06, 202510 min

Ƙalubalen da suka dabaibaye harshen Hausa ta fuskar magana- Kashi na 2

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan makon ya ɗora ne akan shirin makon jiya sai dai a wannan karon shirin ya karakata ne ga ɓangaren yadda matasa ke sauya wasu kalmomin Hausa ta hanyar yi musu ƙawance da wasu yaruka su bayar da wata kalma da za ta bayar da ma'anar da za a fahimci abin da ake nufi cikin sauƙi. Idan mai sauraro na biye da shirin na Ilimi Hasken Rayuwa a makwannin baya-bayan nan yana ci gaba da bibiyar dokoki ko kuma ladubban rubutu da karatu baya ga magana...

Apr 29, 202510 min

Kalubalen da suka dabaibaye harshen Hausa ta fuskar rubutu - kashi na 2

Shirin na yau, ya ɗora ne akan kashi na farko da muka gabatar a makon jiya, wanda ya yi duba game da yadda harshen Hausa ya bunkasa a lokutan baya, da muhimmacinsa, baya ga matsalolin da yake fuskanta da ma kalubalen da Rubutun Hausa ke fuskanta a kafofin sada zumunta. Masana sun bayyana ka'idojin rubutun Hausa, a matsayin wani yanayi na lura tare da kiyaye ka'idojin harshen Hausa a rubuce domin samun damar isar da sakon da marubuci ke nufi zuwa ga mai karatu daidai ba tare da dungushe ko sauya ...

Apr 22, 202510 min

Ƙalubalen da suka dabibaye harshen Hausa ta fuskar rubutu - Kashi na 1

Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan makon shirin ya sauya salo zuwa mai dogon zango ta yadda zai tattauna da masu ruwa da tsaki a kan bunƙasar harshen Hausa da matsalolin da ya ke fuskanta da dalilan da suka haifar da matsalolin, da dai sauran muhimman batutuwa da suka shafi harshen na Hausa. Harshen Hausa, harshe ne da yake da tsohon tarihi wanda ya shafe ɗaruruwan shekaru ana magana da shi, wanda alƙaluma suka tabbatar da cewar zuwa yanzu miliyoyin mutane ne ke magana ...

Apr 15, 202510 min

Yadda ɗalibai a Bauchi ke watsi da karatu don shiga aikin tonon ma'adinai

Shirin wannan makon zai yi dubi ne akan yadda ɗalibai a jihar Bauchi ke yin watsi da karatu don shiga aikin tonon ma'adinai. Jihar Bauchi, ta yi ƙaurin suna a baya a matsayin wadda ke sahun gaba wajen yawan yaran da suka yi watsi da makarantunsu tare da rungumar harkar tonon ma’adinai don samun dogaro da kai. Dalili ke nan da fiye da rabin daliban wasu makarantun firamare a jihar, suka bar zuwa makaranta inda suka karkatar da hankali kan harka haƙon ma’adanan.

Apr 01, 202510 min

Gwamnatin Jigawa ta ƙaddamar da shirin ɗaukar nauyin karatun ƴaƴa mata zuwa PHD

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya maida hankali ne kan shirin da gwamnatin jihar Jigawa ta ƙaddamar, na ɗaukar nauyin karatun ‘ya’ya mata daga Firamaren har zuwa karatun Digirin Digirgir, shirin da ta ce tana fatan zai zaburar da ƙarin mata da iyayensu wajen duƙufa neman ilimi, ba tare da fargabar fuskantar ƙalubale na rashin ƙarfi ta fuskar tattalin arziƙi ba. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare Nura Ado Suleiman.........

Mar 25, 20259 min

Gwamnatin Ghana na nazarin yiwuwar fara bayar da ilimin Sakandire kyauta

Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan mako ya mayar da hankali kan shirin gwamnatin Ghana na fara bayar da ilimin Sakandire kyauta, kodayake an faro da sauraren ra'ayin jama'a kan wannan shiri wanda ma'aikatar ilimin ƙasar ta bijiro da shi. Bayanai sun ce baya ga bayar da ilimin kyauta, tsarin zai kuma kawo gyara a yanayin bayar da ilimi musamman a manyan makarantun ƙasar ta Ghana. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.........

Mar 04, 202510 min

Yadda matasa a Najeriya suka ƙirƙiri injin da ke tsince tsakuwa daga Shinkafa

A wannan makon, shirin Ilimi hasken rayuwa tare da Aisha Shehu Kabara ya mayar da hankali kan yadda wasu matasa suka ƙirƙiri wani nau'in inji da ke cire tsakuwa daga jikin shinkafa, wanda zai taimaka matuƙa wajen samar da tsaftatacciyar shinkafa. Kafin wannan hoɓɓosa daga matasan, akan shigo da irin injinan ne daga ƙasashe irin China don sauƙaƙawa Manoma. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin.

Feb 25, 202510 min

Gwamnatin Najeriya ta ɗaga likafar Kwalejin Kimiyyan Lafiya ta Tsafe zuwa Jami'a

Shirin “Ilimi Hasken Rayuwa” namu na wannan mako, ya yada zango ne a tarayyar Najeriya, inda shugaban ƙasar Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan ƙudurin samar da sabuwar jami’a kimiyyan lafiya da fasaha ta tarayya wato Federal University of Health Science and Technology a garin Tsafe na Jihar Zamfara, bayan tsallake dukkan matakan majalisa dokokin ƙasar. Wannan saka nannu na shugaban ƙasar ya yi zai bada damar ƙara inganta harkan kiwon lafiya ta hanyar samar da kwararru. Ku latsa alamar sauti ...

Feb 18, 202510 min

Matsin rayuwa na barazanar gurgunta karatun ƙananan yara a Najeriya

Shirin ''Ilimi Hasken Rayuwa'' tare da Nura Ado Suleiman a wannan makon, ya mayar da hankali ne kan yadda halin matsin rayuwa ke yin tasiri a kan karatun yara ƙanana lamarin da ya sa kaso mai yawa daga cikinsu ba sa samun cikakkiyar fahimta a kan darussan da ake koya musu, saboda dalilai da dama masu alaka da matsin rayuwar. Baya ga batun ci a koshi dai, yanyayin da yara ƙanana ke tafiya makarantunsu a yanayin da ake ciki ma lamari ne da ya kamata a mayar da hankali akai, la’akari da cewar a was...

Feb 11, 202510 min

Gasar HIFEST karo na bakwai a Najeriya

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan mako, ya yi duba ne, kan yadda wata kungiya a Najeriya, ke karfafa gwiwar daliban sakandire kan yadda za su bayyana baiwar da suke da ita, musamman a bangaren ilimin fasaha.

Jan 28, 202510 min

Mahimmancin kwalejojin fasaha a Najeriya wajen bunƙasar ɓangaren ilimin kimiyya

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa a wannan makon ya yi nazari ne kan mahimmancin kwalejojin fasaha na Najeriya ga bunƙasar ɓangaren ilimin kimiyya da fasaha a ƙasar, da kuma kalubalen da suke fuskanta a halin yanzu, sai kuma duba hanyoyin da za a bi don farfaɗo da martabarsu. Ku latsa almar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Nura Ado Suleiman............

Dec 24, 202410 min

Tasirin da salon koyarwa ke da shi wajen baiwa ɗalibai ingantatcen ilimi

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa a wannan mako, ya tattauna ne a kan salon koyarwa tun daga matakin makarantu na ƙasa wato ‘Method of Teaching’ a turance, da tasirin da wannan salo ke da shi kan bayar da ilimi. Salo ko kuma dabarun koyarwa matakai ne ko tsarin da malamai ke amfani da su wajen koyar da ɗalibai darussa, a kuma tabbatar da cewa ɗaliban sun fahimci darasin da ake yi musu. A mafi yawan lokuta waɗannan dabaru sukan bambamta a tsakanin darussa, zalika ya danganta da matakan ilimi daga ƙasa, ...

Dec 10, 202410 min

Rashin malamai ya tilasta iyaye janye yaransu daga makarantu a kudancin Najeriya

Shirin Ilimi hasken rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda iyaye a yankin kudancin ƙasar ke janye yaransu daga Makarantu saboda ƙarancin makarantu a yankin. Jihar Abia na sahun ƴan gaba gaba da ke fama da wannan matsala inda a baya-bayan nan aka tarin yaran da suka daina zuwa makaranta.

Nov 06, 20249 min

Gwamnatin Bauchi na shirin mayar da yara fiye da miliyan 1 makarantu

Shirin Ilimi hasken Rayuwa tare da Shamsiyya Haruna a wannan makon ya mayar da hankali ne kan yadda gwamnatin jihar Bauchi a Najeriya ke yunƙurin mayar da yara fiye da miliyan guda makaranta a wani yanayi da ake ganin ƙaruwar yaran da basa zuwa makaranta a yankin arewacin kasar. Tuni masu ruwa da tsaki a wannan yanki suka yi maraba da matakin gwamnatin ta Bauchi, lura da yadda yunƙurin zai taimaka matuƙa wajen rage ɗimbin yaran da ke gararamba ba tare da zuwa makaranta ba a Arewacin na Najeriya....

Oct 29, 202410 min

Ɓanagrorin ilimi sun koka da matakin JAMB na durkusar da harshen Faransanci

Sannu a hankali darussan nazarin harshen faransanci na kara karbuwa a manyan makarantun Nigeria, sai dai kuma, wani matakin da hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu ta JAMB a Nigeria, ta aiwatar, na cire takardar shaidar share fagen shiga jami’a ta karatun harshen faransanci, daga cikin darussan da hukumar ta JAMB ke bayar da guraben karatunsu a manyan makarantu ya daga hankalin masu ruwa da tsaki.

Oct 24, 202410 min

Yadda jami’o’i a Najeriya ke neman tallafin inganta ƙirƙirarriyar fasaha ta AI

Shirin Ilimi Hasken Rayuwa na wannan makon ya duba yadda wasu manyan jami’o’i a Najeriya ke neman tallafin ƙasashen da suka ci gaba kan yadda za a inganta ƙirƙirarriyar fasaha ta AI. Tuni kuma suka gabatar da wannan buƙata tasu a wajen taron da ƙungiyar bunkasa ilimi ta ƙasashen Turai kan shirya duk shekara, inda a wannan shekara Faransa ta karbi baƙuncin irin wannan taro da ya samu halartar jami'oi 6 da aka zabo daga Najeriya. Ku latsa alamar sauti don sauraron cikakken shirin tare da Shamsiyya...

Oct 08, 202410 min
For the best experience, listen in Metacast app for iOS or Android
Open in Metacast