Tasirin naɗin da wasu Masarautu ke yiwa waɗanda ba ƙabilunsu ba - podcast episode cover

Tasirin naɗin da wasu Masarautu ke yiwa waɗanda ba ƙabilunsu ba

Feb 18, 202510 min
--:--
--:--
Listen in podcast apps:
Metacast
Spotify
Youtube
RSS

Episode description

Shirin al'adunmu na gado tare da Abdoulaye Issa a wannan mako ya mayar da hankali kan al'adar nan ta naɗin sarauta da wasu masarautun gargajiya ke yi ga  ƙabilun da ba su ke da masarautar ba, wanda hakan ya biyo bayan sabbin naɗe-naɗe da ɗaya daga cikin manyan masarautun ƙabilar gwari a arewacin Najeriya ta yi wa wasu manyan shuwagabannin al'ummar fulani a jihar Neja.

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da ake samun masarautun Hausa da Fulani da ma wasu masarautun a yankin kudanci da kuma arewacin Najeriya ke baiwa ƙabilun da ke zaune a masarautar sarauta ba, abin da shirin Al'adu na wannan mako ya yi nazari akai tare da jin inda hakan ya samo asali da kuma alaƙar da ke tsakanin al'adun ƙabilar gwari da fulani daga masana al'adu da masarautu.

Ku latsa alamar sauti don sauraren cikakken shirin.

For the best experience, listen in Metacast app for iOS or Android
Open in Metacast
Tasirin naɗin da wasu Masarautu ke yiwa waɗanda ba ƙabilunsu ba | Al'adun Gargajiya podcast - Listen or read transcript on Metacast